Yadda Peter Obi ke daukar hankalin matasan Najeriya

Asalin hoton, AFP
Hamshakin dan kasuwa wanda ya yi suna wajen tsantseni, Peter Obi ya yi fitar barden guza yayin da Najeriya ke tunkarar zaben shugaban kasa a watan Fabrairu, inda yake daukar hankalin masu kada kuri'a da sako da maganganu na tsumi da tanadi, sakonnin da suka kasance sun samu karbuwa wadanda kuma tarin masu amfani da shafukan intanet ke yada su. A kasar da ke hankoron samun wanda zai fitar mata kitse a wuta, ya ceto ta daga tarin matsalolin da take ciki, matasan masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara sun daga likkafar Mista Obi zuwa wani gagara-badau, shafaffe da mai kuma dan-mowa.
Suna mara wa jam'iyyarsa ta Labour, wadda ba wata fitacciya ba ce, baya a fafatawar da za a yi ta zaben shugaban kasar tsakaninsa da wasu jiga-jigai kuma hamshakan 'yan siyasa uku.
Yawanci za ka ga sunansa na karakaina a shafukan sada zumunta da muhawara kusan a duk wata tattaunawa da ake yi a shafukan wadda magoya bayansa ke tasowa da ita, inda za ka ga hakan daga irin yadda ake sanya hotunansa, ko na alamar jam'iyyarsa mai launin fari da ja da kore.
Yawancin wadannan magoya bayan nasa matasa ne 'yan birni, 'yan kasa da shekara 30, wadanda ke bayyana kansu a matsayin, 'yan zamani, wadanda suka dogara da kansu ba da kowa ba.
Ssannan kuma suke kallon tsoffin 'yan siyasa a matsayin wadanda ba su tsinana musu komai ba. Da yawa daga cikinsu kamar irin su Dayo Ekundayo, daga yankin kudu maso gabashin Najeriya, a birnin Owerri, sun kasance 'yan gaba-gaba a zanga-zangar nan da ta yi sanadiyyar rushe rundunar 'yan-sandan nan ta musamman mai yaki da 'yan fashi da makami EndSars, shekara biyu da ta gabata, inda kuma suka karkare da neman samar da gwamnati ta gari.
A yanzu kuma wadannan matasa sun sake yunkurowa, da irin wancan salo na baya, inda suka hada dubban matasa 'yan Najeriya, tare da tara miliyoyin naira cikin 'yan makonni, domin taimaka wa wannan gwani nasu, mai shekara 60.
Suna daukarsa a matsayin wanda zai fitar musu da kitse daga wuta a wannan gogoriyo na neman shugabancin Najeriya, tsakaninsa da 'yan takarar manyan jam'iyyun da suka mamaye fagen siyasar kasar tun bayan mulkin soji a 1999.
''Wane dan siyasar Najeriya ne ya rike mukami kuma ya tsira da kimarsa? Ban ga wani kyakkyawan zabi na-gari ba ga matasa 'yan Najeriya fiye da shi,'' in ji Mr Ekundayo.
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta

Asalin hoton, Dayo Ekundayo
Gangamin soshiyal midiya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tuni ya shiga wani shiri na gudanar da wani gangami na nuna goyon baya ga Mista Obi.
Kuma yana bayar da kayayyaki da jan dalibai domin gudanar da yakin neman zaben, kamar yadda ya yi a lokacin zanga-zangar neman rushe rundunar 'yan sandan da ke yaki da 'yan fashi.
To sai dai kuma yayin da duk ake wannan, 'yan hamayyar siyasa na cewa Mista Obi, karabitin dan siyasa ne kawai, daya daga cikin ire-iren masu sammakon bubukuwa, wadanda ke fitowa a lokacin zabe suna yi wa jama'a romon-baka da kuma kurarin za su kayar da manyan jam'iyyu su kwace mulki.
Da yawa daga cikin magoya bayan babbar jam'iyyar hamayya PDP, da kuma masu lura da al'amura wadanda ba sa goyon bayan wani bangare sun yarda cewa Peter Obi, ya fi sauran 'yan takarar cancanta.
Amma kuma sun ce ba shi da karbuwa a fadin kasar, da za ta ba shi nasara, har ma suna ganin magoya bayansa za su yi asarar kuri'unsu ne kawai.
