Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matan da suka fi shahara a 2025
Shahararrun matan Najeriya biyu, Ngozi Okonjo-Iweala da Mo Abudu, sun sake shiga jerin sunayen mata 100 da mujallar Forbes ta ce sun fi shahara a duniya a 2025.
Darakta janar ta ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO) da shugabar kamfanin EbonyLife Mo Abudu, sun shiga jerin sunayen shahararrun matan tare da shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen wadda ita ce ta ɗaya a jerin sunayen, da shugabar babban bankin Turai Christine Lagarde, da firaminista mace ta farko a Japan Sanae Takaichi, da Shugabar Namibiya Ndemupelila Nandi-Ndaitwah.
Har wa yau, a karon farko tauraruwar shirye-shiryen talabijin Kim Kardashian ta shiga jerin sunayen. Kim ta kasance mai mabiya miliyan 350 a shafukan sada zumunta.
Mawakiyar Amurka, Taylor Swift ma na cikin jerin sunayen. Ta zama hamshakiyar attajira a Oktoban 2023, inda ta samu kuɗin da suka kai dala biliyan ɗaya, kuma ta samu kuɗaden ne daga waƙoƙinta kaɗai.
Mujallar da ta wallafa jerin sunayen a intanet a ranar Laraba, 10 ga watan Disamba ta lissafa mata ne da suka yi tasiri a harkokin kasuwanci da siyasa, da al'adu, da kuma shugabancin duniya.
A jerin sunayenta karo na 22 wadda ta ke fitarwa shekara-shekara na mata 100 mafi shahara a duniya, Forbes ta zaƙulo shugabanni mata, da masu kirkire-kirkire, da masu kawo sauyi da suka tsara yanayin duniya a 2025.
Baki ɗaya waɗanda ke jerin sunayen samu jimillar kuɗaɗen shiga da suka kai dala triliya 4.9 sun kuma dauki ma'aikata miliyan 9.3, sun kuma yi tasiri a ƙasashen da ke wakiltar fiye da rabin kuɗaɗen da ake samu a cikin ƙasashe (GDP) na duniya.
Forbes ta ce jerin sunayen na 2025 ya lissafta mata ne da suka kasance a matsayin misalan juriya a lokutan tashin hankali a duniya.
Mataimakiyar shugaban mujallar Moira Forbes, ta ce "Yayin da ake samun sauye-sauye da dama a duniya, matan da ke jerin sunayen bana sun sanya hannu a tsare-tsare da al'amuran da su ka yi matuƙar tasiri kan ɓangarorin tattalin arziki daban-daban na duniya ."
Yadda Forbes ta zaɓo matan
A cewar Forbes, akwai manyan ma'auni guda huɗu waɗanda suka haɗa da kuɗi, da kafofin watsa labarai, da kuma tasiri a bangarorin daban-daban, wand aka yi amfani da su wurin zukulo matan da aka sanya a jerin sunayen bana.
Har ila yau, an yi la'akari da sassa shida da suka shafi kasuwanci, da fasaha da kudi, da kafofin watsa labarai da nishaɗi da siyasa da manufofi, da kuma agaji.
A cikin jerin sunayen mata 100 da suka fi shahara a duniya, akwai waɗanda suka taka rawar gani a fagen fasaha da ƙirƙirarriyar basira ta AI da shugabanin ƙasashe.
A ɓangaren shugabannin siyasa, Forbes ta yi la'akari da yawan kudin da ƙasar ta samu a cikin gida (GDP) da yawan al'umma; a ɓangaren shugabannin kamfanoni, an yi la'akari da kuɗaɗen shiga, da kiman darajar kamfanin da kuma adadin ma'aikata.
Jerin sunayen wannan shekarar ya ƙunshi mata daga ƙasashe 25, waɗanda suka haɗa da ƙarin ƙasashen da suka shigo a karon farko kamar su Namibiya da Lithuania, kuma kaso mafi yawa sun fito ne daga Arewacin Amurka wanda ke da sunaye 50. Akwai Sabbin mutane 17 da suka samu shiga jerin sunayen bana.
Jerin sunayen mata da suka fi shahara a duniya a 2025
Matan Afirka biyar ne suka samu shiga jerin sunayen mata mafi shahara a duniya. Sun haɗa da:
- Mary Vilakazi - CEO, FirstRand Group (N0. 75)
Vilakazi ta zama shugabar kamfanin FirstRand Group na Afirka ta Kudu a watan Afrilun 2024. Ta karɓi ragamar tafiyar da kamfanin da ke ɗaya daga cikin manyan bankunan Afirka. Ya zuwa watan Yuni 2025, bankin na da rand tiriliyan 2.5 (kimanin dala biliyan 150) a cikin jimlar kadarorinsa.
- Netumbo Nandi-Ndaitwah - Shugabar Namibia (N0. 79)
A ranar 21 ga Maris, 2025, a daidai ranar da Namibiya ta cika shekaru 35 da samun ƴancin kai, Netumbo Nandi-Ndaitwah ta zama shugabar ƙasa mace ta farko.
