Su wane ne ƴan ƙabilar Druze kuma me ya sa ake kai musu hari a Syria?

    • Marubuci, BBC News Arabic and BBC News Turkish
  • Lokacin karatu: Minti 5

A baya-bayan nan rikici tsakanin dakarun gwamnatin Syria da mayaƙan ƙabilar Druze ya yi ƙamari a birnin Suweida da ke kudancin ƙasar.

Ƙungiyar sanya ido kan tabbatar da hakkin bil'adama a Syria wadda ke da mazauni a Birtaniya ta ce an kashe mutum 350 tun bayan rikicin da ya ɓarke a ranar Lahadi tsakanin ƴan ƙabilar "Druze ɗin da mayaƙan Bedouin."

Ƙungiyar ta ce cikin waɗanda aka kashe har da fararen hula 21 a wani mataki na aiwatar da hukuncin kisa daga dakarun ƙasar.

Sabuwar gwamnatin Syria - wadda aka kafa a ranar 29 ga watan Maris, 2025 - na yunƙuri ne wajen ganin ta ƙwace makaman ƙungiyoyin masu ɗauke da bindiga domin ganin ta samu amincewar al'ummar ƙabilu daban-daban na ƙasar.

Yankunan ƙananan ƙabilu da yawa - ciki har da Druze, na zargin gwamnatin Shugaban Ahmed al-Sharaa, duk da alwashin da ya ɗauka na ba su kariya.

Har zuwa baya-bayan nan, akasarin lardin Suweida da ke kudancin Syria na ƙarƙashin ikon mayaƙan ƙabilar Druze ne waɗanda suka yi watsi da tayin shiga cikin dakarun ƙasar.

Ƙabilar Druze ta rabu ne tsakanin ƙasashen Lebanon da Isra'ila da kuma yankin Tuddan Golan da kuma Syria.

A ƴan kwanakin baya-bayan nan Isra'ila ta ce ta kai wa dakarun gwamnatin Syria hare-haren bama-bomai a Suweida, wadanda suka yi iƙirarin cewa an aika su wajen ne domin dakatar da rikicin ƙungiyoyin addini.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ya umarci ƙaddamar da hare-hare kan dakaru da makaman gwamnatin Syria a yankin saboda gwamnatin na yunƙurin amfani da su ne kan ƴan ƙabilar Druze.

A nata ɓangare Syria ta yi Allah wadai da shigar gwamnatin Isra'ila cikin rikicin.

Su wane ne ƴan ƙabilar Druze?

Ƴan ƙabilar Druze wasu mutane ne masu magana da harshen Larabci, masu bin aƙidar addini ta daban.

Duk da cewa an fi sanin su da Druze, amma suna ayyana kansu da al-Muwahhidun.

Sun gina imaninsu a kan kaɗaituwar ubangiji - wanda ba a san shi ba, da ba za a iya bayyana kamanninsa ba, kuma mai iko a kan komai.

Yayin da ake yi musu kallon ɗaya daga cikin al'umomin da suka daɗe a yankin Gabas ta Tsakiya, ƴan ƙabilar Druze sun yi ƙoƙarin hada kansu wuri guda don ci gaba da wanzuwa tsawon ɗaruruwan shekaru.

A aƙidar, addininsu babu wanda zai shiga in ba wanda aka haifa a ciki ba, sannan kuma babu wanda zai fita daga addinin. Haka kuma aƙidarsu ta haramta aure daga wata ƙabilar ta daban.

Suna da litattafan addini, amma malamansu ne kawai aka yarje wa buɗewa da karanta littattafan da kuma gudanar da al'amuran addinin.

Ba sa yaɗa cikakken koyarwa da ibadun addininsu.

Saboda haka ne ake yi musu kallon al'ummar da ke gudanar da harkokinsu cikin sirri.

A al'adance da ƙabilance da kuma harshen da suke magana da shi, ana yi musu kallon Larabawa.

Amma mafi yawan ƴan ƙabilar na ayyana kansu da Druze a farko sannan Larabawa a mataki na biyu.

A ina suke zaune

Akwai ƴan ƙabilar Druze kusan miliyan 1.5 a faɗin duniya, kuma sun karkasu cikin ƙasashe huɗu, da suka haɗa da Syria da Lebanon da Isra'ila da kuma Jordan.

Kusan rabin al'ummar Druze - kimanin 700,000 – na zaune ne a Syria.

