Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mukaminmu na tsaro je-ka-na-yi-ka ne -Gwamnonin Najeriya
Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya, kuma gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ya ce mukamin da ake jingina wa gwamnoni cewa su ne shugabannin tsaro a jihohinsu suna ne kawai.
A wata hira da ya yi da BBC gwamnan ya yi bayanin cewa gwamna a Najeriya ba shi da ikon ya bai wa jami'an tsaro umarni ba tare da amincewar shugabanninsu ba domin iko da jami'an tsaro hurumin gwamnatin tarayya ne.
'Gwamnatin tarayya ya kamata ta sake duba yadda ake gudanar da al'amuran tsaro. Misali, a matsayina na gwamna, idan na kira kwamishinan 'yan sanda ko na ba shi umarni, zai ce sai ya nemi Babban Sufeeton 'Yan sanda na Najeriya, shi kaɗai zai ji umarninsa. kowanne gwamna kuma haka ne, sai an bi wannan tsarin.' In ji shi
Ya ce akwai buƙatar ganin an sauya yanayin ikon tsaro a ƙasar saboda gwamnoni su sami damar ɗaukan muhimman matakai wurin tabbatar da tsaro a jihohinsu.
Ya ce : 'Wasu jihohin sun nemi cewa a bar su su kafa rundunar 'yan sanda na kansu domin gudar da tsaro ta yadda suke ganin ya fiye masu. yanzu kuma akwai buƙatar a sake duba wannan lamari saboda yanayin da muka shiga, saboda idan kiɗa ya sauya ya kamata rawa ma ta sauya'.
Gwamna Yahaya, ya ƙara da cewa harkar tsaro abu ne da ya shafi kowa kuma abin da ya shafi jiha ɗaya yana tasiri a duka jihohin yankin.
Ya jaddada buƙatar ganin kowa ya ba da gudummawa domin magance matsalar rashin tsaro a arewacin Najeriya.
'Kowa ce jiha tana zaman kanta ne kuma akwai ayyukan tsaro da suke gudanarwa, amma duk da haka aka ƙirƙiri wannan ƙungiya ta gwamnonin arewa kuma a haka muke tarayya don abu ne da ya shafe mu baki ɗaya, dole kuma mu ga cewa mun tunkari wannan lamari a matsayin al'umma ɗaya kuma ta wannan hanyar ce kawai za mu iya samun sauƙi'. in ji gwamnan.
Ya ce gwamnonin yankin sun jajanta wa al'ummar Tudun Biri da jirgi mara matuki na sojoji ya kai masu hari bisa kuskure da kuma al'ummomi a jihar Filato da 'yan bindiga suka kai wa hari cikin kwanakin nan inda ya ce sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa wani abu makamancin haka bai sake aukuwa ba.
Ya ce: 'Mun yi baƙin ciki bisa abin da ya faru a Filato, kuma mun buƙaci al'umma da a kai zuciya nesa, mu yi ƙokarin samun zaman lafiya kamar yadda ake samu a sauran ɓangarorin Najeriya'.