Kane zai buga wa Ingila wasa na 100 a karawa da Finland

Asalin hoton, Getty Images
Harry Kane zai yiwa tawagar Ingila wasa na 100 ranar Talata a lokacin da za ta karɓi bakuncin Finland a nations League a Wembley.
Cikin karawa 99 da Kane ya yiwa Ingila ya zura ƙwallo 66 a raga, shi ne kan gaba a wannan ƙwazon a tawagar a tarihi.
Ya yi kan-kan-kan da Wayne Rooney a baya da ya ci ƙwallo na 53 a bugun fenariti a kofin duniya a 2022 a kwata fainal a karawa da Faransa.
Sai a wasannin neman shiga Euro 2024, Kane ya ɗora a kan zura ƙwallaye a raga a wasan da Ingila ta doke Italiya.
Daga nan ya ci gaba da zazzaga ƙwallye a raga sama da 12, hakan ya sa ya shiga jerin waɗanda suka zura ƙwallo 30 a babbar gasar duniya kamar bajintar Edin Dzeko na Bosnia and Herzegovina ya yi.
Yana bukatar cin ƙwallo uku nan gaba ya shiga jerin ƴan wasa 25 masu wannan bajintar, idan ya zura biyar a raga, zai faɗa cikin ƴan wasa 20 masu ƙwazon cin ƙwallaye.
Kane ya ci ƙwallo uku rigis karo biyar, ya fara a kan Panama a gasar kofin duniya a 2018 a Faransa.
Daga cikin wasu da ya ci uku rigis sun haɗa da Bulgaria da Montenegro a wasannin neman shiga Euro 2020 da karawar neman shiga kofin duniya na 2022.
Kaso ɗaya daga cikin ƙwallayen da ya ci a fenariti ne wato guda 22 - ya yi wasa shida a jere yana ci wa Ingila, karo uku yana wannan ƙwazon.
Ya zura ƙwallo tara a raga a wasa na 22 zuwa 27 da ya buga wa Ingila, tsakanin Oktoban 2017 zuwa Yulin 2018.
Ya kuma ci 10 a fafatawa ta 40 zuwa 45, tsakanin Satumba zuwa Nuwambar 2019, ya kuma ci bakwai a wasa na 79 zuwa na 84 daga gasar kofin duniya a 2022 zuwa Yulin 2023.
Wasan da ya daɗe bai ci ƙwallo ba shi ne karo bakwai a lokacin da ya buga wa Ingila tamaula daga karawa ta 28 zuwa ta 34 a manyan gasar duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A mukamin ƙyaftin ɗin Ingila karkashin Gareth Southgate, ya kusan lashe manyan kofi biyu, tun bayan da Ingila ta yi nasarar cin kofin duniya a 1966, shi ne mafi ƙwazon kasar.
Kane ne ya lashe takalmin zinare a gasar kofin duniya a 2018 da cin ƙwallo shida, inda Ingila ta kai daf da karshe da Crotia ta yi waje da ita a bugun fenariti.
Ingila ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Italiya a Euro 2020, Kane ya zura ƙwallo huɗu a raga, sannan Sifaniya ta doke ta 2-1 a Euro 2024, Kane ya ci ƙwallo uku a gasar da lashe takalmin zinare tare da ƴan wasa biyar.
Ƙwallo biyun da ya zura a raga a kwata fainal a kofin duniya a 2022, shi ne rashin ƙwazon da Kane ya yi a babbar gasa karkashin Southagate.
Kane shi ne kan gaba a yawan ci wa Ingila ƙwallaye a gasar cin kofin nahiyar Turai tare da Alan Shearar da kowanne keda bakwai.
Yana kuma kan-kan-kan da Garry Lineker da kowanne ya ci ƙwallo 10 a Ingila a gasar kofin duniya.
Kane ya ci ƙwallo 17 a wasan neman shiga gasar kofin duniya da zura 23 a wasannin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da uku a Nations League da takwas a wasan sada zumunta.
Kane zai zama ɗan wasa na 10 da zai yi wa Ingila wasa 100, inda Wayne Rooney shi ne na daga baya bayan nan.
Peter Shilton, shi ne mai tsaron raga tilo da ya buga karawa 125 a tawagar Ingila, sai Rooney mai 120.
David Beckham ya buga wa Ingila karawa 115 da Steven Gerrard mai fafatawa 114 da kuma Bobby Moore mai wasa 108 a tawagar Ingila.
Sauran da suka yi wa Ingila wasa 100 ko fiye da hakan sun hada da Ashley Cole da Sir Bobby Charlton da Frank Lampard da kuma Billy Wright.
Kane ya buga karawa 72 a mukamin ƙyaftin ɗin Ingila da yin wasa 81 karkashin Southagate da fafatawa 16 a jagorancin Roy Hodgson da wasa ɗaya lokacin Sam Allardyce da ɗaya karkashin Lee Carsley.











