Yahudawan da ke taimakon Falasɗinawa kare yankunansu daga Yahudawa masu mamaya

- Marubuci, Fergal Keane
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Special correspondent
- Aiko rahoto daga, Al Farasiya, Jordan Valley
- Lokacin karatu: Minti 6
Kamar kowace safiya, akwai tashin hankali. Daga sama kawai za ku gane akwai matsala. Abubuwa da yawa na faruwa ta yadda maras kan-gado ne kawai zai shiga yankunan ba tare da yana ankare ba.
A kan wani tsauni can, akwai wani matsugunin Yahudawa na Rotem. A kusa da shi kuma akwai wani ofishin dakarun sojin Isra'ila IDF da aka kafa domin kare Yahudawan 'yan kama-wuri-zauna.
Duk wanda ya kallo ƙasa zai ga dandazon mutane zagaye da gidan Ahmad Daraghme: Bafalasɗine makiyayi; da Isra'ilawan da ke taimaka masa; da kuma 'yan jaridar ƙasar waje ɗauke da kyamarorinsu.
Cikinsu akwai wani dattijon Bayahude mai shekara 71 da ke taimaka wa Ahmad zuwa tsaunin duk da tashin hankali da tsangwama da suke fuskanta.
"Duk loakcin da na aminta cewa fahimtata gaskiya ce, to zan yi ta gwagwarmaya game da ita. Ko da wani na ganin na fiya taurin kai? Shi ya jiyo," in ji Bayahuden Gil Alexander.
Yana cikin Yahudawan Jordan Valley 'yan gwagwarmya, wasu Isra'ilawa da suka lashi takobin kare Falasɗinawa. Sukan yi wa makiyaya rakiya a zuwa da kuma komawa daga wuraren kiwo.
Tsangawamar da makiyaya kamar Ahmad ke fuskanta ta ƙaru tun bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023 da ya kashe aƙalla mutum 1,200 da kuma yin garkuwa da 251.
Tashin hankalin da Yahudawan kama-wuri-zauna ke haddasawa a yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan na ƙaruwa ta hanyar cigaba da fitar da Falasɗinawa daga gidajensu.
A cewar OCHA - hukumar Majalisar Ɗuniya mai ba da agaji - Yahudawa masu mamaya sun kai wa Falasɗinawa hari sama da sau 1,000 tun daga watan Oktoba, wanda ya kori aƙalla mutum 1,390 daga gidajensu cikihar da yara 660.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
OCHA ta gano hare-hare 107 da aka kai wa Falasɗinawa waɗanda suka kai ga mutuwa da kuma ji musu rauni, da kuma 859 da suka lalata muhallansu.
An lalata dubban bishiyoyi na Falasɗinawa. Manoma kamarAhmad kan ba da labarin yadda ake yawan hana mazauna yankin samun ruwan sha da iri na noma.
Hankalin duniya ya fi karkata ga Zirin Gaza amma yawan hare-haren 'yan mamaya ya sa Amurka da Tarayyar Turai (EU) suka sanya takunkumai kan wasu Yahudawa, har ma da wani rukunin gidajen Yahudawa cancakat.
'Yan gwagwarmya a Jordan Valley sun fahimci cewa abu mafi muhimmanci shi ne mutane su kwantar da hankali duk kuwa da irin tsokanar da ake yi musu.
Gil Alexander ya san irin ƙetar da Yahudawa masu mamaya ke da ita. Yana ɗauke da tabo a jikinsa da ke tabbatar da hakan. Amma yana cike da ƙwarin gwiwa a wannan safiya.
"A irin wanann ranar," in ji shi, "nakan ji daɗi. Idan za mu iya hana kai hare-hare to hakan zai yi min daɗi sosai."
Gil ya zama babban aboki ga Ahmd, wanda Yahudawa ke yawan tsangwama. Ahmad ya zargi 'yansanda da sojojin Isra'ila da goyon bayan Yahudawan masu mamaya kamar yadda rahotonni iri-iri na 'yan gwagwarmyara Isra'ila da Falasɗinu suka tabbatar.

