Man Utd na son aron Felix, Chelsea ta yi wa Arsenal kancal kan Mudryk

A shirye Manchester United take ta biya Yuro miliyan 4 (Fam miliyan 3.5) domin karbar aron dan wasan gaba na Atletico Madrid Joao Felix zuwa karshen kakar nan, sai dai kuma kungiyar ta Sifaniya ta ce Yuro miliyan 12 zuwa 13 za ta karba a kan dan Portugal din.

Benfica ta ki yarda da tayin farko da Chelsea ta yi a kan dan wasanta na tsakiya na Argentina Enzo Fernandez. Blues din tana son biyan Fam miliyan 112 kashi-kashi a cikin shekara uku, amma kungiyar ta Portugal ta ce ba ta yarda ba, sai dai ta biya Fam miliyan 106 lakadan, kamar yadda yake a cikin yarjejeniyar kwantiragin sayen dan wasan mai shekara 21.

A ranar Alhamis din nan Shakhtar Donetsk za ta yi watsi da tayin da Arsenal ta sake yi a kan matashin dan wasanta na Ukraine Mykhailo Mudryk, Fam miliyan 62, yayin da Chelsea ke tattaunawa kan sayensa ita ma. (Mail)

Chelsea dai a shirye take ta biya sama da duk wani farashi da Arsenal za ta yi wa Mudryk don ganin ita ta dauke shi.

Real Madrid na kara samun kwarin guiwar nasarar sayen dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Jude Bellingham, na Ingila, inda take nuna wa matashin mai shekara 19 cewa kungiyar ce ta fi dacewa da matasan ‘yan wasa na Turai.

Ana sa ran Barcelona za ta dauki dan bayan Sifaniya Inigo Martinez, idan kwantiraginsa da Athletic Bilbao ya kare a bazara. 

Kociyan Everton Frank Lampard ne zai jagoranci kungiyar a wasan cin Kofin FA zagaye na uku da za ta yi da Manchester United a ranar Juma'a, yayin da ake nuna tababa kan ci gaba da zamansa a kungiyar ta Goodison Park zuwa wani tsawon lokaci. 

Aston Villa ta yi watsi da bukatar Everton ta karbar aron dan wasanta na gaba Danny Ings na Ingila. Kungiyar tana son sai dai ta sayar da shi gaba daya, kuma daman wasu kungiyoyin ma da suka hada da Bournemouth da Southampton da West Ham na sha'awarsa.

Everton din kuma a shirye take ta sayar da dan wasanta na tsakiya Abdoulaye Doucoure, na Mali a watan Janairu kuma tuni daman sun tattauna da Fulham.

Wolves ba ta da wata masaniya cewa Liverpool na sha'awar dan wasanta na tsakiya Matheus Nunes, kuma kungiyar ta Molineux ta ce dan Portugal din mai shekara 24 na cikin tsarinta na tsawon lokaci. (90 Min)

Kungiyoyi daga Saudi Arabia na nuna sha'awarsu a kan dan wasan gaba na Liverpool Roberto Firmino, amma kuma dan Brazil din ya fi sha'awar tsawaita zamansa Anfield inda tuni suka fara tattaunawa da shi a kan haka.

Leicester City ta yi tattaunawar farko-farko a kan sayen dan bayan Denmark Victor Kristiansen na FC Copenhagen, wadda za ta iya karbar tayin farko na kusan Fam miliyan 5 zuwa 8 a kan matashin mai shekara 20.

Southampton na tattaunawa da wakilan dan wasn tsakiya na Villarreal Nicolas Jackson a kan karbar aron matashin dan tawagar Senegal din, amma kuma da zabin sayensa gaba daya a lokacin bazara.