Ana kwashe 'yan Isra'ila a ƙauyukan iyaka da Lebanon saboda barazanar hari

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Anna Foster da David Gritten
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC da ke arewacin Isra'ila da kuma na London
Rundunar sojin Isra'ila na kwashe 'yan ƙasar daga ƙauyuka 28 da ke kusa da iyakarta da Lebanon ta arewaci saboda rikicinta da ƙungiyar Hezbollah.
An kashe farar hula da soja ɗaya 'yan Isra'ila a ranar Lahadi, lokacin da aka harba makamin fasa tankar yaƙi kuma ya faɗa kan wani gari da kuma tashar sojoji.
Rundunar sojin ta ce ta kai wa sansanonin Hezbollah hare-haren ramuwa.
Ta kuma zargi Iran, wadda ke taimaka wa Hezbollah, da ba da umarnin kai mata harin don a karkatar da hankalinta daga yaƙin da take yi a Zirin Gaza.
Ita kuma Iran ta gargaɗi Isra'ila game da haɗarin yaɗuwar rikicin idan ta ci gaba da kai hare-hare a kan Falasɗinawa saboda rama abin da Hamas ta yi mata na kashe 'yan ƙasar a farkon watan nan.
Hezbollah ce babbar rundunar soja a Lebanon wadda ke da manyan makamai masu linzami da ke cin dogon zangon da za su iya kaiwa tsakiyar Isra'ila.
Ta fafata yaƙin wata guda da Isra'ilar a 2006.
Rundunar sojin Isra'ila (IDF) ta sanar ranar Litinin cewa tana shirin kwashe dukkan fararen hula da ke zaune a tsawon kilomita biyu kusa da iyakar Lebanon, inda za ta kai su wuraren da gwamnati ta tanada.
Sai dai da ma tuni mutane suka ƙaurace wa ƙauyukan, inda ɗaya cikin uku na garuruwan suke fayau.
Mazauna yankunan sun faɗa wa BBC cewa ba su jira umarnin gwamnati ba kafin su tsere zuwa kudancin ƙasar don tsira da rayuwarsu.
Mutanen da suka rage yanzu a ƙauyukan su ne sojoji da kuma 'yan sa-kai da suka tsaya don taimaka musu.
Ƙauyukan na da kusanci da iyakar sosai ta yadda ana iya hango katangar da Isra'ila ta gina a tsakani. Kazalika, ana iya hango tashar sojojin Hezbollah a ɗaya tsallaken.
Ƙarin labarai kan rikicin Isra'ila da Gaza:

Wani lokaci a ranar Lahadi, an yi ƙazamar fafatawa a kan iyakar tsakanin Hezbollah da dakarun Isra'ila.
Isra'ila ta ba da rahoton mutum na farko farar hula da aka kashe mata a wanna rikici. Wani mutum ne mai shekara 40 da 'yan kai da aka kashe bayan makamin harbe tanka ya dirar masa garin Shtla da ke kan iyaka.
Daga baya kuma, aka kashe sojan Isra'ila Laftanar Amitai Granot a wani harin na makami mai linzami a wata tashar soja, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta ruwaito.
A wata musayar wutar ta daban, wani makamin roka ya faɗa kan hedikwatar dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a Lebanon, Unifil, a garin Naqoura. Ba a jikkata kowa ba.
IDF ta ce ta kai hare-hare ranar Lahadi da kuma tsakar dare a kan sansanonin Hezbollah.
An kuma samu rahotannin da ke cewa na harba makaman roka tara daga Lebanon zuwa Isra'ila, an tare biyar daga ciki kuma ta mayar da martani kan wuraren da aka harba su.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ranar Litinin da ta gabata, an kashe sojin Isra'ila uku yayin da mayaƙan ƙungiyar Islamic Jihad suka tsallaka iyaka daga Lebanon. A ranar dai, Isra'ila ta kashe mayaƙan Hezbollah uku bayan harin ramuwa da ta kai na makamin da aka harba mata.
A ranar Juma'a kuma, an kashe mai ɗaukar bidiyo na kamfanin labarai na Reuters Issam Abdallah yayin da yake ba da rahoto a kusa da ƙauyen Alma al-Shaab na Lebanon. IDF ta ce tana bincike kan cewa dakarunta ne suka harba makamin.
Ministan tsaro na Isra'ila Yoav Gallant ya ce ba su da "niyyar fara yaƙi a arewacin ƙasar".
"Idan Hezbollah ta zaɓi yaƙi, za ta fuskanci horo mai tsanani. Mai tsananin gaske. Amma idan ta haƙurƙurtar da kanta, za mu yi hakan mu ma," in ji shi.
Shi kuma Ministan Harkokin Wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ya ce ƙasarsa ta aika wa Isra'ilar saƙo ta hannun ƙawayenta cewa "idan ba ta daina kai wa Falasɗinawa hare-hare ba, Iran ba za ta zira ido tana kallo ba".
Ya kuma yi gargaɗi cewa "idan yaƙin ya faɗaɗa" Amurka za ta yi "asara mai yawa".
Amurka ta ce za ta tura wani babban jirgin ruwan yaƙi mai kai hari a gabashin Tekun Baharrum ranar Lahadi "don daƙile kai wa Isra'ila hari ko kuma yunƙurin faɗaɗa rikicin" bayan harin da Hamas ta kai.











