Dalilan da suka hana Atiku da Wike sasanta rikici tsakaninsu

Attiku da Wike

Asalin hoton, PDP

Bayanan hoto, Tsohon hoton Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike na JIhar RIvers

Har yanzu sakamakon zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya bai gushe daga zukatan wasu 'yan takara ba, musamman Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike da ya sha kaye.

Duk da yunƙurin da jagororin jam'iyyar suka yi na rarrashin Wike, har yanzu gwamnan bai nuna alamun ajiye kayan yaƙinsa ba, inda a kwanan nan yake ci gaba da hulɗa da jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Duk da cewa Wike bai ce zai yaƙi tafiyar Atiku ba amma kuma ba ya shiga dukkan ayyukan jam'iyyar, hasali ma ya fi yin hulɗa da 'yan sauran jam'iyyu.

Ɓangaren Atiku na cewa sakamakon zaɓen ne bai yi wa gwamnan daɗi ba, yayin da magoya bayan Wike ke musantawa.

Kazalika, rikicin ya sake ɗaukar sabon salo bayan Atiku ya ɗauki Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin abokin takararsa na shugaban ƙasa, bayan an yi zaton Wike zai ɗauka.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin 'Yan Majalisar Amintattu na PDP da ke goyon bayan Wike ba su halarci taron da majalisar ta shirya yi ba a ranar 3 ga watan Agusta a Abuja da zimmar sasanta rikicin.

Haka nan, an ruwaito cewa Wike ya ƙi yarda ya gana da Atiku gaba da gaba, sannan ya saka sharaɗin cewa a sauke shugaban jam'iyyar na ƙasa da aka zaɓa a 2021, Iyorchia Ayu.

Wike ya zama abokin 'yan adawa

Gwamna Nyesom Wike da 'yan siyasar adawa a Najeriya

Asalin hoton, Othe

Bayanan hoto, Daga hagu zuwa dama: Gwamna tare da Rabi'u Kwankwaso na NNPP; Wike da Peter Obi na LP; Wike da gwamnonin Legas da Ekiti - Sanwo Olu da kayode Fayemi; Wike da Sanata Wamakko jagoran APC a Sokoto

Tun bayan ɓarkerwar riicin, an ga yadda jiga-jigai a jam'iyyun adawa suka dinga turuwa zuwa birnin Fatakwal don ganawa da Gwamna Wike da kuma ko janye shi daga PDP.

A ranar 24 ga watan Yuni ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP ya kai wa Wike irin wannan ziyara.

Ganawar Wike da Kwankwaso ta faru ne ƙasa da kwana ɗaya bayan ɗan takarar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya je wajensa.

Har wa yau, Wike ya gayyaci Gwamnan Legas Babajide Sanwo Olu, don ya taya shi ƙaddamarwa da kuma buɗe wasu ayyuka da gwamnatinsa ta gudanar a jihar, inda shugabannin suka dasa ɗambar gina gadar sama a birnin Fatakwal.

Ƙasa da kwana ɗaya bayan haka, sai ga tsohon gwamnan Sokoto kuma jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya je Rivers don ƙaddamar da ayyuka.

Sai dai Wike bai gayyaci wani gwamna ko jigo ba daga PDP kamar yadda aka saba.

Dalilan da suka hana Wike da Atiku sasantawa

Atiku da Okowa

Asalin hoton, PDP

Bayanan hoto, Rikicin Atiku da Wike ya sake ɗaukar sabon salo bayan da aka zaɓi Gwamna Okowa (hagu) a matsayin abokin takarar Atikun
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ƙarshen watan Mayun 2022 ne Atiku Abubakar ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja, inda ya samu ƙuri'a 371 daga cikin karɓaɓɓun ƙuri'u 764 da aka kaɗa.

Gwamna Wike ne ya zo na biyu da ƙuri'a 237, yayin da sauran 'yan takara bakwai suka raba sauran ƙuri'u - duk da cewa biyu ba su samu ƙuri'a ko ɗaya ba.

Jiji-da-kai

"Wannan rikici ya wuce siyasa, ya wuce adawa, ya wuce takara ma, ya zama jiji-da-kai," a cewar Dr Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa a Jami'a Abuja.

Gwamna Wike ya hidimta wa PDP tun bayan faɗuwarta a babban zaɓen 2015, saboda haka yake ganin ya kamata a yi masa alfarma shi ma, in ji masanin.

