Dalilin da ya sa mawaƙan Najeriya ke haɗa casu a wurin yin rajistar zaɓe

Falz arrives at the 2019 BET Hip Hop Awards on October 05, 2019 in Atlanta, Georgia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mawaƙin rap falz na nuna tutar Najeriya cikin alfahari yayin bikin kyautar BET a 2019 a birnin Atlanta na Amurka

Cikin jerin wasiƙu daga marubuta na nahiyar Afirka, marubuciya Adaobi Tricia Nwaubani ta wallafa cewa 'yan Najeriya da dama na jin cewa suna da ikon yin amfani da ƙuri'unsu wurin kawo sauyi.

Short presentational grey line

Dubban 'yan Najeriya ne suka hallara a wani wurin casu a Legas da wasu shahararrun mawaƙa suka haɗa, ciki har da mawaƙin rap Falz da kuma Teni.

Abin da kawai ake buƙata don shiga wurin shi ne katin zaɓe da zai nuna mai shi yana da ikon yin zaɓe a watan Fabarairun 2023.

"Idan ba aku yi rajistar ba har yanzu, ku zo ku yi a wurin a ranar!! Lokaci ne mai muhimmanci a gare mu. Ku faɗa wa wani shi ma ya faɗa wa wani. Nishaɗantarwa na ƙunshe da nauyi," kamar yadda Falz ya rubuta cikin wani saƙo a dandalin Instagram.

Duk da cewa saura wata takwas kafin zaɓen, casun wanda hukumar zaɓe ta INEC ta haɗa da haɗin gwiwar Yiaga Africa da ƙungiyar Tarayyar Turai (EU), ɗaya ne daga cikin hanyoyin da ake bi wajen ƙarfafa gwiwar 'yan Najeriya su yi rajistar zaɓen.

Masu mabiya da yawa a shafukan zumunta ma na ci gaba da zaburar da mabiyansu. Shugabannin addini ma na yi, inda aka ga wani fasto na faɗa wa mabiyansa cewa daga yanzu duk wanda bai yi rajistar ba ba za a bar shi shiga cocin ba cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta.

Ana yin duk waɗannan ne don jan hankalin matasa, waɗnda su ne kusan rabin al'ummar Najeriya mai mutum kusan miliyan 200. Da yawansu ba su taɓa yin zaɓen ba.

The Youths of End Sars Protesters gather to barricade the Lagos - Ibadan expressway, the oldest highway and major link to all parts of the country, on October 16, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Matasa da yawa sun fito zanga-zangar EndSars a 2020

"'Yan mata, idan wani saurayi ya tambaye ku game da mahaifiyarku, ku tambaye shi game da katin zaɓensa," kamar yadda ɗaya daga cikin masu shirya zanga-zangar EndSars Rinu Odula ta wallafa ga mabiyanta fiye da 400,000 a dandalin Twitter. "In ba katin zaɓe ba lamba."

Sai dai kuma saka mutane su yi rajista wani ɓangare ne kawai na babban aikin. A zaɓen shugaban ƙasa na 2019, kashi 35 cikin 100 na masu katin zaɓen ne kawai suka kaɗa ƙuri'a, a cewar INEC.

Zaɓen wanda ya bai wa Shugaba Muhamadu Buhari nasara a wa'adinsa na biyu, shi ne wanda aka samu mafi ƙaranci na masu kaɗa ƙuri'a tun daga 1999 - lokacin da Najeriya ta koma mulkin farar-hula.

A shekarara da ta wuce, INEC ta ce a wasu zaɓukan cike gurbi da ta gudanar, masu kaɗa ƙuri'ar sun yi ƙasa har zuwa kusan kashi 8.3 cikin 100.

Voters form a queue at a polling station in Port Harcourt, Rivers State, on March 9, 2019

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kusan mutum miliyan 84 ne suka yi rajistar zaɓe a Najeriya a 2019

Wasu 'yan Najeriyar kan ƙi fita ne saboda irin yanayin da suke tsintar kansu a wurin rumfar zaɓen.

An san yadda mutane ke shafe awanni a tsakiyar rana suna jiran layi ya zo kan su, musamman ma idan aka samu tsaiko wajen kawo kayan zaɓen, ko kuma idan na'urar tantance masu zaɓe ta tsaya da aiki.

Wani zubin zaɓen kan rikiɗe zuwa tashin hankali, zuwa harbe-harbe da kuma fitina a rumfunan zaɓe.

Wani zubin kuma masu kaɗa ba yadda suka iya illa su sayar da ƙuri'unsu ga 'yan siyasa, inda sukan yi tunanin 'yan dubunnan da za a ba su sun fi zaɓen wanda ya yi musu tarin alƙawuran kamfe waɗanda ba zai taɓa cikawa ba.

1px transparent line

Kazaliak, akwai maganar cin hanci wadda ke sa masu zaɓe tunanin ƙuri'un nasu ba su da amfani. Ko da a ce sun gama shafe awanni a rana da ruwa sun yi zaɓe, maguɗin da aka saba yi a zaɓukan Najeriya shi ne dai za a kuma yi.

Da zimmar daƙile maguɗi, 'yan gwagwarmaya na ta fafutikar a koma yin zaɓen ta hanyar latironi - kuma za a jarraba hakan a zaɓe mai zuwa.

Abu ne mai wuya a iya yin maguɗi a zaɓukan da aka yi da latironi ta hanyar sauya adadin ƙuri'u, balle ma cika akwati da ƙuri'un da aka yi dangwale ko na bogi.

Ya yi wuri sosai a iya faɗar wani ɗan takara da matasa za su zaɓa, musamman ma saboda 'yan Najeriya kusan miliyan uku ne kawai suke amfani da dandalin Twitter, a cewar wasu alƙaluman shafin Africa Check - saboa a nan ne aka fi tafka muhawara ta siyasa.

Akwai miliyoyin matasan da ba a jin muryarsu saboda ba sa kan Twitter kuma sun kai minzalin kaɗa ƙuri'a.

Zuwa yanzu, abin da INEC ta fi mayar da hankali a kai shi ne dukkansu su yi rajistar. Waɗanda za su yi zaɓe a karon farko da kuma waɗanda suke son gyara bayanansu a jikin katin dole ne su yi sabuwar rajista.

"Na roƙe ku, ku tabbatar min cewa za ku yi rajistar, ku karɓi katinku, ku kaɗa ƙuri'a," a cewar shugaban INEC Farfesa Mahmud Yakubu yayin casun na Legas.

"Ni kuma ina tabbatar muku ƙuri'unku za su yi amfani."

Presentational grey line