Wace ce Akshata Murty, Matar Ba'indiyen da ya zama sabon firaministan Birtaniya

Rishi Sunak tare da matarsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mista Rishi tare da matarsa misis Akshata sun yi aure a shekarar 2009

Samun nasarar ɗarewar kujerar Firaministan Birtaniya da Rishi Sunak, ya yi, abu ne da ya ja hankula sosai a Indiya, ba wai kawai saboda kasancewarsa ɗan Asiya na farko da ya samu wannan matsayi ba.

Matarsa Akshata Murty 'ya ce ga biloniyan kasar Indiya Narayana Murthy, ɗaya daga cikin hamshakan 'yan kasuwa a kasar ta Indiya, wanda ake yi wa lakabi da 'Bill Gates' ɗin Indiya.

Bayan tarin biliyoyin da ta gada a wajen mahaifinta, Akshata ta fuskanci matsin lamba a 'yan shekarun baya-bayan nan, inda aka zarge ta da rashin biyan haraji kan kasuwancin da take yi a ƙasashen waje.

Ko da yake daga bisani ta amince za ta fara biyan haraji ga Birtaniya a kan kudaden da take samu a ketaren.

Duk da tarin kuɗin da iyayenta ke da shi, Akshata ta samu nasarar fara harkokin kasuwancinta da kafar dama.

A wata wasika, da aka wallafa a shekarar 2013, mahaifinta ya bayyana yadda ya yi farin ciki da samun labarin haihuwarta cikin watan Afrilun 1980, daga wani abokin aikinsa, saboda a cewarsa a wancan lokacin gidansu ba su da sukunin mallakar waya.

"A lokacin ni da mahaifiyarki muna matasa, kuma muna fafutikar yadda za mu tsaya da kafafunmu'' kamar yadda ya rubuta a wasikar.

Bayan 'yan watanni da haihuwarta, iyayen Akshata sun kai ta wajen kakanninta domin kula da ita, a yayin da su kuma suka tafi harkokin kasuwancinsu a birnin Mumbai.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan shekara guda mahaifinta ya haɗa hannu da wasu wajen kafa kamfanin fasaha na Infosys, wanda kuma shi ne ya sanya shi zama ɗaya daga cikin hamshakan masu arzikin Indiya.

Iyayenta sun mayar da hankali wajen ilimi da aiki tukuru ga 'ya'yansu biyu wato Akshata da kanwarta.

Mahaifinta ya ce ko akwatin talabijin bai saka ba a gidansa, lamarin da ya ce, ya sa yaran mayar da hankali sosai wajen karatu.

Akshata ta karanta fannin tattalin arziki da harshen faransanci wata kwaleji mai zaman kanta da ke birnin California.

Ta kuma samu difloma a kwalejin fasahar kayan kawa, kafin ta fara aiki da kamfanonin Deloitte da Unilever, sannan daga baya ta samu digirin farko a jami'ar Stanford.

A jami'ar ne dai ta haɗu da mijinta mista Rishi. Inda suka yi aure a shekarar 2009, kuma yanzu suke da 'ya'ya biyu, duka mata.

Akshata mai shekara 42 ta fara harkokinta a birnin California, kafin ta buɗe kamfaninta na kayan kawa, wanda ta sanya wa suna 'Akshata Designs' a shekarar 2011.

To sai dai jaridar Guardian ta ruwaito cewa an rufe kamfanin bayan shekara uku.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tana da hannun jari na kusan kashi 0.9 a kamfanin Infosys na mahaifinta, wanda aka kiyasta darajarsa za ta kai fan miliyan 700.

Ɗaya daga cikin manyan kamfanoninta shi ne kamfanin 'Catamaran Ventures' da ke Birtaniya, wanda ta kafa tare da mijinta a shekarar 2013.

To sai dai a watan Fabarairun wannan shekarar an rufe kamfanin bayan da ya kasa biyan bashin da ake binsa saboda raguwar kuɗin shiga da annobar korona ta haddasa, duk da tallafin kuɗin da ya samu.

Misis Akshata ta taba zama babbar daraktar kamfanin New & Lingwood, wanda ke sayar da tufafi masu tsada.

Tana da hannun jari na kusan kashi 0.9 a kamfanin Infosys na mahaifinta, wanda aka kiyasta darajarsa za ta kai fan miliyan 700.

Hannun jarinta a kamfanin ya zamo wani abin ce-ce-ku-ce bayan da Rasha ta mamaye Ukraine, lokacin da kamfanin ya fuskanci matsin lambar rufe ayyukansa a kasar Rasha.

A watan Afrilu, an shaida wa BBC cewa kamfanin Infosys ya rufe ofishinsa a Rasha.

Tarin dukiyar da misis Akshata da mijinta mista Rishi suka mallaka ya sa wasu da dama cikin tantama kan taimakon talakawa, musamman a lokacin da talakawan suke fuskantar matsin tsadar rayuwa.

A baya dai ba a cika jin abokanan auren tsoffin firaministoci da mallakar tarin dukiya ba, alal-misali Philip mijin Theresa May, ba wani fitaccen mutum ba ne.

Haka kuma ita ma matar Tony Blair, wadda lauya ce mai kare hakkin dan adam, ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na lauya har bayan saukar mijinta daga mulki.

Inda ayyukanta na jin-kai suka rika jan hankulan kafafen yada labarai.

To amma kawo yanzu ita misis Akshata ba ta fara daukar hankulan kafafen yada labarai ba, in ban da dan ce-ce-ku-cen da aka samu kan batun rashin biyan harajinta a shekarun baya-bayan nan.

To amma yanzu kasancewar mijinta a matsayin firaminista, Misis Akshata za ta fara shiga kanun labarai.