Wace dabara ta rage wa jam'iyyun hamayya a Najeriya?

Hamayya

Asalin hoton, FB/Multiple

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

A ranar Laraba, 31 ga watan Disamba ne tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sanar da sauya sheƙarsa zuwa jam'iyyar haɗaka ta ADC.

Obi ya bayyana hakan ne a wani taro da magoya bayansa da shugabannin siyasa suka gudanar a Enugu, babban birnin Jihar Enugu.

Da yake jawabi a taron, Peter Obi ya ce bayan watanni na tuntuɓa da tattaunawa, su da wasu waɗanda ya bayyana da "sauran shugabannin yankin Kudu maso Gabas" sun yanke shawarar shiga ADC domin haɗa ƙarfi da sauran jam'iyyun adawa.

Ya ce burinsu shi ne "Ceto Nijeriya daga mummunar shugabanci tare da yin duk mai yiwuwa don daƙile maguɗi da murɗiyar zaɓe a shekarar 2027, sannan tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya, Atiku Abubakar ya yi masa maraba.

Manyan shugabannin siyasa daga sassa daban-daban na ƙasar da wasu tsofaffin gwamnoni da manyan jiga-jigan siyasa ne suka halarci taron, lamarin da ake ganin ya ƙara ƙarfafa yunƙurin haɗin kan ƴan adawa domin fuskantar zaɓen 2027.

Sai dai sauya sheƙar ta Obi ta zo a daidai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara kan yadda ake ta rububin komawa jam'iyyar APC mai mulki, inda wasu ke tambayar shin jam'iyyar hamayya za su iya wani kataɓus kuwa?

Shin PDP ta mutu?

A ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara ne gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya sanar da ficewarsa daga PDP, sannan a ranar Juma'a, 2 ga watan Janairun, ya sanar da komawarsa APC.

A babban zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, PDP ce ta zo ta biyu, inda Bola Tinubu ya doke Atiku Abubakar.

Tuni Atiku ya fice daga PDP ya koma ADC, sannan wanda ya mara masa baya a takarar, Ifeanyi Okowa ya koma APC.

Haka kuma a zaɓen, PDP ta samu gwamnoni da dama da sanatoti da ƴan majalisun tarayya, amma yanzu jam'iyyar ta rasa wasu jiga-jiganta.

Gwamnoni PDP bayan babban zaɓen 2023

  • Ahmadu Fintiri - Adamawa
  • Bala Mohammed - Bauchi
  • Caleb Mutfwang - Filato
  • Agbu Kefas - Taraba
  • Dauda Lawal - Zamfara
  • Seyi Makinde - Oyo
  • Siminalayi Fubara - Rivers
  • Ademola Adeleke - Osun
  • Umo Eno - Akwa Ibom
  • Sheriff Oborevwori - Delta
  • Peter Mbah - Enugu
  • Douye Diri - Bayelsa

Waɗanda suka rage yanzu a PDP (Janairun 2026)

  • Ahmadu Fintiri - Adamawa
  • Bala Mohammed - Bauchi
  • Seyi Makinde - Oyo
  • Dauda Lawal - Zamfara

Bayan gwamnoni, akwai kuma jiga-jigan ƴan siyasa da sanatoci da ƴan majalisar wakilai da dama da suke fice daga jam'iyyar, inda wasu ke ganin ta fara sauka da muƙamin babbar jam'iyyar adawa a ƙasar.

Bayan haka kuma jam'iyyar na fama da rikici, inda yanzu haka ake jira ganin ko hukumar INEC za ta amince da shugabancin jam'iyyar a ƙarƙashin Kabiru Tanimu Turaki.

Ana dai tunanin akwai yiwuwar jam'iyyar za ta iya ƙara rasa wasu daga cikin jiga-jiganta nan da wani lokaci, musamman saboda rikicin shugabancin, da kuma rashin tabbas da wasu ke gani a tattare da ita.

Sauran jam'iyyun hamayya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ba PDP ba ce kawai ta shiga ruɗu a cikin jam'iyyun hamayya a Najeriya, inda suma jam'iyyun Labour da NNPP da ake gani suna ɗan tagomashi suke ta fama da rikice-rikicen cikin gida.

Tuni rikici ya ɓarke a cikin jam'iyyar NNPP, inda aka fara raɗe-raɗin cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, wanda shi ƙadai ne gwamnan jam'iyyar na yunƙurin komawa APC, lamarin da ya haifar da ɓaraka babba.

A ɗaya ɓangaren kuma, babban jigo a jam'iyyar Labour, Peter Obi shi ma ya fice ya koma ADC, sannan wasu sanatocin jam'iyyar suka fice, wanda hakan ya sa ita ma ta fara tsilla-tsilla.

Haka kuma Jam'iyyar Labour na fama da rikicin shugabanci, inda yanzu haka ɗaya tsagin shugabancin a ƙarƙashin Julius Abure ta ce Umma ta gaida Aisha, inda ta ƙara da cewa yanzu ne za ta samu sukuni.

Ita kuma jam'iyyar NNPP ana ganin tana fuskantar barazana mafi girma a tarihinta, lamarin da wasu ke ganin zai iya jawo watsewarta matuƙar ba ta iya tsallake wannan sabuwar ɓarakar ba.

Sannan ita ma tana fuskantar shugabanci, lamarin da wasu ke ganin har yanzu akwai sauran rina a kaba.

ADC za ta iya?

