Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ke faruwa tsakanin Ukraine da Rasha bayan ɓarkewar faɗa a Gaza?
A farkon watan Nuwamba, Ukraine ta bayar da rahoton cewa, an yi ruwan bama-bamai kan kimanin wurare 120 a cikin kwana ɗaya, hari mafi girma tun bayan kamawar wannan shekarar.
Amma duk da haka hankalin duniya ya ci gaba da kasancewa a kan Gaza da Isra'ila.
Yiwuwar samun raguwar daga kasashen duniya, shi ne fargaba mafi muni ga kasar Ukraine tun daga lokacin da Rasha ta ƙaddamar da mamaye a kanta.
Idan babu tallafin soji da na kudi daga kawayenta, Ukraine ba za ta samu wata dama ba wajen tunkarar Rasha a fagen daga da kuma kiyaye farmaki ta sama, wanda ke da matukar muhimmanci ga kare garuruwan Ukraine.
Bari mu duba wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a watan da ya gabata a fagen daga tsakanin Rasha da Ukraine.
Yaƙin Juriya
Manazarta da dama sun ce bangaren da zai iya jure wa hasara na tsawon lokaci shi ne zai yi nasara a yakin.
Kwamandan dakarun Ukraine, Valery Zalumzhny ya bayyana yaƙin a matsayin "mai gajiyarwa."
"Kamar yadda ya faru a yaƙin duniya, mun kai wani matsayi na ci gaban ƙere-ƙere da za a iya cewa an kai bango," kamar yadda ya bayyana a wata maƙala a jaridar 'the Economist' ta Birtaniya.
A wani bayani kan wata biyar da sojojin Ukraine suka kwashe suna ƙoƙarin ƙwato yankunan da Rasha ta ƙwace, ya ce a tsawon wata biyar, sojojin sun matsa a yankin da bai wuce kilomita 17 ba.
A halin yanzu Rasha na iko da kimanin kashi 17.5% na faɗin ƙasa mallakin Ukraine, duk da an samu sauyi a 2023.
A makonnin da suka gabata faɗa ya ƙazanta a kusa da garin Avdiivka da ke gabashin Ukraine, inda dukkanin ɓangarorin biyu suka yi asarar dakaru ba tare da wata nasarar a zo a gani ba.
Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta yi ƙiyasin cewa asarar da Rasha ta yi a garin Avdiivka a shekarar 2023 ta fi ta kowane lokaci.
Janar Zalunzhny ya bayyana yadda a yanzu ɓangarorin biyu ke taƙama da kayan yaƙi na zamani, ta yadda kowa na iya ganin abin da abokin hamayyarsa ke kitsawa.
Ya ce sanadiyyar hakan ne dukkanin ɓangarorin biyu suka kasa samun nasarar a-zo a -gani.
Daga nan sai ya yi kira ga ƙawayen Ukraine da su samar wa ƙasar da makamai masu tsananin saiti, dakuma makaman atilare.
Alaƙar Amurka da Ukraine
Yanzu haka ana sake duba yadda Amurka da ƙawayenta ke samar wa Ukraine makamai - bayan da Majalisar Dokokin Amurka ta zaɓi sabon shugaba.
An zaɓi ɗan majalisar jam'iyyar Republican, Mike Johnson daga Loisiana a kan muƙamin ranar 25 ga watan Oktoba.
Tun farko shugaban Amurka, Joe Biden ya buƙaci majalisar da ta amince da kuɗi dala biliyan 106 waɗanda za a kashe a ɓangaren tsaro, ciki har da dala biliyan 61 waɗanda za a yi amfani da su wajen tallafa wa Ukraine.
Sai dai sabon shugaban majalisar wakilan na Amurka ya fi bayar da muhimmanci kan taimakon da Amurka za ta ba Isra'ila, inda ya ce duk da cewa "Amurka ba za ta bari Vladimir Putin ya ci galaba a kan Ukraine ba, dole ne kuma mu tsaya wa babbar aminiyarmu a gabas ta tsakiya, wato Isra'ila."
Mike Johnson ya ce duk da dai yana goyon bayan bai wa Ukraine tallafi, to amma akwai buƙatar cikakken bayani da kuma kyakkyawan tsari daga fadar White House.
Babban jami'in tsaro na Ukraine, Oleksiy Danylov ya ce wannan ba wani aiki mai wuya ba ne: "A shirye muke mu yi cikakken bayani kan tallafin, babu wani abu da ake ɓoyewa."
Sai dai koda za a amince da wani tallafin, zai iya yiwuwa a samu jinkiri, wani abu da zai iya haifar da nakasu a fagen yaƙi.
Haka nan akwai wasu a majalisar dokoki ta Amurka da ke son a rage tallafin da ake bai wa Ukraine tare da karkatar da shi zuwa ga Taiwan.
Shugaba Zelensky dai ya musanta rahotannin da ke cewa Amurka da Tarayyar Turai na tattaunawa da Rasha, inda suka mayar da Ukraine gefe.