"Matsalar ita ce...an hana mu shiga waɗannan yankunan. An haramta mana zama a wannan tsaunin, dukkansa. Wannan abu ya munana: sukan tayar mana da hankali a kodayaushe," a cewar Ahmad.
A watan Disamban da ya gabata, Gil Alexander da wani ɗan gwagwarmya na tare da Ahmad lokacin da masu mamaya suka kai masa hari cikin dare. Aka yi musu duka kuma aka fesa musu yaji.
Yayin wani harin daban, sai da Gil ya suma a yunƙurin hana wani Bayahude tarwatsa dabbobin Ahmad.
An sha yi masa barazana. Abin da ya fi ɓata wa Yahudawan rai shi ne yadda yake bin addinin Yahudanci sau da ƙafa alhalin kuma fahimtarsu ita ce yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan - da suke kira Judea da Samaria - mallakin Yahudawa ne.

Asalin hoton, Jordan Valley Activists
Falasɗinawa kamar Ahmad Daraghme sun zauna a ƙarƙashin mamayar Isra'ila tun bayan da ta ƙwace yankin a Yaƙin Kwana Shida na shekarar 1967.
Tun daga lokacin kuma an gina rukunin gidajen masu mamaya sama da 160 a yankunan - ciki har da Gabashin Ƙudus - inda suke ƙunshe da Yahudawa kusan 700,000. Akwai Falasɗinawan kimanin miliyan ukua Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Ƙudus.

Asalin hoton, Jordan Valley Activists
Gil wanda ke kiran kansa mai rajin kafa ƙasar Yahudawa, yana ganin iyakokin ƙasar bai kamata su wuce na shekarar 1967 ba. Duk gidan da za a gina a Gaɓar Yamma sai an nemi izinin Falasɗinawa.
"Za mu iya nuna ƙauna ga wanan yankin ba tare da mun mallake ta ba, a ce mu kaɗai ke da ita...Idan muna so mu koma zama wata rana cikin kwanciyar hankali, bai kamata mu kori mutane da ƙarfin tsiya ba," in ji shi.
A kwanan nan, ministan kuɗi na Isra'ila, Bezalel Smotrich, ya nemi gwamnati "ta yi babban yunƙuri" na faɗaɗa gidajen Yahudawa.
Mako biyu da suka wuce gwamnatin Benjamin Netanyahu ta ayyana eka 3,000 a yankin Jordan Valley a matsayin ƙasar Isra'ila - wanda shi ne mafi girma cikin shekara 30.
An yi hakan ne bayan ta ayyana eka 2,000 a yankin a watan Maris.
Sai dai kuma yanzu babbar kotun ƙasa da ƙasa ta bayyana mamayar da Isra'ila ke yi a matsayin wadda ta saɓa wa yarjejeniyar daƙile wariya a duniya.

Ahmad Daraghme ya ce: "Duka waɗannan yankunan, ba a ba mu damar mu shige su ba. An shuka inibi a wasu. An keɓance wasu...Kawai so suke mu bar yankin. So suke su dawo wurin. Ba su son ganin mu a nan."
Majalisar Isra'ila ta kaɗa ƙuri'a a baya-bayan nan cewa kafa ƙasar Falasɗinawa a Gaɓar Yamma zai "zama barazana ga tsaron Isra'ila da 'yan ƙasarta, ya haddasa rikici tsakanin Yahudawa da Falasɗinawa", inda inda 68 suka goyi baya, masu adawa kuma suke da ƙuri'a tara.

Shai Rosengarten na cikin jagororin ƙungiyar Im Tirtzu da ke goyon bayan kafa ƙasar Yahudawa kuma suke neman cigaba da mamaye ƙasar Falasɗinawa. Yana cewa 'yan tsiraru ne ke kai wa Falasɗinawan hari, amma kuma wai Yahudawan da gwagwarmayar kare Falasɗinawa su ne masu matsala.
"Muna kallonsu a matsayin tsagera, da ke kawo wa ayyukan sojoji cikas kuma hakan matsala ce ga yankin.
"Ina nufin hakan na jawo wa ayyukan sojoji matsala. Ƙwarai suna son korar maharan ne amma kuma sukan kori sojoji ma. Muna da misalan irin waɗannan yunƙurin da suka faru a gaban sojojin Isra'ila," in ji Shai.
Sai dai Gil ya yi watsi da wannan batu yana mai cewa yana kare cikakkun ɗabi'un Yahudawa ne.
"Ba mu da wani zaɓi...Tabbas yaƙi ba zai haifar da komai ba. Daga yaƙi zuwa yaƙi, hakan na ƙara rage mana ƙarfi...Ai ƙarfin zuciyarmu ma na da iyaka."
Tare da taimakon masu rahoto Alice Doyard da Haneen Abdeen.











