Zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza na cikin haɗari

Falasɗinawa na buɗe baki a watan Ramadan.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Isra'ila ta hana shigar da abinci da man fetur cikin Gaza bayan ƙarewar zango na farko na yarjejeniyar tsagaita wuta ranar Asabar.
    • Marubuci, Lyse Doucet
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief International Correspondent
    • Aiko rahoto daga, Cairo
  • Lokacin karatu: Minti 5

Zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta kasance cikin rashin tabbas, kuma a yanzu al'amarin ya fito fili inda alamu ke nuna babu ita a daidai lokacin da ake sa ran za ta fara aiki.

Ana zulumin cewa ɓangarorin biyu za su koma yaƙi da juna kuma haka babu abin da zai ƙara illa ƙara jefa al'ummar Falasɗnawa cikin halin ƙunci sannan su ma waɗanda ke hannun Hamas za su ci gaba da fuskantar barazanar rayuwa.

Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka ta ce yanzu akwai sabuwar yarjejeniya, bayan ƙarewar zangon farko na yarjejeniyar a ranar Asabar. Kuma ta dakatar da shigar da dukkan wani agajin kayan jinƙai zuwa Gaza har sai hamas ta amince da sabuwar yarjejeniyar.

Ƙarƙashin yaryarjeniyar tsagaita wutan ta farko dai, za a bar manyan motoci ɗauke da kayan jinƙai 600 domin shiga Gaza a tsawon kwanaki 42 na yarjejeniyar.

Ƙasashen Larabawa da ƙungiyoyin agaji na duniya na sukar hana shigar da kayan agajin zuwa Gaza da Isra'ila ta yi.

Sakatare Janar na Majalisar ƊInkin Duniya, Antonio Guterres wanda ya sauka a birnin Alqahira na Misra domin halartar wani taron gaggawa ranar Talatar nan kan yadda za a sake gina Gaza, ya yi kira da a tabbatar da cigaba da shigar da kayan agaji Gaza da "gaggawa". Ya buƙaci dukkan ɓangarorin su yi duk maiyiwuwa wajen tabbatar da cewa ba a koma yaƙi a Gaza ba.

Danny Elgarat

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Litinin, aka yi jana'izar Itzik Elgarat ɗaya daga cikin gawarwakin da Hamas ta miƙa Isra'ila a makon da ya gabata.

Ƙarƙashin yarjejeniyar dai wanda ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, wannan ne makon da ya kamata sojojin Isra'ila su fara janye jiki daga mashigar Philadelphi da ke kan iyakar Gaza da Misra, sannan kuma za a ci gaba da tattaunawa da manufar kawo ƙarshen yaƙin sa kuma tabbatar da sakin ragowar waɗanda ake garkuwa da su tare da sakin fursunonin Falasɗinawa.

To sai dai kuma Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce jakadan Amurka na musamman, Steve Witkoff ya bujuro da wani sabon tsari.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Witkoff dai har yanzu bai sanar da sabon tsarin da ya fito da shi ba amma kuma Netanyahu ya ce za a ƙara tsawon lokacin zangon farko na yarjejeniyar da kwanaki 50 saboda watan azumin Ramadan da na ranar tuna wa bautar da Yahudawa da samun ƴancin kansu.

Bisa tsarin ƙungiyar Hamas za ta saki rabin mutanen da suka rage a hannunta ba tare da ɓata lokaci ba kamar yadda Netanyahu ya ce. Isra'ila ta ce har yanzu akwai mutum 59 da Hamas ke riƙe da su kuma an haƙƙaƙe cewa kimanin 24 na da rai.

A ranar Litinin Hamas ta yi watsi da yadda aka samu sauyi "a wani yunƙuri da Isra'ila ta yi na ƙin mutunta yarjejeniyar farko da kuma zamewa daga shiga tattaunawa a zango na biyu."

