Qatar 2022: Ghana ta kasa kaiwa zagaye na gaba a Kofin Duniya

An kori tawagar ƙwallon ƙafa ta Ghana daga Gasar Kofin Duniya bayan Uruguay ta doke ta 0-2 a wasan ƙarshe na Rukunin H.

Ɗan wasan Ghana kuma kaftin ɗin tawagar ya kasa cin bugun finaretin da aka ba su bayan mai tsaron raga Rochet ya bigi ƙafar Kudus. Shi ne dai kuma ya kaɗe ƙwallon da Ayew ya buga masa a minti na 21.

Sai dai ita ma Uruguay ta fita daga gasar duk da nasarar da ta samu saboda ƙwallo biyu kawai ta zira a raga idan aka kwatanta da na Koriya ta Kudu huɗu.

Portugal da Koriya ne suka tsallaka zagayen 'yan 16 daga rukunin.

Ghana ta ƙare wasan a ƙasan teburi da maki uku, yayin da Portugal ta kasance ta ɗaya da maki shida, sai Koriya mai maki huɗu bayan ta doke Portugal ɗin da 2-1.