Bayan komawar Peter Obi jam'iyyar ta haɗaka, da ganin irin marabar da Atiku Abubakar, sai aka fara tattaunawa yadda haɗakar manyan siyasan biyu za ta yi kyau domin fuskantar APC.

Sai dai ƴan Najeriya na yin tambayar cewa wane ne a cikin jiga-jigan ƴan siyasar da ke cikin jam'iyyar ta haɗaka zai yi wa jam'iyyar takarar shugaban ƙasa domin ƙalubalantar shugaba Bola Tinubu na jam'iyya mai mulki ta APC a 2027.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda ya yi takarar neman shugaban ƙasa sau huɗu da Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar LP a 2023 da tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi tare da wasu gaggan ƴan hamayya su ne ake tunanin suna neman tikitin jam'iyyar.

Wannan ya sa jam'iyyar, wadda masana ke ganin za ta karɓi wasu sababbin baƙin za ta fuskanci babbar barazana zaɓin wanda zai mata takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.

Magoya bayan Peter Obi dai suna ganin shi ne zaɓinsu, inda suke ganin shi ne ya fi cancanta, a ɗaya gefen kuma magoya bayan Atiku Abubakar suke ganin tsohon shugaban ƙasar ne ya fi dacewa da takarar.

Ana dai ganin babbar matsalar da ke gaban ADC ita ce ayyana ɓangaren da ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito, musamman ganin yadda ƴan kudancin Najeriya suka ganin suna da sauran lokaci.

Ina mafita?

Duk da cewa sauye-saueyen jam'iyya ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya, ana kallon faruwar hakan a yanzu a matsayin mafi tasiri saboda yadda duka manyan jam'iyyun adawa ke cikin rikici.

A wata tattaunawa da BBC ta yi da Farfesa Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa ne a Jami'ar Abuja, ya ce nan gaba idan ba a yi taka tsan-tsan ba Najeriya za ta iya komawa kasa mai jam'iyya ɗaya.

Farfesa Kari ya ce ya kamata ya yi jam'iyyun hamayya su riƙa haɗuwa suna gangami domin ƙwace mulki daga jam'iyya mai muki, "amma saboda lalacewa da rashin haɗin kai na 'yan'adawa, sai ya zama akasin haka ne ke faruwa".

A game da abin da ya kamata a yi, Farfesa Kari ya ce: "Ƴan'adawa su yi gagarumin yunƙuri domin ganin hakan bai ci gaba da faruwa ba, kuma suma su fara zawarcin manyan ƴansiyasa daga APC ganin cewa ita ma jam'iyyar mai mulki tana fuskantar ƙorafe-ƙorafe da rashin gamsuwa da yadda abubuwa ke wakana."

Shi ma Farfesa Abubakar Mu'azu na Jami'ar Maiduguri kuma darakta a cibiyar diflomasiyya da cigaban ƙasa ya bayyana a wata tattaunawarsa da BBC, cewa ya yi ita ma APC haɗaka ce aka yi domin kayar da PDP.

"Kamata ya yi jam'iyyun hamayya su tsara gidansu ta yadda za su ja hankalin masu zaɓe. Ai da ba APC ba ce take mulki, daga baya ne wasu suka haɗe suka kayar da PDP.

"Ya kamata su yi la'akari da cewa duk wanda yake kan mulki yana so ya ci gaba, ya rage nasu su san dabarar da za su yi domin ƙwace mulki."

Ko APC na da hannu a rigingimun ƴan hamayya?

Wata magana da ta daɗe tana yawo a tsakanin masu bibiyar harkokin siyasar Najeriya ita ce zargin cewa gwamnatin tarayya da APC tana da hannu wajen shirya rikice-rikicen da jam'iyyun hamayya suke fuskanta.

A game da waɗannan zarge-zarge, a wata tattaunawa da BBC, Farfesa Kamilu Sani Fagge na Jami'ar Bayero ta Kano ya ce akwai ƙamshin gaskiya a zargin.

A cewarsa: "Ganin yadda abubuwa ke faruwa ba za a yi mamaki ba idan an ce jam'iyya mai mulki na da hannu a rikicin. Ko dai ba ita ƙirƙira ba, zai iya zama tana da hannu wajen rura rigingimun domin ganin ba su ƙare ba. Haka ake yi a siyasar Najeriya, inda kowace jam'iyya take ƙoƙarin rushe abokiyar hamayyarta ita kuma ta gina kanta."

Farfesa Fagge ya ce ko a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi tsakanin Bola Tinubu da Atiku Abubakar, "Wike ya yi ƙoƙari domin tabbatar da jam'iyyarsa ta kafa gwamntin jiha, amma ya ƙi bayar da goyon baya wajen kafa ta tarayya".

Ya ƙara da cewa rigingimun suna yawa ne saboda yawancin jam'iyyun ba su da aƙida. "Kawai mutane suna shiga ne saboda biyan buƙata, idan buƙatar ba ta biya ba, su fice su kom wata. Ko kuma su zauna a ciki su mata ƙafar unguwa."

Sai dai farfesan ya ce ba yanzu aka fara hakan ba, domin a cewarsa, an yi a jamhuriyya ta ɗaya da ta biyu.

"Amma lamarin ya fi ƙamari a jamhuriya ta huɗu. Misali, manyan jam'iyyu su ne PDP da APP. Da PDP ta samu mulki, sai ta janye wasu jiga-jigan APP ta ba su ministoci, daga baya kuma suka narke a PDP."