Nandi-Ndaitwah ta shafe fiye da shekaru 30 ta na hidimar gwamnati a manyan ma'aikatu da manyan muƙamai, wanda ya ba ta ƙwarewa a fannin ilimi.
Lokacin da ta hau karagar mulki, ta naɗa majalisar ministoci mai ɗauke da kashi 57% na mata, mafi girma a tarihin ƙasar.
- Mpumi Madisa - CEO, Bidvest (N0. 89)
Mpumi Madisa ita ce shugabar kamfanin Bidvest, ɗaya daga cikin manyan kamfanonin Afirka ta Kudu, wanda ke da kusan ma'aikata 130,000 da kuma kusan darajar dala biliyan 5 a kasuwannin hannun jari.
A lokacin da ta zama shugaba a 2020, Madisa ta zama Bakar fata mace ɗaya tilo da ke shugabantar ɗaya daga cikin manyan kamfanoni 40 na kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Johannesburg.
- Ngozi Okonjo-Iweala - Darekta Janar, hukumar ciniki ta duniya (WTO) (N0. 92)
Madam Okonjo-Iweala kwararriya ce a fannin tattalin arziki kuma ƙwararriya a fannin ci gaban ƙasa, ta sami ƙarin gogewa na shekaru 30 yayin da ta yi aiki a Asiya, da Afirka, da Turai, da Latin Amurka da kuma Arewacin Amurka.
A watan Maris na 2021, ta zama mace ta farko kuma ƴar Afirka ta farko da ta zama Darakta-Janar na Ƙungiyar Ciniki ta Duniya.
Tun da farko dai, Okonjo-Iweala ta yi wa'adi biyu a matsayin ministar kuɗin Najeriya, daga 2003-2006 kuma da 2011-2015; Ta kuma yi aiki a takaice a matsayin ministar harkokin waje na 2006.
- Mo Abudu - shigabar kamfanin EbonyLife Media (N0. 98)
Shahararriyar ƴar jaridan Najeriya Mo Abudu na ɗaya daga cikin mata masu ƙarfin faɗa a ji a duniya.
A shekara ta 2006, Abudu ta kafa kamfanin Ebonylife TV, wata hanyar sadarwa da ke watsa shirye-shirye a fiye da ƙasashe 49 a fadin Afirka, tare da Burtaniya da kuma yankinCaribbean.
A cikin shekarun da suka gabata, EbonylifeTV ya shiga manyan yarjejeniyoyin haɗin gwiwa tare da Sony Televisions, da AMC Networks da Netflix.
Mata 10 da ke kan gaba a jerin sunayen su ne:
- Ursula von de leyen - Shugaban Hukumar Tarayyar Turai: Ita ce mace ta farko da ta fara aiki a wannan matsayi, wacce ke da alhakin aiwatar da dokar da ta shafi fiye da mutane miliyan 450 na Turai.
- Christine Lagarde - Shugabar Baabban bankin Tarayyar Turai : Lagarde ta zama mace ta farko da ta shugabanci babban bankin Turai a ranar 1 ga Nuwamba, 2019.
- Sanae Takaichi - Firaministar Japan: A watan Oktoba 2025, an zaɓi Sanae a matsayin Firaminista na Japan, a karon farko a tarihin ƙasar da mace ta riƙe mukamin.
- Giorgia Meloni - Firaministar Italiya: A ranar 22 ga Oktoba, 2022, Giorgia Meloni tazama Firaminista Italiya, ta zama mace ta farko a tarihi da ta riƙe mukamin.
- Claudia Sheinbaum - Shugabar ƙasar Mexico: Claudia Sheinbaum ta kafa tarihi ne inda aka zaɓe ta a matsayin mace ta farko da ta zama shugabar ƙasar Mexico a watan Yunin 2024.
- Julie Sweet - Shugabar kamfanin Accenture: Ta zama shugabar kamfanin ne a watan Satumban 2019.
- Mary Barra - Shugabar kamfanin General Motors: Ta fara jan ragamara kamfanin ne a shekarar 2014, Barra ita ce mace ta farko da ta jagoranci ɗaya daga cikin manyan kamfanoni masu ƙera motoci guda uku na Amurka.
- Jane Fraser - Shugabar Bankin Citi: A watan Maris ɗin 2021 ne aka zaɓi Fraser a matsayin mace ta farko da za ta shugabanci Citi a tarihin bankin.
- Abigail Johnson - Shugabar Fidelity Investments: Ita ce shugabar kamfanin tun 2014 lokacin da ta karɓi ragamara daga hannun mahaifinta.
- Lisa Su - Shugabar AMD: Su Ita ce shugabar kamfanin kera kayayyakin fasaha na Advanced Micro Devices, eadda ke taka rawar gani a ɓangaren ƙere-ƙeren fasaha a duniya.