Wadannan rukunin jama'a na ganin dan tayar da kura ne kawai, wanda zai dauke hankali daga babban abin da suka sanya a gaba na kawar da jam'iyya mai mulki ta APC, wanda kuma zai haddasa rarrabuwar kuri'a.
Mabiyin addinin Kirista, dan darikar Katolika daga gabashin Najeriya, amma kuma suna nuna cewa ba shi da farin jini a yankin arewaccin kasar, wanda yawancin al'ummarsa Musulmai ne, wadanda kuma kuri'arsu tana da tasiri sosai wajen cin zaben shugaban kasa.
Kuma masu sukar lamirinsa na nuna tababa kan ko shi na daban ne a kan batun yaki da cin hanci da rashawa, abin da yake hankoro a kai, inda har ma suke nuni da cewa sunansa ya bayyana a cikin takardun (Pandora Papers) bayanan da aka taba satar fitar da su, na sunayen hamshakan attajirai a 2021.
Duk da cewa ba a zarginsa da satar kudi, amma kuma an zarge shi da kin bayyana yawan asusun ajiya na waje da kuma kadarorin da iyalansa suka mallaka, wanda ya danganta da rashin sani.
Haka kuma an zarge shi da amfani da kudin gwamnati ya sanya jari a kamfanin da yake da alaka da shi a lokacin yana gwamna.
A kan hakan ya kafe cewa shi bai yi wani abu da ya saba doka ba, kuma ma har yake cewa ai jarin da ya zuba ya karu, an samu riba.
Mista Obi ya kuma kafe cewa shi fa bai dauki burinsa na zama shugaban kasa a matsayin ko-a-mutu-ko-ai-rai ba, wato bai damu lalle ya ci zabe ba, wanda wannan abu ne sabani ga mutumin da ya sauya jam'iyya har sau hudu tun 2002.
A watan Yuni, 'yan kwanaki kafin zaben fitar da gwani, ya yi watsi da PDP, jam'iyyar da ta zabi tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, mai shekara 75 a matsayin dan takararta na zaben da za a yi a 2023.

Asalin hoton, AFP
Damar cin zabe
Masu suka sun ce ya fice ne daga neman takarar saboda ya san ba shi da wata dama sosai ta ci.
Amma shi a karan-kansa ya bayar da dalilai na rikici a jam'iyyar ta PDP, wadda ya yi mata mataimakin dan takarar shugaban kasa a 2019, a kan dalilinsa na sauya sheka zuwa jam'iyyar Labour.
Haka kuma magoya bayansa na ganin ya bar jam'iyyar ne saboda ya ki ba wa wakilai masu zabe (daliget) cin hanci a zaben fitar dan takarar.
Har wasunsu ma ke tunkaho da bugun kirji da irin tattali da tsimi da yake da su a harkar kula da kudin gwamnati a kasar da ta yi kaurin suna a almundahana da dukiyar jama'a.
Suna daukarsa a matsayin wani dan siyasa na daban, wanda ya gwamma ce ya yaki APC da PDP, jam'iyyun da ake yi wa kallon tamkar Danjuma ne da Danjummai, wadanda suke zargi da sata da almundahana.
Akwai kuma batun bambancin addini da kabilanci a game da takararsa.
A kasar da ake ganin kusan rabin al'ummarta mabiya addinin Kirista ne, magoya bayansa na ganin wannan zai ba shi damar cin zabe.
Domin bayan mulkin shekara 8 na Muhammadu Buhari, ba za su so ganin wani Musulmin walau Bola Tinubu, na APC, mai shekara 70, ko Atiku Abubakar mai shekara 75 na PDP ya jagorance su ba.
Wasu kuma suna goyon bayansa ne saboda kasancewarsa dan kabilar Igbo, kabilar da take ta uku a tsakanin kabilun kasar, kabilar da rabonta da shugaban kasa tun lokacin da Najeriya ta samu 'yanci daga mulkin mallakar Ingila, a 1960, kuma ko a lokacin ma shugaban na je-ka-na-yi-ka ne.
'Yan kabilar Igbo da dama na zargin gwamnatocin Najeriya da suka gabata da mayar da su saniyar-ware, kuma hakan ya sa suke ganin idan Obi ya samu mulki, zai raya yankin kudu maso gabas yankin da yawancinsu suka fito.
