Yadda jirgin dakon mai na Venezuela da Amurka ta ƙwace ya dinga ɓatar da sawunsa

- Marubuci, Joshua Cheetham, Paul Brown, Richard Irvine-Brown & Matt Murphy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
- Lokacin karatu: Minti 3
Jirgin ƙasa na dakon mai da Amurka ta ƙwace a ranar Laraba na da tariihin ƙirƙira ko kuma ɓoye bayanan sawunsa da zimmar ɓoye ayyukansa da kuma ko masu bin diddiginsa.
Da yammacin Laraba ne Amurka ta tabbatar da dakarunta sun ƙwace jirgin bayan sun dira kansa daga cikin jirgin helikwafta a kusa da gaɓar ruwan Venezuela.
Sashen BBC Verify ya tabbatara da sunan jirgin dakon a matsayin Skipper bayan tantance alamomi daga bidiyon da Amurka ta fitar ta hanyar shafin Trackers.com mai bin diddigin jigilar mai a duniya.
Bayanan da shafukan intanet suka fitar ba su iya bayyana ainahin kowane jirgi ba ne kuma bai bayyana inda yake ba tun daga 7 ga watan Nuwamba.
Kamfanin harkokin jigila ta kan ruwa Kpler na ganin jirgin ya sha sauke kaya a kan sauran jirage.
Sakatariyar shari'a ta Amurka Pam Bondi ta bayyana jirgin a matsayin na dakon "ɗanyen man fetur na Venezuela da Iran da aka ƙaƙaba wa tukunkumi".
Ma'aikatar baitulmalin Amurka ta fara saka wa jirgin takunkumi a 2022, lokacin da yake ɗauke da sunan Adisa, kuma an zarge shi da zama cikin "gungun masu fasa ƙwaurin fetur".
Skipper ya sha fita ƙarƙashin tutar ƙasar Guyana, amma gwamnatin ƙasar ta yi wuf ta musanta cewa jirgin mai shekara 20 "satar tutar Guyana ya yi saboda ba a can aka yi masa rajista ba".
Masana sun faɗa wa BBC Verify cewa akwai yiwuwar Skipper wani ɓangare ne na "gungun jirage" - wani rukuni masu dakon mai da ke kauce wa takunkumai ta hanyara ɓoye sawunsu.
Ɓatar da sawu
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A ƙarƙashin yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya, dukkan jiragen da suka wuce wani nauyi dole ne su dinga tafiya tare da na'urar bin sawu ko kuma tracker a Turance mai suna Automatic Identification System (AIS).
Na'urar na fitar da bayanan jirage ciki har da inda suke, kuma za a iya bin sawunsu ta hanyar shafukan intanet kamar MarineTraffic.
Sai dai akwai bayanan zirga-zirgar Skipper da ba daidai ba. A cewar shafin Marine Traffic, wuri na ƙarshe da aka ga Skipper shi ne Soroosh da ke Iran ranar 9 ga watan Yuli, inda ya isa bayan zango a Iraƙi da Daular Larabawa.
Amma Kpler ya nuna cewa wannan yunƙuri ne na kawar da hankali. Masu sharhi a kamfanin sun ce jirgin ya sha yin lodin mai daga Venezuela da Iran yayin da yake yin ƙarya game da inda yake - abin da ake spoofing a Turance.
Venezuela na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da suka fi arzikin man fetur, amma tana fuskantar takunkumai tun daga 2019 da Amurka ta ƙaƙaba mata saboda zarge-zargen maguɗi a zaɓuka.
Kamfanin ya ce na'urar AIS ɗinsa ta nuna ya je tashar Basrah ta Iraƙi ranar 7 da 8 ga watan Yuli, amma bayanai daga tashar ba su nuna ya je can ba. A madadin haka, Skipper ya kwashi lodin ɗanyen mai a Tsibirin Kharg da ke Iran, in ji Kpler.
Sai kuma ya nausa gabas, kamar yadda bayanan bin diddigi suka nuna, inda Kpler ya ce jirgin ya sauke kaya kan wani jirgi a tsakanin 11 da 13 ga watan Agusta. Daga baya aka sauke kayan a China, inda Kpler ya ce an yi ƙarya wajen bayyana hakan.
Ya koma ta Iran zuwa yankin Caribbean. Karo na ƙarshe da jirgin ya bayyana inda yake shi ne ranar 7 ga Nuwamba a kusa da gaɓar ruwan Guyana. Sai a ranar 10 ga Disamba sannan ya sake bayyana bayan kama shi da Amurka ta yi.
Masu sharhi a Kpler sun ce jirgin ya yi lodin kayan da suka kai aƙalla "gangar mai miliyan 1.1 samfurin Merey" ya zuwa 16 ga watan Nuwamba kuma ya bayyana cewa Cuba zai je.
Akwai kuma hujjar da ke nuna cewa Skiper ya sha sauke kaya kan wasu jiragen a ranar 7 ga watan Disamba, 'yan kwanaki kafin dakarun Amurka su yi masa dirar mikiya.
Hotunan tauraron ɗan'adam da Kpler ya nazarta sun nuna lokacin da ake sauke kayan, inda Kpler ya ce jirgin Skipper ne.
Wane ne ya mallaki jirgin Skipper?
Shafin MarineTraffic ya bayyana kamfanin da ke gudanar da jirgin a matsayin mazauna Najeriya, wato Thomarose Global Ventures Ltd, kuma mamallakinsa shi ne Triton Navigation Corp da ke Marshall Islands.
A 2022, ma'aikatar baitulmalin Amurka ta wani attajirin ɗankasuwar Rasha Viktor Artemov, wanda ƙasashen Yamma suka ƙaƙaba wa takunkumi, na amfani da kamfanin Triton wajen fasa ƙwaurin man fetur a duniya.
A lokacin, jami'an Amurka sun ce Mista Artemov ya yi amfani da wani gungu na jiragen ruwa sosai da aka yi wa rajista ba cikakkiya ba domin yin safarar man Iran.
Cikin bayaninta, ma'aikatar baitulmalin Amurka ta ce Triton "ya taimaka da kuma ɗaukar nauyin ayyukan Artemov".
BBC Verify na ƙoƙarin tuntuɓar kamfanonin biyu domin jin ta bakinsu.










