Abin da 'yan Najeriya ke cewa kan wa'adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗi

Asalin hoton, CBN
Kwanaki kalilan ne dai suka rage a daina amfani da tsoffin takardun kuɗi a Najeriya kamar yadda Babban Bankin kasar ya sanar.
Babban bankin Najeriyar ya ce ba gudu ba ja da baya game da wa'adin da ya sanya na daina amfani da tsoffin takardun kuɗin ƙasar daga ranar 31 ga watan Janairu.
Sai dai, bangarori da dama a cikin ƙasar na kira ga Babban Bankin da ya tsawaita wa'adin.
Ƴan Najeriya da dama na ƙorafi game da ƙarancin sabbin takardun kuɗin, inda suka ce har yanzu bankunan ƙasar na bai wa kwastomominsu tsoffin takardun kuɗi.
A ranar Laraba 26 ga watan Oktoba ne Babban Bankin Najeriyar ya sanar da matakin sauya fasalin kudin kasar na naira 200 da 500 da kuma 1000, inda ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.
Lokacin kaddamar da sabbin kuɗin, shugaba Buhari ya ce sauya fasalin kuɗaɗen zai yi tasiri ƙwarai wajen taimaka wa ƙasar ta magance matsalar yaɗuwar kuɗi ba bisa ƙai’da ba da cin hanci.
Shugaban ya ce sabbin kudaden za su inganta tatalin arzikin Najeriya da ƙara wa kuɗin ƙasar daraja.
Mutane da dama na ta bayyana ra'ayoyinsu a kafafen sada zumunta. Ga wasu da muka tsakuro muku daga shafukanmu.

Yellow Man ya ce: An bar karɓar tsoffin takardun kuɗi a yankinsu sannan masu shaguna ma sun rufe.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Nasiru Abubakar Dagawa ya ce: Allah ya kawo mana sauki.

Jamila Abubakar ta ce: Masu shago da waɗanda ke yin sana'o'i basa karɓar tsoffin takardun kuɗi, Allah ya kawo mana sauki.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Zulkiflu Salisu Dankaka Jargaba ya ce: Mu dai fatan mu duk waɗanda suke da tsoffin kuɗi za su kai su banki don kaucewa asara.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Bala Garba ya ce: Harkoki na neman tsayawa a yankunan karkara saboda ƙarancin sabbin takardun kuɗi, akwai buƙatar duba inda matsalar take.