Dalilin da ya sa ba zan zama mataimakin Peter Obi ba – Kwankwaso

.

Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam'iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ba zai iya zama mataimakin Peter Obi ko wani ɗan takarar shugaban ƙasa ba.

Tsohon gwamnan Jihar Kanon ya bayyana haka a Jihar Gombe yayin ƙaddamar da ofishin jam'iyyar da kuma ganawa da wasu daga cikin waɗanda za su yi wa jam'iyyar takara a zaɓen 2023.

Jaridun Najeriya sun ruwaito tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya a ranar Asabar yana ba ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin Jam'iyyar Labour Party shawara da ya karɓi tayin da ya yi masa na zama mataimaki a zaɓe mai zuwa.

Ko a kwanakin baya lokacin da BBC ta yi hira da Kwankwaso sai da ya ce yana tattaunawa da Peter Obi kan batun samun maslaha a tsakaninsu.

A yayin da Kwankwaso yake hira da ƴan jarida a Gombe, ya bayyana cewa idan ya kuskura ya zaɓi ya zama mataimakin Peter Obi ko wani ɗan takara, hakan zai ja jam'iyyarsa ta NNPP ta rushe.

Kwankwaso ya bayyana cewa ƙwarewarsa a siyasa da kuma irin ayyukan da ya yi a baya sun taimaka masa wurin ɗaukakar Jam'iyyar NNPP.

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa jama'ar kudu maso gabashin Najeriya sun ƙware a harkar kasuwanci kuma suna da basira, amma har yanzu suna koyon siyasa ne.

A kwanakin baya ne dai Jam'iyyar NNPP wadda aka fi sani da jam'iyya mai kayan daɗi ta tsayar da Rabiu Kwankwaso a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban ƙasa bayan Kwankwason ya fito takara ba tare da hamayya ba.