Kuma hakan zai kawar da hankoron kungiyoyin 'yan a-ware irin su Ipob ( Indigenous People of Biafra (Ipob).)
Mutum ne da ya karanta ilmin falsafa, ya yi aiki a harkokin kasuwanci na gidansu, kafin ya ware ya kafa nasa, inda ya rika shigo da kayayyaki Najeriya.
Kayayyakin da ya rika shigo da su sun kama daga man salad zuwa man shafe-shafe na mata da sauransu, hadi da kayan gwangwani da barasa, kari kuma a kan wannan yana da kamfanin yin giya ga kuma jari da yake da shi a bankuna uku a Najeriya.
A Najeriya daga nesa za ka iya gane biloniya idan ka hange shi, to amma Peter Obi ba haka yake ba, ya fita daban, domin ba za ka ga alamun shi hamshalkin attajiri ba ne, wanda wannan abu ne da yake alfahari da shi.
Yana gaya wa mutane cewa takalma kafa biyu kawai yake da su na kamfanin Ingila na Marks and Spencer, da kwat ta dala 200 maimakon ta wajen dala 4,000.
Kuma shi yake rike jakarsa maimakon ya biya wani ya rike masa.
Hatta 'ya'yansa ma ba su tsira daga tsiminsa ba, kasancewar ya hana dansa mai shekara 30 mota, shi kuma daya dan nasa yana koyarwa ne a makarantar furamare.
Hakan wani abu ne na daban, wanda a kasar da hatta sunan dan siyasa ke zama hanyar samun gwaggwaban aiki ga mutum baya ga tarin alfarma.
End of Wasu labaran masu alaka
Magoya bayansa
Duk da irin ce-ce-ku-cen da ake yi a game da mulkinsa a lokacin yana gwamnan jihar Anambra, salon mulkin nasa ya kasance abin nuni ko yakin neman zabe a takararsa ta shugaban kasa.
Magoya bayansa suna nuni da cewa ya zuba kudi sosai a harkar ilimi kuma ya rika biyan albashi a kan lokaci, wanda wannan abu ne mai sauki da yawancin gwamnonin Najeriya suke kawar da hankali a kai.
Haka kuma ya bar makudan kudade lalitar gwamnatin jihar bayan da ya kammala wa'adinsa biyu na shekara hurhudu, wanda wannan ma ba karamin abu ba ne a Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
To amma ba duka aka taru aka zama daya ba, domin Frances Ogbonnaya, wadda dalibar jami'a ce a lokacin da Mista Obi yake gwamna, tana mamakin yadda ake koda shi.
''Wa, mutumin da yake tsimin kudi a lokacin da ake yunwa? Wanda yake tattalin kudi a lokacin da ba kayayyakin rayuwar jama'a?'' Ina amfanin badi ba rai? in ji ta.
To amma dabi'a da al'adarsa ta tsimi da tanadi da kuma tattali ke janyo masa magoya baya da ake wa lakabi da ''OBIdients.''
Har ma ana zargin wasu daga cikin cikinsu da cin zarafin wadanda ba sa goyon bayansa a shafukan intanet da kiran wadanda ba su zabe shi ba a zaben da ke tafe a matsayin makiya kasa.
A wani sako a shafinsa na tuwita, Mista Obi ya roki magoya bayansa da su zama masu yakana da mutunta kowa, amma duk da haka ba su ji ba.
Duk mai sukarsu da cewa yawansu na tuwita hakan ba yana nufin yawan kuri'u ba ne, suna nuni da yadda suke turuwa zuwa yin rijistar zabe.
Duk da haka wannan ba daya yake ba da fita zabe a ranar zabe.
Yayin da ya rage 'yan watanni a fita filin zabe, ba shakka Mista Obi na ci gaba da samun tarin magoya baya, amma kuma masu suka na ganin rashin tasirin jam'iyyarsa a ko'ina a fadin kasar gaba daya, abu ne da zai sa tababa a kan yuwuwar cin zabensa.
Ya musanta hakan da nuni da cewa 'yan Najeriya miliyan 100 da ke cikin fatara da talauci da miliyan 35 wadanda ba su san inda za su samu abincin da za su ci ba, idan har rabin wadannan za su zabe shi to abin da yake bukata ke nan.











