Bahagon Mai Takwasara ya buge Garkuwan Dutse a Maraba

Damben Gargajiya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Bahagon Mai Takwasara ya buge Garkuwan Dutse a Marabar Nƴanya a jihar Nasarawa, Najeriya a damben safiyar Lahadi.

Damben gasa ne na naira dubu ɗari tsakanin Bahagon Mai Takwasara Guramaɗa da Garkuwan Dutse daga Kudu.

Tun farko da aka haɗa wasan ƴan damben biyu sun nuna cewar ba sa dambe a tsakaninsu, domin aminai ne su na hakika.

Sai dai Idris Bambarewa ya sanar da su cewar da zarar an shiga da'irar dambe kowa zai iya karawa da kowa, kamar yadda kuka sani Garkuwan Dutse daga Guramaɗa yake ya koma Kudu.

Haka suka taka damben da tun farko ake ganin watakila su yi keja, tumin farko ba kisa, bayan da suka koma turmi na biyu ne aka buge Garkuwan Dutse.

Sauran wasannin gasa da aka buga a jiya, an tashi canjaras tsakanin Yahayan Tarasa Guramaɗa da Ɗan Yalon Tula daga Arewa.

Shi kuwa Bahagon ɗan Kanawa daga Kudu buge Danny Mai Takwasara ya yi Guramaɗa, inda aka tashi ba kisa tsakanin Ɗan Aliyu na Arewa da Bahagon Ali Yaro Guramaɗa da ake kira wuta-wuta.

Tun kan nan an fara da damben da Ƴar mage daga Kudu mai wuyar goyo da ya doke Garkuwan Yahaya Guramaɗa.

An buga wasannin a gidan Idris Ɓambarewa da ke Ƴan tifa a karamar hukumar Karo a jihar Nasarawa Nageriya.

Sai dai kafin damben gasa an fara da na kasuwa, domin ƴan wasan da ba sa gasa su samu kuɗi.

Wasannin kasuwa da aka yi kashe-kashe

Aljanin Nokiya ya buge Jan Idon Guramada

Autan Autan ɗan Bunza ya yi nasara a kan Bahagon Autan Kudawa

Nepar Autan ɗan Bunza ya doke Ɗan Bahagon Aliyu

Shagon Jimama ya yi nasara a kan Jan Idon Guramada

Sabon Gundumi ya buge Bahagon ɗan Aliyu

Wasannin kasuwa da aka yi canjaras

Shagon Na Jimama da Bahagon ɗan Aliyu

Zamani Autan Mamman da Ɗan kukar Maitakwasara

Paston Maitakwasara da Garkuwan Autan ɗan Bunza

Autan Makada da Garkuwan Jamawa - Ɗan Hausa

Koso da Dogon Jamilu