An ga yadda Wike ya tsaya tsayin daka a wancan lokacin wajen nema wa jam'iyyar shugabanci, inda har ya tsaya wa Uche Secondus ya zama shugabanta a lokacin. Sai dai dangantakarsu ba ta wanye lafiya ba a ƙarshe.

"Saboda irin wannan tunani nasa [Wike] ne ya sa suka ɓata da wanda ake ganin yaronsa ne, tsohon shugaban jam'iyya Uche Secondus. Shi [Secondus] ya so a ce jam'iyya ta fi ƙarfin mutum ɗaya amma Wike na ganin shi ne jam'iyyar."

Gwamna Tambuwal ya ƙara zafafa rikicin

Idan ba a manta ba, Atiku Abubakar ya yi nasarar lashe zaɓe ne bisa taimakon Gwmanan Sokoto Aminu Waziri Tamnbuwal bayan da ya janye masa yayin da ake daf da fara kaɗa ƙuri'a.

Rahotanni sun bayyana cewa Wike ya nemi Tambuwal ya janye masa amma ya ƙi amincewa, inda daga baya kuma ya janye wa Atiku, abin da ya sa Wike ya ji ɗaci kuma yake ganin Tambuwal a matsayin wanda ya butulce masa.

Hakan ba zai rasa nasaba da kuma taimako irin na siyasa ba da Wike ya bai wa Gwamna Tambuwal a zaɓen 2019, lokacin da yake neman gwamna karo na biyu.

"Kasancewar Tambuwal a ɓangaren Atiku ya ƙara zafafa rikicin saboda Wike na ganin Tambuwal a matsayin butulu," in ji Dr Kari.

Wasu na ganin gayyatar da Wike ya yi wa Wamakko na nuni da shirinsa na haɗa gwiwa da APC wajen yaƙar Aminu Tambuwal yayin da yake neman takarar sanata a zaɓen 2023.

'Labaran ƙarya'

A gefe guda kuma, ɗan Majalisar Wakilai Solomon Bob daga Jihar Rivers ya ce labaran ƙarya da magoya bayan Atiku ke yaɗawa kafin da kuma bayan zaɓen na fitar da gwani ne suka ta'azzara rikicin.

Daga cikin ƙarairayin, a cewarsa, har da maganar cewa Wike bai gamsu da sakamakon zaɓen ba, sannan ya musanta cewa mai gidan nasa ya so ya zama mataimakin Atiku.

"Rahotannin da ake yaɗawa cewa Wike ya yi fushi da jam'iyya saboda ba a zaɓe shi a matsayin abokin takarar Atiku ba ba gaskiya ba ne," a cewa Mista Bob yayin hirarsa da Channels TV a ranar Litinin.

"Gwamnan bai taɓa neman ya zama abokin takaerar Atiku ba. Bai taɓa tambaya ba kuma bai taɓa kamun ƙafa ba."

Ya ƙara da cewa ana yaɗa labaran boge ne "don a ƙasƙanta Wike kuma a ɗaukaka darajar ɗan takarar [Atiku]. Wanna ita ce gaskiyar da ba za su taɓa faɗa ba, da alama wani yunƙuri ne da gangan don a ɓata martabar Wike kuma a ƙasƙantar da shi."

'Akwai yiwuwar Wike ya yaƙi Atiku daga cikin gida'

Duk da irin abota da yake yi da 'yan jam'iyyar adawa a faɗin ƙasa, masana na ganin zai yi wuya Wike ya bar PDP amma kuma zai iya yaƙar Atiku daga cikin gida.

Dr. Kari na ganin "Wike babban ɗan siyasa ne mai tunanin, wanda ya san cewa ba shi da wata makoma sama da PDP".

A cewarsa: "Ba na tsammanin zai bar PDP, abin da ya fito fili shi ne ba lallai ya goyi bayan Atiku ba. Hamshaƙin ɗan siyasa ne kuma ya san ba shi da makoma a wajen PDP.

"Shure-shuren da yake yi shi ne ya nuna cewa har yanzu yana da kima da ƙarfi a jam'iyyar.

'Yanzu abin ma ya wuce su kansu 'yan takarar, saboda da ma wasu na neman dama ta samun muƙami da wasu abubuwa. Shi ya sa za ka ji wasu daga ɓangarorin biyu suna yaɗa abubuwa ko da ba gaskiya ba ne."