Wurin da suka fi yawa a ƙasar shi ne lardin Suweida, da ke kudancin Damascus, babban birnin ƙasar.

Wannan wuri da a baya aka fi sani da "Jabal al-Druze" – Dutsen Druze – har yanzu ana yi masa kallon cibiyar ƴan ƙabilar Druze.

A shekarar 1923 tsarin rabon kan iyaka da Birtanya da Faransa suka gudanar ya raba yankin da suke zama zuwa biyu.

Ƴan ƙabilar Druze da ke zaune a kudancin Suweida suka samu kansu a ɓangaren Jordan. A yanzu haka akwai kimanin ƴan ƙabilar kusan 30,000 da ke zaune a wasu ƙauyukan kudu da Amman, babban birnin ƙasar Jordan.

Lebanon ta ksance ƙasa ta biyu da ƴan ƙabilar Druze suka fi yawa bayan Syria, inda take da ƴan ƙabilar kusan 300,000.

Galibi suna zaune ne a Dutsen Chouf, da yankin Metn da tsibirin Teym.

A Lebanon a hukumace ana kallon ƴan ƙabilar Drize a matsayin wata ƙungiyar addini, inda aka ware musu wasu kujerun majalisar dokoki.

1967, shekara ce mai muhimmanci ga ƴan ƙabilar Druze. A wannan shekarar ne Isra'ila ta mamaye tuddan golan, wanda mallakin Syria ne.

Cikin dare aaka wargaza al'ummar a yankin, wasu suka ci gaba da zama a yankin Syria, yayin da wasu suka faɗa ƙarƙashin ikon Isra'ila.

A yau, mafi yawan ƴan ƙabilar Druze da ke zaune a ƙauyukan da aka mamaye suna jin kansu a maysatin ƴan Syria.

A faɗin ISra'ila ciki har da Tuddan Golan, akwai ƴan ƙabilar Druze kusan 150,000. Ƴan Druze ne Larabawa kaɗai a Isra'ila da ake tilastawa shiga aikin soji.

Ƴan ƙabilar Druze a Syria

A ƙarƙashin gwamnatin Bashar al-Assad, da dama cikin ƴan ƙabilar Druze sun nuna goyon bayansu ga gwamnatinsa, saboda a ganinsu haɗa kai da gwamnatin zai kare su daga rikicin yaƙin basasar da aka kwashe shekara 13 ana yi.

Da dama cikin ƴan ƙablar ba su shiga cikin ƙungiyoyi masu adawa da gwamnatinsa ba, yayin da wasu daga cikinsu suka nesanta kansu daga yaƙin basasar.

Amma a 2015 mayaƙan masu iƙirarin jihadi ƙarƙashin jagorancin Jabhat al-Nusra sun kama yankuna da dama a Daraa da kuma Tuddan Golan inda suka riƙa yi wa gwamnati barazana a lardin Suweida, lamarin da ya sa ƴan ƙabilar Druze da dama suka shiga cikin dakarun gwamnati.

Suna da nasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makaman da ke kare yankunansu daga hare-haren ƙungiyoyin Musulmi Sunni.

Sun kafa ƙungiyoyin ne a lokacin yaƙin basasar ƙasar, domin kare garuruwansu. Kuma ƙungiyoyin nasu ne ke da iko da garin Suweida.

To sai dai bayan da ƙungiyoyin Sunni suka samu nasarar tumbuke gwamnatin Assad, ƴan ƙabilar Assad sun shiga halin zaman fargaba.

Rikicin baya-bayan nan da hare-haren Isra'ila

Rikicn na baya-bayan nan ya ɓarke ne a ƙarshen watan Afrilu bayan da wani sautin murya da aka yi zargin na wani jagoran addinin ƙabilar Druze ɗin ne ya furta kalaman suka ga Annabi Muhammad (S.A.W).

Duk da cewa jagoran addinin ya musanta zargin, sannan ministan cikin gidan Syria daga baya ya tabbatar da cewa sautin na boge ne, amma rikicin bangaranci a addini ya bazu tsakanin al'umomi a faɗin ƙasar.

Tun daga lokacin ne, gwamnatin Syria ta ce dakarun tsaronta sun riƙa kai hare-hare domin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin ƙasar.

Gwamnatin Isra'ila ta ce ta kai hare-hare kan tankokin gwmanati domin hana su shiga birnin Suweida.

Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ya ce hare-haren ''gargaɗi ne ga gwamnatin Syria''.