City za ta tsuga kudin sayen Haaland, Barca ba za ta iya daukar Messi ba

Manchester City za ta bai wa Erling Haaland sabuwar kwantiragin da za ta tsuga kudi ga duk mai son sayen dan wasan, wanda a baya ta gindaya £150m. . (Athletic - subscription required)

Kungiyar ta Etihad na fatan korar dun wata kungiyar da ke kwadayin sayen Haaland mai shekara 22, wanda ya ci mata kwallo 12 a Champions League a bana.

Chelsea ta janye daga shirin neman tsohon kociyan Sifaniya, Luis Enrique, yanzu za ta mayar da hankali wajen daukar tsohon wanda ya horar da Paris St-Germain, Mauricio Pochettino. (Telegraph - subscription required)

Da yake Chelsea za ta hakura da daukar Enrique hakan zai bai wa Tottenham damar daukar dan kasar Sifaniya, mai shekara 52, a matakin wanda zai maye gurbin Antonio Conte a kungiyar da ke Arewacin Landan. (Express)

Manchester United na son daukar dan kwallon Bayer Leverkusen mai tsaron baya daga gefen hagu, Jeremie Frimpong, yayin da United ke fatan sayar da Aaron Wan-Bissaka da kuma Diogo Dalot. (Mail)

Barcelona ba za ta iya daukar Lionel Messi ba, mai shekara 35 daga Paris St-Germain a wannan matakin da take matse bakin aljihu in ji shugaban La Liga Javier Tebas. (Goal)

West Ham ta hangi kociyan Lille, Paulo Fonseca a matakin wanda zai maye gurbin David Moyes, wanda ake cewar zai iya barin kungiyar a karshen kakar nan. (Guardian)

Watakila Arsenal ta sayar da Folarin Balogun - wanda ke wasannin aro a Reims a kakar nan - zuwa RB Leipzig, domin ta hada £100m, wanda zai ba ta damar sayen dan kwallon West Ham, Declan Rice, 24. (Metro)

Dan wasan Real Madrid, Karim Benzema, ya saka hannu kan tsawaita zamansa a Santiago Bernabeu kaka daya zuwa karshen kakar 2024. (Mirror)

Dan wasan AC Milan, Rafael Leao, ya tabbatar yana son ci gaba da taka leda a San Siro duk da batun cewar Manchester City. na son zawarcinsa (Manchester Evening News)

Liverpool na shirin daukar Adrien Rabiot, wanda yarjejeniyarsa da Juventus za ta karkare a karshen kakar nan. (Liverpool Echo)

Liverpool na fatan daukar dan kwallon Bayern Munich, Ryan Gravenberch, mai shekara 20, domin ta rage yawan dattawan da ke buga mata gurbin tsakiya. (FourFourTwo)

West Ham za ta rabu da 'yan wasa da yawa a karshen kakar nan da suka hada da Manuel Lanzini da Angelo Ogbonna da Vladimir Coufal da Aaron Cresswell da Pablo Fornals da Tomas Soucek har da kyaftin Rice. (Football Insider)

Watakila Toni Kroos ya saka hannu kan karin kwantiragin kaka daya a Real Madrid, koda yake ana cewar zai yi ritaya a karshen kakar nan. (Mail)

Tottenham na shirin daukar matashin dan wasan Chelsea mai shekara 20, Levi Colwill, wanda ke wasannin aro a Brighton, wanda ya nuna kwarewarsa a bana. (Sun)

Kyaftin din Manchester City, Ilkay Gundogan, wanda ake alakanta shi da Barcelona, mai shekara 32 ya ce zai auna ya gani ko zai iya kaka daya a kungiyar da ke buga Premier League nan gaba. (Times - subscription required)

Watakila Chelsea ta rabu da golanta, Edouard Mendy da Kepa Arrizabalaga, domin ta dauki mai tsaron ragar Borussia Dortmund, Gregor Kobel, 25. (Bild - in German)