Ifeanyi Okowa: Atiku ya zabi gwamnan Delta a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP

Okowa

Dan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar ya zabi gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023.

Atiku ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis a wajen tantance ɗaukar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar a hedikwatar jam'iyyar da ke Abuja.

Atiku ya sanar da gwamnan jihar Delta da ke shiyyar kudu maso kudancin kasar Ifeanyi Okowa a zaman mataimakinsa ne bayan shafe kwanaki ana shawarwari da muhawara kan wanda zai tsayar.

Ya dai yi wannan sanarwar ne yayin wani taron manema labarai a hedikwatar jam'iyyar da ke birnin Abuja.

Dama an sanya ran cewa a ranar Alhamis ɗin ne jam'iyyun siyasar Najeriyar za su sanar da sunayen mutanen da za su mara baya ga 'yan takararsu na shugaban ƙasa.

A yayin da PDP ta fitar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar daga kudancin Najeriya, ita kuwa jam'iyyar APC mai mulki za ta ɗauko abokin tafiyar ɗan takararta ne daga yankin arewacin ƙasar.

Tuni dai jam'iyyar APGA ta fitar da abokin tafiyar ɗan takararta daga arewa ita ma.

An zaɓi mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasar na PDP ne ta hanyar kafa wani kwamiti don tantance mutanen da ke son mara wa ɗan takararta Atiku Abubakar baya.

PDP

Me Atiku ya ce?

Atiku ya ce shi ya ayyana a ransa dukkan wadanda aka tantance ɗin sun cancanci zama mataimakan shugaban ƙasa, "har ma shugaban ƙasar cun cancanci tsayawa takarar kujerar.

"Da a ce tsarin mulkin Najeriya kamar tsarin mulkin Musulnci yake yadda za a auri mata biyu, uku, huɗu, da sai na aure su dukansu," kamar yadda ya shaida wa BBC Hausa.

A wata sanarwa da ya fitar bayan tsayar da ɗan takarar, Atiku ya yaba wa jam'iyyar PDP kan abin da ya kira "tsara sahihin zaɓen fitdar da gwani da ya sa na zama ɗan takararta na shugaban ƙasa.

Atiku ya ce kafin a yanke shawarar tsayar da mataimakinsa a wannan takara, sai da ya yi ta tuntuɓar masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnonin jam'iyyar da kwamitin gudanawa da sauran jagorori don su bayar da tasu shawarar.

"A yayin neman waɗannan shawarwari ne, na bayyana cewa ina son mataimakin takarata ya kasance yana da ƙwarewar da zai iya gadona idan na kammala wa'adin shugaban ƙasa.

Wannan layi ne