Ban yi nadamar ɗage zaɓen Senegal ba - Macky Sall

Asalin hoton, bbc
Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya ce bai yi nadamar ɗage zaben ƙasar ba da ya kamata a gudanar a watan da ya gabata, lamarin da ya haifar da ƙazamar zanga-zanga a faɗin ƙasar.
A wata hira da shugaban ya yi da BBC, Sall ya fayyace cewa ya ɗauki matakin ɗage zaɓen ne saboda matsalolin zaɓen da 'yan majalisar suka nuna.
"Babu wani haƙurin da zan bayar, ban yi wani laifi ba, ina magana da kai a matsayin shugaban ƙasar Senegal. Dukkan matakin da aka ɗauka kan zaɓen sun kasance cikin tsarin doka da ka'idoji," in ji Shugaba Sall.
Ƙoƙarin da shugaba Sall ya yi na ɗage zaɓen wanda ya haifar da tarzoma da tashe-tashen hankula a faɗin kasar ya samu cikas, inda daga karshe kotun ƙolin kasar ta soke shi.
Yanzu dai an shirya gudanar da zaɓen a ranar Lahadi.
Da farko dai, shugaban ya nemi a mai da zaben zuwa watan Disamba amma bai samu nasarar yin hakan ba.
Masu suka dai sun zargi shugaban da yunkurin tsawaita zamansa kan karagar mulki.
Amma Mista Sall ya nace da cewa ba zai ƙara kwana guda ba a matsayin shugaba ko da kuwa kuri'ar ranar Lahadi ba ta nuna wanda ya yi nasara ba.
A makon da ya gabata ne aka sako babban jagoran 'yan adawa kuma daya daga cikin masu sukar Sall, Ousmane Sonko da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa Bassirou Diomaye Faye daga gidan yari a ƙarƙashin wata afuwar da shugaban kasar ya yi.
Shugaba Sall ya musanta cewa tuhumar da ake yi wa abokan hamayyarsa na da nasaba da siyasa.
Bayan wa'adi biyu a matsayin shugaban Senegal, Sall zai sauka inda jam'iyyarsa mai mulki Benno Bokk Yakaar (BBY) ta zaɓi Amadou Ba mai shekaru 62 domin ya tsaya takarar shugabancin kasar.