Ƙungiyar tana amfani da mutanen da ta yi garkuwa da su ne a matsayin wani abu mafi muhimmanci da take dogaro da shi kuma za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta ci gaba da yin garkuwa da su har sai wannan kiki-kaka ɗin ya zo ƙarshe bisa sharuɗɗan da take ganin sun yi mata daidai.

A ranar Litinin, ministan harkokin wajen Misra, Badr Abdelatty ya nanata cewa " babu wata hanya da za a bi face dukkan ɓangarorin sun tabbatar da aiwatar da abin da aka rattaɓa wa hannu a watan Janairu."

Falasɗinawa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Rahotanni sun ce sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa guda biyu a kudancin Gaza ranar Litinin.

Kafafen watsa labarai na Isra'ila sun wallafa rahotannin da ke nuna wani daftarin da Egypt ta fitar na tabbatar da Hamas ta saki mutum uku na waɗanda take garkuwa da su da kuma gawar ƙarin wasu mutum uku, domin samun ƙarin lokacin yarjejeniyar da mako biyu inda ita kuma Isra'ila za ta janye daga mashigar Philadelphi da kuma titin Salah-al-Din.

Sai dai kuma wani jami'in diflomasiyya na ƙasar Larabawa da ke da masaniya kan tattaunawar da ake yi ya ce har yanzu ba su koma teburin tattaunawar ba a Alqahira duk da dai "tawagar da ke tattaunawar na ganawa da juna a koyaushe."

Za a yi ta samun yanayi mai haɗari a daidai wannan lokaci.

Babban burin firaiminista Netanyahu dai shi ne karya lagon ƙarfin sojin da na siyasa da Hamas ke da shi.

Irin ƙarfin da Hamas ta nuna lokacin sakin Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su ya ɓaƙanta wa Isra'ilawa, duk da cewa an karya lagon Hamas amma har yanzu tana da cikakken iko a Gaza.

Majiyoyin diflomasiyya na ƙasashen Larabawa sun ce a lokacin da Hamas ta amincewa cewa ba za ta ci gaba da gudanar da al'amuran Gaza ba bayan ƙarshen yaƙin, amma ba za ta ruguza irin ƙarfi da ikon da ya rage mata ba.

Isra'ila da ƙawarta Amurka ba za su amince da hakan ba.

Isra'ilawa na yawan yin zanga-zangar matsin lamba ga gwamnati.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Iyalan Isra'ilawan da hamas ke garkuwa da su na roƙon gwamnati ta cimma yarjejeniyar da za ta bayar da damar komawar ƴanuwan nasu gida.

A ranar Lahadi ne Majalisar Tsaro ta Amurka ta bayar da cikakken goyon baya ga shirin Isra'ila "na gaba. Ta ɗora laifin kocokan kan Hamas, inda ta ce ƙungiyar ta nuna cewa "ba ta da sha'awar" cimma yarjejeniyar tsagaita wutar."

A wani jawabin bidiyo, firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana shugaban Amurka, Donald Trump a matsayin "babban abokin da Isra'ila ta taɓa gani a fadar White House."

To sai dai kafafen watsa labaran Isra'ila sun ce Amurka na ƙara matsin lamba kan shugabannin Isra'ila da ka da su koma yaƙi.

Irin wannan tursasawar ce dai aka ganin take jefa yarjejeniyar cikin ƙila-wa-ƙala tun ma kafin Trump ya shiga fadar White House ranar 20 ga watan Janairu.

A hannu ɗaya kuma ana samun matsin lambar daga Isra'ilawa da suka zaƙu a saki dukkan waɗanda Hamas ɗin ke garkuwa da su domin su koma gida.

A daren Lahadi, ɗaruruwan masu zanga-zanga ne suka ture shingayen da ƴansandan Isra'ila suka gindaya a wajen gidan firaimininsta da ke Jerusalem.

Yanzu haka dai dukkan ɓangarorin biyu a shirye suke da su sake komawa yaƙi a daidai lokacin da kuma suke duba damar cimma zaman lafiya bisa sharuɗɗan da suke ganin za su amfane su.