Ya bayyana a taron manema labaru na haɗin gwiwa tare da tare da shugabar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen a watan Nuwamba cewa "Kowa ya san halayyata, wadda ta yi daidai da ɗabia'ar al'ummar Ukraine...Babu wanda ke matsa min lamba (domin tattaunawa), babu, daga ɓangaren Tarayyar Turai ko Amurka."
Ya musanta duk wata yiwuwar tattaunawa da Rasha, sai dai ya amince cewar yaƙin da ya ɓarke a Gabas ta tsakiya ya ɗauke hankalin duniya daga Ukraine.
Kamar yadda hafsan hafson ƙasar ya bayyana, shi ma Zelensky ya roƙi ƙawayen Ukraine "Amurka da Turai da Asiya", su ci gaba da taimaka wa ƙasar kasancewar tana ƙoƙari ne na kare abin da dukkaninsu suka yarda da shi, wato dimokuraɗiyya.
Haka nan a wata tattaunawa da kafar yaɗa labaru ta NBC da ke Amurka, ya ce kau da kai daga Ukraine na da haɗari: "Idan Rasha ta kashe mu gaba ɗaya, za ta koma kan ƙasashen NATO."
Ukraine dai ta sha alwashin ƙwace duk wani yanki da Rasha ta karɓe daga gare ta, har da Crimea wanda Rasha ta ƙace a 2014.
Ita kuwa Rasha ta bayyana samamen da take yi a Ukraine a matsayin wani "wani aikin soji na musamman", wanda ta ƙaddamar domin ƙalubalantar ƙasashen yamma da take wa kallon maƙiyanta.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar Rasha, Dmitri Peskov ya nace kan cewar "yaƙin bai tsaya ba" kuma a cewar sa Rasha za ta ci gaba da dannawa a fagen fama.
Bayanan kowace rana da Rasha ke fitarwa kan yaƙin ba sa ƙunshe da da irin sojojin da take rasawa a fagen daga, sai dai takan bayyana asarar sojoji da makamai da Ukraine take yi.
Sai dai masu rahoto kan tsaro a Rasha sun yi kakkausar suka ga kwamandojin ƙasar saboda rashin bayar da isasshen horo da taimako ga bataliyoyin da aka tura domin gwabza yaƙi a yankin Avdiivka.
Ƙarin hare-hare kan fararen hula
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke tayar wa Ukraine hankali yayin da lokacin tsananin sanyi ke ƙaratowa shi ne yadda Rasha ke ƙara ƙaimi wajen kai hari kan cibiyoyin samar da abubuwan rayuwa na fararen hula, kamar tashoshin lantarki da hanyoyin sufuri.
Yawaitar irin waɗannan hare-hare na sanyawa abin na zama mai wahala ga shingayen kariya ta sama na ƙasar su samar da tsaro.
Ukraine na fama da hare-hare na makaman atilare da rokoki da makamai masu linzami da kuma na jirage marasa matuƙa a kullu-yaumin.
Yankunan da ke kusa da fagen daga da kuma inda makaman atilaren Rasha ke iya kai wa na ci gaba da asarar rayuka da kuma lalacewar gine-gine.
Sa'ilin da yake bayani ranar 31 ga watan Oktoba, wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya shaida wa kwamitin tsaro na majalisar cewa "Hare-haren Rasha na tsunduma al'ummar Ukraine cikin matsanancin hali, sannan sama da kashi 40% na buƙatar agaji jin-ƙai.
Ramesh Rajasingham, wanda shi ne daraktan tafiyar da al'amura a ofishin MDD mai kula da harkar jin-ƙai, ya ce dubban mutane ne hare-haren Rasha suka kashe tun lokacin da ta ƙaddamar da samame a Rasha a watan Fabarairun 2022.
MDD ta tabbatar da cewa an kashe fararen hula 9,900, sai dai ta haƙikance kan cewa "ainahin yawan waɗanda aka kashen ya zarta haka."
Yarjejeniyar fitar da hatsi
A cikin wata ɗaya da ya gabata, hukumomin Ukraine sun samu damar fita da hatsi daga ƙasar ta wata kwarkwaɗa da ke a yammacin tekun Bahar Rum, ta ruwan da ke ƙarƙashin ikon ƙasashen Romania da Bulgaria, zuwa cikin Turkiyya, a wani yunƙuri na kauce wa hari daga Rasha.
Sai dai wannan tsari na bari ana fitar da kaɗan ne daga cikin hatsin da ya kamata a fitar.
An yi ƙiyasin cewar kimanin tan miliyan ɗaya na tsaba ne ta fita daga Ukraine ta sabuwar hanyar daga watan Agusta.
Kafin samamen da Rasha ta ƙaddamar, Ukraine kan fitar da tsaba da kan kai tan miliyan shidda.
Duk da cewar abin da ake fitarwa a yanzu kimanin rabi ne na tsabar da aka fitar a watan Oktoba, amma ya zarta abin da aka yi tsammani.