Ba zan sauka daga shugabancin PDP ba - Iyorchia Ayu

Asalin hoton, Iyorchia Ayu
Shugaban jam’iyyar PDP a Najeriya Iyorchia Ayu ya ce ko a jikinsa game da kiraye-kirayen da wasu suke yi cewa ya sauka daga kan mukaminsa.
Kazalika ya ce masu yin hakan yara ne da ba su fahimci manufofin kafa jam’iyyar ba.
A hirarsa da BBC, tsohon dan Majalisar Dattawan Najeriyar ya ce a iya saninsa ‘yan kasar ne suka zabe shi bisa sharuddan da jam'iyyarsu ta shata.
Ya kara da cewa ko a lokacin da za su gudanar da zaben shugabannin PDP na kasa, an yanke cewar ba za a yi la'akari da bangaren da shugaban jam’iyyar ya fito ba wurin fid da dan takarar shugaban kasar.
An jima ana kai ruwa rana tsakanin jam'iyyar da dan takarar shugaban kasa da ya sha kaye a zaben fid da gwani, wato gwamnan Rivers Nyesom Wike, wanda rahotanni suka ce ya gindaya sharuddan ci gaba da zama jam'iyyar, da kuma mara wa Atiku Abubakar baya a matsayin dan takararta a zaben 2023.
Daga cikin sharuddan akwai bukatar Shugaban jam'iyyar Iyorchia Ayu, wanda ya fito daga Arewacin Najeriya ya sauka daga mukaminsa.
Sai dai a martanin da ya yi da BBC ta tambaye shi, Mr Ayu ya ce ba bu inda za shi, la'akari da cewa an zabe shi ne bisa dokokin da jam'iyyar PDPn ta shimfida, a don haka ba zai sauka ba saboda kawai wasu ba sa son ganin shi a kai.
''An zabe ni na Shugabanci PDP har tsawon shekaru hudu, yanzu ban kai shekara daya ba ma.
''Maganar zaben Atiku ba ta shafi mukamin Shugaban jam'iyya ba. Ni na ci zabe. A cikin kundin tsarinmu muka yi wannan.'
''Ba wani laifi da na yi, ina gyara jam'iyya ne, hayaniyar da ake yi wallahi ba ta dame ni ba,'' in ji Mr Ayu.
Shugaban PDP ya kara da cewa ''ni dai na san ina yin aiki, ban saci kudi ba, ban yi wani laifi ba, don haka ban ga abin magana ba.''
Sai dai kuma ya musanta batun cewa rashin dinke baraka da Gwamna Wike zai iya kawo wa jam'iyyar cikas a zaben na 2023, inda yace su suka asassa jam'iyyar PDP a Najeriya, saboda haka 'wasu yara' da ba su san gwagwarmayar da suka sha ba ba za su iya basu matsala ba.
''Lokacin da muka fara tafiyar PDP wadannan yara bamu gan su ba. Su yara ne basu san abunda yasa muka kafa wannan jam'iyyar ba.
"Ba za mu yarda mutum daya ya zo ya lalata mana jam'iyya ba,'' a cewar Ayu.

Asalin hoton, PDP
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da yunƙurin da jagororin jam'iyyar PDP suka yi na rarrashin Wike, har yanzu gwamnan bai nuna alamun ajiye kayan yaƙinsa ba, inda a baya-bayan nan yake ci gaba da hulɗa da jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
To amma kuma Wike bai fito karara yace zai yaƙi tafiyar Atiku ba, duk da ba ya shiga dukkan ayyukan jam'iyyar, hasali ma ya fi yin hulɗa da 'yan sauran jam'iyyu ciki hadda babbar abokiyar hamayyarsu wato jam'iyyar APC mai mulki.
Sai dai a cikin makon da ya gabata dan takarar Shugabancin kasa na PDPn Atiku Abubakar da wasu gwamnonin jam'iyyar sun gana da Wike a birnin London na Burtaniya, inda ake kyautata zaton suna ci gaba da rarrashin gwamnan na Rivers ne game da bukatar ya rungumi tafiyar Atikun.
To amma kawo yanzu Wike bai fito ya bayyana matsayarsa ba, don kuwa ko bayan jiga-jigan PDPn, ya sa labule da wasu yan takarar Shugaban kasa a jam'iyyun hamayya, da suka hada da Bola Tinubu na APC da kuma Peter Obi na Labour Party.
Sai dai kuma yayin da PDP ke fadi tashin dinke baraka da Wike, kwatsam sai gashi ta yi babban kamu a Arewacin kasar, bayan da tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya sanar da sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa PDPn.
Shugabancin PDP dama yan takararta basu yi wata-wata ba suka dira birnin Kano don karbar Malam Ibrahim Shekarau, wanda ba makawa shigarsa PDPn zai kara wa jam'iyyar tagomashi musamman a jihar ta Kano mai matukar tasiri a zaben Shugaban kasar Najeriya.










