'Shara': Ƴan Somaliya na mayar wa Trump martani kan 'aibata' su

Asalin hoton, Aj Awer
- Marubuci, Brandon Drenon
- Lokacin karatu: Minti 4
Amurkawa ƴan asalin Somalia da ke Minnesota sun bayyana ƙaruwar fargabar da suke ciki bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ƙara zafafa caccakar da yake yi wa ƴan yankin tun daga farkon wannan makon.
Jagororin yankin sun shaida wa BBC cewa suna cikin fargaba tun bayan kalaman na Trump, inda a ciki ya bayyana cewa ba ya son zaman ƴan Somalia a Amurka, sannan kuma "ƙasar za ta ci gaba da shiga matsala idan ta ci gaba da barin su."
"Idan shugaban ƙasar Amurka yana sukarka, dole ka shiga tashin hankali domin ba abu ba ne mai kyau," in ji Aj Awed, shugaban yankin Cedar-Riverside, yankin da ake wa laƙaci da Mogadishu saboda yawan ƴan Somalia.
Mr Awed ya ce za su zauna domin tattauna barazanar da suke fuskanta tare da tunanin yadda za su yi game da taron shekara-shekara da suke yi, wanda ya kamata su yi a ƙarshen wanan makon.
"Matsalar ita ce yawancin waɗanda suke cikin babbar barazanar su ne mutanen da ba sa jin Ingilishi sosai ko kuma suke magana da harshe irin namu, amma kuma mutane ne da suke zaune a ƙasar tsawon gomman shekaru," in ji shi.
Ya ƙara da cewa, "kawai don mutum ba ya jin Ingilishi sosai ko kuma don harshensa daban ne bai kamata a ce ya zama ƙasƙantacce ba."
Trump ya caccaki ƴan Somalia ne a fadar gwamnatin ƙasar a ranar Talatar da ta gabata, inda ya ce, "ba na son ƴan Somalia a ƙasar nan, maganar gaskiya ke nan. Wataƙila wannan ne ya sa ƙasarsu ba ta samun cigaba," in ji shi.
Awed ya ce kalaman suna da matuƙar "hatsari," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa, "bai dace a ce shugaban ƙasa yana sukar ƴan ƙasarsa ba."
Ya ƙara da cewa irin wannan zazzafar sukar na sa mutum ya zama "ɓatagari."
Kalaman Trump na zuwa ne bayan zargin cin hanci da rashawa da ake yi kan shirin tallafi da aka yi a Minnesota.
Ana tuhumar gomman mutane da rashawa, lamarin da masu shigar da ƙara na gwamnatin ƙasar suka ce suna zargin gwamnatin Minnesota da hannu a sama da faɗi da wasu kuɗaɗe da aka bayar a matsayin tallafi domin ciyar da ƙananan yara a lokacin annobar Covid-19.
An samu hannun wasu Amurkawa ƴan asalin Somalia a badaƙalar, wadda ta janyo wa jihar asarar miliyoyin daloli.
Duk da cewa waɗanda ake tuhumar ƴan kaɗan ne a cikin mutanen na Minnesota, Trump ya caccake su baki ɗaya, inda ko a watan jiya ya wallafa a shafukan sada zumunta yana alaƙanta jihar da zama "matattarar masu safarar kuɗi."
Tuni majalisar Amurka ta ce za ta ƙaddamar da bincike kan gwamnan Minnesota Tim Walz kan yadda ya gudanar da bincike kan lamarin.
'Muna cikin tashin hankali'
Jamal Osman, wanda mamba ne a majalisar birnin Minneapolis, ya ce ya koma Amurka ne tun yana da shekara 14 a duniya.
"Duk wani wanda yake kama da ni yana cikin tashin hankali da fargaba," in ji shi a zantawarsa da BBC.
"Mutanenmu na cikin fushi, da gaske akwai masu aikata laifi, amma bai kamata a ce an tuhumi dukkan mutanen gari ba saboda laifin wasu ƴan ƙalilan."

Asalin hoton, Abdilatif Hassan
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"ICE, wato hukumar tabbatar da dokokin taƙaita shiga Amurka ta riga ta fara aiki," in ji Kowsar Mohamed, wadda ke zaune a kudancin Minneapolis, birnin da ke ɗauke da sama da ƴan Somalia 80,000.
"Ana shigowa ana tare mutane ana tambayar su wace irin shaidar zama suke da ita. Wannan ba tsari ba ne mai kyau," in ji ta.
"Yawancin mutanenmu suna da cikakkiyar shaida, don haka ba wannan muke fargaba ba, fargabar ita ce za a iya yin kuskure."
Akwai rahotanni da nuna cewa jami'an tsaron gwamnatin ƙasar suna kama ƴan Amurka ƴan asalin wasu ƙasashen, inda ƙididdigar ProPublica ta nuna cewa an samu irin hakan sau 170.
An ga wasu faye-fayen bidiyo da suke nuna jami'an ICE suna fasa motoci tare da kama mutane, lamarin da ya ƙara ta'azzara fargabar baƙin da ke ƙasar.
Sai dai kakakin sashen tsaron cikin gida, wanda ke kula da ayyukan ICE ya ƙaryata zargin, inda ya ce ƙanzon-kurege ne kawai.
"Ba ma amfani da launin fata da ƙabilanci a ayyukan ICE, muna duba masu zama ba bisa ƙa'ida ba ne."
Ƙungiyoyi ƴan fafutika a Minnesota sun ce suna ƙara ƙaimi wajen jiran ko-ta-kwana saboda barazanar ta Trump.
Kowsar ta ce tuni sun fara tattaunawa tare da neman masana shari'a, sannan suna horar da mutanensu kan dokoki domin sanin ƴancinsu.
Haka kuma sun ce suna tattara lambobin wayar kar-ta-kwana, sannan sun buɗe zaurukan Whatsapp inda za su riƙa zantawa tare da tura duk abubuwan da suka gani domin nusar da ƴanuwansu.
"Maganar fargaba akwai ta, muna cikin tashin hankali. Don haka dole kowa ya kasance cikin shiri da taka-tsantsan," in ji Kowsar.
Ta ƙara da cewa za su ci gaba da bibiya tare da tattaunawa kan halin da ake ciki, da abubuwan da za su iya biyo baya, "akwai matsala amma," in ji Kowsar a zantawarta da BBC.










