Chelsea za ta taya Vinicius, Madrid da manyan ƙungiyoyin na gogayya kan Wharton

Hoton Vinicius Jr

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Chelsea na neman gabatar wa Real Madrid tayin kuɗi da wasu tsarabe-tsarabe da suka kai fam miliyan 130 domin shawo kan ƙungiyar ta Sifaniya ta sayar mata da Vinicius Jr, ɗan Brazil mai shekara 25. (Fichajes)

Real Madrid ta shirya gogayya da Chelsea, da Liverpool, da Manchester City da kuma Manchester United a kan ɗan wasan tsakiya na Crystal Palace Adam Wharton, na Ingila, mai shekara 21 (AS)

Crystal Palace ɗin na da burin sayen 'yan wasa da dama a watan Janairu - 'yan wasan da suka haɗa da ɗan bayan Bayern Munich, Sacha Boey, na Faransa mai shekara 21, da ɗan wasan tsakiya na Wolves Joao Gomes, na Brazil, mai shekara 24, da kuma ɗan wasan tsakiya na Auxerre Kevin Danois, ɗan Faransa mai shekara 21. (Mail+)

AC Milan ta sa ido a kan yadda za ta kaya game da ɗan bayan Manchester City, Nathan Ake, ɗan Netherlands mai shekara 30, yayin da suke nazari a kan wasu ƙarin 'yan wasan da dama, idan ba su same shi ba. (Corriere dello Sport)

Ɗan wasan Argentina mai kai hari Taty Castellanos, mai shekara 27, na shirin zuwa a gwada lafiyarsa a West Ham kafin kammala cinikinsa daga Lazio a kan fam miliyan 27. (Talksport)

Tottenham ta tura masu farauto mata 'yan wasa su kalli yadda ɗan wasan gaba na gefe Maghnes Akliouche ɗan Faransa zai taka rawa a karawar Monaco da Lyon ranar Asabar. (Teamtalk)

Eintracht Frankfurt na tattaunawa da Newcastle a kan cinikin William Osula, mai kai hari na Denmark, mai shekara 22. (Florian Plettenberg)

Ɗan wasa gaba na gefe Omar Marmoush, mai shekara 26, na ɗaukar hankalin Aston Villa da Tottenham, amma kuma shi ya fi son ya tsaya ya ci gaba da fafutukar neman guri a Manchester City. (Football Insider)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bournemouth na gogayya da Fiorentina, da Cagliari da kuma Genoa a kan ɗan wasan tsakiya na Atalanta, Marco Brescianini, ɗan Italiya mai shekara 25 (Calciomercato)

Tottenham ta mayar da hankali a kan ɗan bayan Udinese Oumar Solet, ɗan Faransa mai shekara 25, amma kuma tana fuskantar gogayya daga Chelsea da Crystal Palace. (Caught Offside)

Sunderland za ta bar Luke O'Nien, mai shekara 31, ya bar ƙungiyar a wannan watan na Janairu, inda Birmingham, da Coventry da kuma West Bromwich Albion ke nuna sha'awarsu a kan ɗan bayan, ɗan Ingila. (Chronicle)

Watford na son karɓar aron ɗan bayan Bournemouth Julio Soler, ɗan Argentina mai shekara 20. (Fabrizio Romano)

Barcelona na nazari a kan tayin fam miliyan 70 da Sunderland ta gabatar mata a kan ɗan wasanta na gaba na gefe Fermin Lopez na Sifaniya mai shekara 22. (Fichajes)

Bisa ga dukkan alamu ɗan wasan gaba na gefe na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 31, zai samu damar nbarin Chelsea a watan nan na Janairu, inda Newcastle ta zama ƙungiyar Firemiya ta baya-bayan nan da ta nuna sha'awarsa. (Football Insider)