Sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Senegal

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Lahadi 24 ga watan Maris, 2024 ne aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Senegal, inda ƴan takara 17 suka fafata domin samun gwanin da zai gaji shugaba mai barin gado, Macky Sall.
Wannan zaɓe ne da ke da matukar muhimmanci ga alummar kasar ta Senegal, bayan kai ruwa ranar da aka yi ta yi da tashin-tashina kan yunkurin Shugaba Macky sall na jikrta shi.
Manyan ƴantakara biyu na zaɓen su ne, jagoran ƴan hamayya Bassirou Diomaye Faye, sai kuma dantakarar jam’iyya mai mulki, kuma tsohon firaminista Amadou Ba.
Shafa saman taswira domin ganin yawan ƙuri'un ƴantakara daga kowane yanki:
Senegal mai yawan al’umma miliyan goma sha takwas (18 ) ta kasance ɗaya daga cikin kasashen Afirka da suka fi zaman lafiya da wanzuwar mulkin dumukrdiyya lami lafiya.
Kasar ba ta taba gamuwa da juyin mulkin soji ba, kuma haka take samun sauyin shugabanci cikin kwanciyar hankali tun da ta samu mulkin kai daga Faransa a shekarar 1960.
Wanda ya ci zaɓen zai yi fama da kalubale na magance matsalar tsadar rayuwa da rashin aikin yi da kuma sauye-sauye na hukumomi.
Alƙaluma kan ƙasar Senegal

Yawan masu kaɗa ƙuri'a:

Asalin hoton, Getty Images
Yawan ƴanmajalisa da jam'iyyunsu:

Yawan mata a majalisar dokoki:







