Ra'ayoyin ƴan Najeriya mazauna Dakar kan zaɓen shugaban ƙasar Senegal

Bayanan bidiyo, Latsa nan domin kallon wannan bidiyo
Ra'ayoyin ƴan Najeriya mazauna Dakar kan zaɓen shugaban ƙasar Senegal

Ranar Lahadi al’ummar Senegal za su zabi sabon shugaban kasa bayan karewar wa’adin mulkin shugaba Macky Sall.

Hakan na zuwa ne bayan turka-turka da aka sha game da yunkurin dage zaben, lamarin da ya janyo zanga-zanga da fargaba a fadin kasar.

Shin ya al’ummar Hausawa mazauna kasar ke kallon zaben na ranar Lahadi?