Saudiyya ta gindaya sabbin sharuɗɗan zuwa aikin hajji

Asalin hoton, Getty Images
Tuni dai aka fara bayyana fargaba bayan da kasar Saudiyya ta bullo da wasu sabbin tsauraran ka'idoji ga maniyyata aikin Hajjin bana.
Saudiyya ta tsaya kai da fata wajen yin aiki da sababbin ka'idojin, wanda idan ta tabbata da yawa daga cikin maniyyatan Najeriya ba za su sami damar zuwa sauke farali a aikin Hajjin da ke tafe ba.
Yanzu haka dai wasu jami'an hukumar alhazan Najeriya suna kasar mai tsarki, domin tattauna yadda za a fuskanci sababbin matakan.
Fatima Sanda Usara, mai rikon mukamin daraktar yada labarai ta hukumar alhazan Najeriyar, wato NAHCON ce, ta shaida wa BBC cewa, babban matakin da Saudiyya ta dauka shi ne da zarar an daina karbar kudin aikin hajji, to ba za su koma baya ba, ama'ana babu wanda za a karbi kudinsa daga baya.
Ta ce," A bana Saudiyya ta bayyana cewa zuwa 12 ga watan Oktoban 2025, tana so a fara tura sunayen wadanda suka biya kudinsu na aikin hajjin da ke tafe, sannan mahukuntan Saudiyyan sun ce duk wani kudi ko kwangila da za a bayar a game da abubuwan da suka shafi harkokin sufuri a Saudiyyan wajen jigilar alhazai a kasa mai tsari, to ya kamata a kammala komai zuwa ranar 12 ga watan Oktoban."
Mai rikon mukamin daraktar yada labarai ta hukumar alhazan Najeriyar, ta ce," Ta fuskar kiwon lafiya kuma, mahukuntan Saudiyya sun ce a bana duk wanda zai je aikin hajji to dole sai an tabbatar a asibiti cewa yana da koshin lafiya, sannan duk wani mai ciwon koda ko hanta da sauran cutuka masu tsanani, to ba za su je aikin hajjin a bana ba."
Ta ce," Wannan mataki kuma ya shafi masu juna biyu da masu tabin hankali.Sannan duk mutumin da ke dauke da wata cuta wadda za a iya yada ta kamar tarin fuka da Ebola da cutar zazzabin lasa, shi ma ba zai je aikin hajjin bana ba muddin aka tabbatar da cutar."
Fatima Sanda Usara, ta ce," A cikin cutukan da suka lissafa babu hawan jini da ciwon siga, to amma a lokuta da dama ana cewa masu irin wadannan cuta su rika tafiya da maganinsu da kuma shaidar cewa kana da cutar."
Ta ce," Mahukuntan Saudiyya, sun ce sun dauki wadannan matakan ne domin tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen da suka kamata domin su san iya adadin mutanen da za su je aikin hajjin daga kowacce kasa don a shirya abin da ya dace."
"Saudiyya a kodayaushe tana so ta san iya adadin mutanen da za su halarci aikin hajji a kowacce shekara domin yin tanadin duka bin da ya kamata, shi ya sa ta ke so a gama komai a kan lokaci don gudun fuskantar matsala ko kuma suma kansu alhazan su rasa samun kulawar data dace." In ji ta.










