Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ganawar Peter Obi da Goodluck ke nufi a siyasar Najeriya
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
Babu shakka ganawar da tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi da Peter Obi ta ƙara jawo muhawara da kuma matso da babban zaɓen ƙasar da za a yi a 2027 kusa a zukatan mabiya harkokin siyasar ƙasar.
Jiga-jigan adawar biyu daga kudancin Najeriya sun gana ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin da haɗakar 'yan hamayya ke ci gaba da ɗaukar salo iri-iri domin tunkarar jam'iyar APC mai mulki.
Duk da cewa Obi na iƙirarin har yanzu shi ɗan jam'iyyar Labour (LP) ne, yana kuma cikin ƴan hamayyar da suka dunƙule a jam'iyyar haɗaka ta ADC.
Kazalika, duk da shi ma Jonathan bai taɓa bayyana ficewarsa daga babbar jam'iyyar adawa ta PDP ba, bai cika shiga ayyukan jam'iyyar ba tun daga lokacin da ya faɗi zaɓe a 2015, abin da ya sa ake yi masa kallon ya dawo daga rakiyarta musamman a yanzu da take cikin rikici tsamo-tsamo.
Ana iya cewa babban abin da haɗuwar 'yansiyasar biyu ke nufi shi ne yunƙurin yi wa APC taron dangi bayan ta shafe shekara 10 tana mulkin Najeriya.
Me Jonathan da Obi suka tattauna?
"Yau [Alhamis] a Abuja na gana da ɗan'uwana dattijon ƙasa, jagora, kuma tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan," a cewar Peter Obi cikin wani saƙo da ya wallafa ɗauke da hotonsu tare a dandalin X.
"Mun yi tattaunawa mai amfani a ɓoye kuma muka yi nazari kan halin da ƙasarmu ke ciki," kamar yadda ya bayyana.
Duk da cewa Obi bai yi wani ƙarin bayani ba, ana ganin tattaunawar tasu ba za ta wuce ta neman yin haɗaka domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu ba a 2027.
"Babu mamaki sun tattauna ne kan yadda ake kiraye-kiraye a gare su da su haɗa kai wajen tunkarar jam'iyya mai mulki," kamar yadda Dr Mukhtar Bello na Jami'ar Bayero ta Kano ya shaida wa BBC.
Obi ya samu ƙuri'u masu yawa daga yankunan kudu maso gabas - inda ya fito - da kuma kudu maso kudu - inda Jonathan ya fito - lokacin da ya yi wa LP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Alaƙar ƴansiyasar biyu daɗaɗɗiya ce. "Na farko dai sun fito daga kudu. Na biyu kuma, lokacin da Peter ya koma mulkin jihar Anambra a karo na biyu Jonathan yana shugaban ƙasa," in ji Dr Bello.
'Ba zai yiwu su yi takara tare ba'
Tuni Peter Obi ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a zaɓen mai zuwa, yana mai cewa idan ya yi nasara wa'adin mulki ɗaya zai yi.
Saɓanin Obi, har yanzu Goodluck Jonathan bai ce komai ba game da takarar duk da yadda wasu ƴan PDP ke neman ya tsaya wa jam'iyyar takara. Idan Jonathan ya yi nasarar zama shugaban ƙasa wa'adin mulki ɗaya zai yi saboda ya riga ya yi ɗaya tsakanin 2011 zuwa 2015 - kafin marigayi Muhammadu Buhari na APC ya doke shi.
Sai dai kasancewarsu ƴan yankin siyasa ɗaya ta sa duk wani yunƙuri da za su yi ba zai wuce ɗaya ya mara wa ɗayan baya ba a zaɓe.
"Bisa al'ada a siyasar Najeriya, idan ɗantakarar shugaban ƙasa ya fito daga kudu sai ya zaɓo mataimkai daga arewa, saboda a samu daidaito," a cewar Dr Bello.
Sai dai ba kundin tsarin mulkin Najeriya ne ya tanadi hakan ba.
"To ka ga yiwuwar a samu takara a tsakaninsu ma ba ta taso ba. Idan kowannensu ya fito takara za su yi wa kan su mahangurɓa ne ta yadda Tinubu zai iya cin zaɓen cikin sauƙi," in ji Dr Bello.
"Bugu da ƙari, dukkansu Kiristoci ne. Kuma kowa ya ga irin ƙuri'un da Obi ya samu har tsakanin Kiristocin da ke arewacin Najeriya. Shi ma kuma Jonathan yana da irin wannan magoya bayan tsakanin Kiristoci a arewacin."