Tantance gaskiya: Da gaske Elon Musk na goyon bayan Peter Obi a zaben 2023?

An jirkita kalaman Mr Musk awata hira da ya yi da Sam Altman na Y Combinator a watan Satumbar 2016.

Asalin hoton, Y Combinator

Bayanan hoto, An jirkita kalaman Mr Musk awata hira da ya yi da Sam Altman na Y Combinator a watan Satumbar 2016.
Lokacin karatu: Minti 2

Ana ta yada wani bidiyon bogi da ke cewa fitaccen attajirin nan na duniya mai kamfanin SpaceX da Tesla Motors Elon Musk ya goyi bayan dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi.

A bidiyon an nuna cewa Mr Musk ya yi alkawarin yin aiki tare da Mr Obi.

Wannan bidiyo, mai tsawon dakika 11, ana ta rabbara shi a shafukan WhatsApp, Twitter da kuma Facebook.

An jirkita kalaman Mr Musk awata hira da ya yi da Sam Altman na Y Combinator a watan Satumbar 2016.

A bidiyon da aka jirkita, an juya muryar Mr Musk da kalamansa inda aka sa shi yana magana a kan Peter Obi.

Tuni dai bidiyon ya jawo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta inda wasu magoya bayan Peter Obi suka bayyana jin dadinsu kan wannan goyon baya na bogi.

Wani mai amfani da Twitter, Benson, ya ce "tuni Elon Musk ya soma magana kan hada gwiwa da Peter Obi. Wannan kyakkyawan fata ne ga Najeriya."

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wasu kuma irin su Lanre 'Obi' Lagos sun yi ta kiraye-kirayen a tantancen sahihancin bidiyon na bogi.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Bidiyon wata manuniya ce ta irin girman matsalar labaran karya maus sarkakiya, wadanda suke da wahalar tantancewa..

Ana yin amfani da salo irin na fasahar zamani ta kwamfyuta wajen jirkita bidiyo domin yin irin wadannan labarai na karya.

Binciken da Sashen Tantance Gaskiya na BBC ya gudanar ya nuna cewa an samar da bidiyon ne ta hanyar amfani da wani shafi mai suna https://elontalks.com/, wanda ya bayar da damar jirkita bidiyon Elon Musk da sauya kalamansa.