Matashin da ke neman sauya rubutun Hausa da sabbin harufa
Ranar 26 ga watan kowane Agusta - irin ta yau ke nan - ne aka ware domin bikin Ranar Hausa.
Albarkacin wannan rana, mun tattauna da matashi Sadar Musa, wanda ke neman sauya rubutun Hausa ta hanyar ƙirƙirar baƙaƙe da wasula 37 sababbi fil.
Mazaunin unguwar Dala a birnin Kano na arewacin Najeriya, Sadar ɗalibin Hausa ne a Buɗaɗɗiyar Jami'a ta Ƙasa (National Open University) a Najeriya.








