Abin da ya sa Saudiyya ta rage yawan kujerun aikin Hajji ga Najeriya

Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Ƴan Najeriya da dama sun bayyana fargaba kan matakin da hukumomin Saudiyya suka ɗauka na rage wa ƙasar wani kaso mai yawa na kujerun aikin Hajjin da aka ware mata.

Hukumar aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON ta sanar da cewa hukumomin ƙasar Saudiyya sun rage yawan kujerun aikin hajjin na Najeriya daga 95,000 zuwa 66,000.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar ranar Alhamis, ta ce hukumomin Saudiyya sun sanar da NAHCON cewa wuraren kwanan mutum 66,910 kawai aka keɓe wa ƙasar, wani abu da ke nuna adadin maniyyatan da aka ware wa Najeriyar.

"Wuraren kwanan da aka keɓe wa maniyyatan Najeriya a 2026 shi ne 66,910, da suka haɗa da na hukumomin alhazai na jihohi 51,513 da sauran jami'an hukumar, yayin da aka ƙebe wurare 15,397 ga kamfanonin shirya tafiye-tafiye'', in ji sanarwar.

Sai dai wani mataimaki na musamman ya ce alƙaluman ba Saudiyya ce ta bayar da su a hukumance ba sannan kuma hakan ya saɓa tsarin da Saudiyyar ke bi wajen ware wa kasashen Musulmi kujerun aikin hajji.

Me ya sa aka rage yawan kujerun?

Hukumar ta NAHCON ta ce hukumomin Saudiyyar sun ɗauki matakin ne saboda Najeria ta kasa cike kujeru 95,000 da aka ware mata a shekarar 2025.

NAHCON ta ce a shekarar da ta gabata an samu kujeru 35,872 da ba a cike su ba.

Hukumar Alhazan ta Najeriya ta bayyana damuwarta kan matakin da hukumomin Saudiyya suka ɗauka na rage wa ƙasar wani kaso mai yawa na kujerun aikin Hajjin da aka ware mata.

Akwai yiwuwar ƙara yawan kujerun?

..

Asalin hoton, Getty Images

Duk da cewa hukumomin ƙasar ta Saudiyya sun tanadi wurin kwanan ƴan Najeriya 66,910 bayanai na nuna cewa akwai yiwuwar hukumar alhazan Najeriya ta iya samun ƙarin gurabe nan gaba.

"Yanzu ba mu rattaɓa hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin bana da Saudiyya ba. Sai watan Nuwamba ne za mu rattaɓa hannun kuma a lokacin ne za a tantance yawan adadin alhazan da za yi aikin hajjin na bana da su."

Sannan kuma idan ka dubu tsarin da Saudiyya ke bi na rabon kujerun aikin hajji ga ƙasashen Musulmi za ka ga ba haka abin yake ba," in ji Ahmad Mu'azu, mataimaki na musamman ga shugaban hukumar alhazan ta Najeriya.

Sai dai Ahmad ya ce yanzu abin ya koma hannun maniyyata, inda ya kamata su yi ƙoƙari su kammala biyan kuɗaɗensu kafin ƙarewar wa'adin da aka gindaya ta yadda hukumar za ta samu ƙarfin gwiwar gamsar da hukumomin Saudiyyar.

Tsarin da Saudiyya ke bi na raba kujerun Hajji

..

Asalin hoton, Getty Images

Ahmad Mu'azu, mataimaki na musamman ga shugaban hukumar alhazan ta Najeriya ya shaida wa BBC cewa akwai ƙa'idoji da ƙungiyar ƙasashen Musulmi da Larabawa, OIC ta fitar da kuma ƙasar Saudiiyar ke la'akari da su.

"Abin da ake dubawa shi ne nawa ne yawan Musulmin kowace ƙasa?. Misali Najeriya bisa hasashen OIC a baya, yawan Musulmai ya kama miliya 95. To sai a ɗauki mutum ɗaya a cikin kowace miliyan ka ga kenan shi zai ba ka 95,000 daidai da yawan kujerun da aka ware mana a bara.

To ka ga batun cewa a bana an ba mu kujeru 65,000 zai yi wuya. Insha Allah za a kara mana lokacin da za mu zauna mu ƙarƙare al'amura a watan Nuwamba."

Ahmad ya kuma ƙara da cewa "mu ai yanzu ma muna fatan a sake waiwayar adadin Musulman Najeriya na yanzu saboda muna hasashen Musulmai a Najeriya sun wuce miliyan 120."