Ƙasar da zama da dabbobi ƴan lele ka iya kai ka kurkuku

Wata mata na sumbatar karenta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sabuwar dokar na iya sa masu kiwon dabbobi ƴan lele a uku

“Yana kallo na da idanunsa masu kyau. Alamunsa na nuna yana so in kai shi waje ya wala, amma ba zan kuskura in gwada ba. Hukumomi za su kama mu.”

Masha ‘yar kasar Iran ta mallaki kare a babban birnin kasar Tehran, kuma tana bayani ne akan yadda aka fara tsare iyayen gidan dabbobi ‘yan lele da ƙwace dabbobin nasu a birnin.

Jami’an tsaro a Tehra sun riga sun bayyana cewa kai karnuka filayen hutawa da shaƙatawa na birnin ”karya doka” ne.

Masu goyon bayan dokar sun ce ta dace saboda ”tsaron lafiyar al'umma”.

A daidai lokacin kuma bayan share watanni ana muhawara, majalisar dokokin Iran za ta iya amince wa da wata sabuwar doka mai taken ‘yancin al'umma a kan dabbobi, wanda zai karkare mallakar dabbobi ‘yan lele a duk fadin kasar.

Tara

Kamar yadda sababbin sharrudan dokar suka tanada, sai wanda yake da takardar dama da wani kwamiti na musamman ne zai iya aje dabobi ‘yan lele.

Dokar ta kuma saka tara mafi ƙaranci dala 800 ga duk wanda ya shigo da, ko ya saya, ko ya sayar, ko ya yi safarar dabbobi ƴan lele kamar mage ko kunkuru ko zomo.

“An fara gudanar da muhawara akan wannan doka sama da shekara 10 da suka gabata, a lokacin da wasu ‘yan majalisar dokokin Iran suka yi kokarin tallata wata doka da ta yi tanadin ƙwace duka karnuka da bai wa gidajen ajiye dabbobin dawa ko kuma a bar su a cikin hamada”, a cewar Dr Payam Mohabi, shugaban kungiyar likitocin dabbobi, kuma mai adawa da wannan doka a lokacin da ya zanta da BBC.

“A shekarun da suka gabata, sun sauya wannan doka da dama, kuma sun tattauna gudanar da hukuncin gallazawa ga duk wadanda suka mallaki karnuka. Sai dai shirinsu bai yi nisa ba” a cewar Dr Mohebi.

Dr Mohebi asibitinsa a Tehran

Asalin hoton, Courtesy of Dr Payam Mohebi

Bayanan hoto, Dr Payam Mohebi, president of the Iran Veterinary Association, is openly against the new bill

Alama ta rayuwar birni a Iran

An jima da yi wa mutanen karkara a Iran shaidar masu ajiye karnuka, amma kuma wannan dabba ta zama alamar rayuwar birni a wannan ƙarni na 20.

Iran na daya daga cikin kasashen da ke yankin gabas ta tsakiya ta farko da ta yi tanadin dokokin kula da jin dadin dabbobi a shekara ta 1948.

Kuma gwmanatin kasar ta kafa hukumar farko na inganta ‘yancin dabbobi. Iyalin Sarkin Iran su ma su mallaki nasu karnukan.

Amma juyin juya halin shekara ta 1979 ya sauya abubuwa da dama na rayuwar Iraniyawa da karnuka.

A picture of Iran's royal family with a dog

Asalin hoton, Iranian Royal Family Collection

Bayanan hoto, Dogs became a symbol of urban life in Iran during the 20th Century and even the country's royal family kept them

Al'adun addinin Musulunci sun bayyana kare a matsayin dabba mara tsarki.

A idanun sabuwar gwamnati, ana yi wa kare kallon alamar al'adun yammacin duniya, da hukumomi ke kokarin dakilewa.

“Babu wasu tanade-tanade masu ƙwari dangane da mallakar karnuka” a cewar wani likitan dabbobi a babban birnin Tehran mai suna Dr Ashkan Shemirani a lokacin da ya zanta da BBC.

“Jami’an tsaro na kama mutane saboda suna yawo da karnukan su, ko ma saka su a cikin mota saboda suna wa haka fassara a matsayin alamu na al adun turawan yammacin duniya.”

Kurkukun karnuka

“Har kurkukun dabbobi suka kirkiro, kuma mun ji labarai masu tayar da hankula a kan abubuwan da ke faruwa a wajen“ a cewarsa.

An Iranian family with a dog dressed as Superman

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

“Ana ajiye dabobin ne a budadden waje na kwanaki masu yawa ba tare da isashen abinci da ruwa ba, yayin da mammallakan dabbobin ke fuskantar kalubale a kotu.“

Matsalar tattalin arziki da Iran ke fama da shi saboda takunkuman kasashen yammacin duniya ya taka rawa wajen samar da wannan doka.

Hukumomi sun haramta shigar da abinci dabbobi ƴan lele tsawon shekaru uku a yunkurin tattalin asusun kudaden waje da kasar ke tanada.

Saboda haka a wannan yanayi da kusan duka abincin dabbobi ‘yan lele daga kasashen ketare suke, farashin abincin ya yi tashin gworon zabo musamman bayan kafa kasuwar boye da wasu suka yi.

“Mun dogara da mutanen dake satar shigo da abincin a sirrance,” a cewar wani mammallakin asibitin dabbobi dake birnin Mashhad bayan zantawa da BBC.

“Yanzu farashin ya yi biyar din yadda yake a watannin baya.“

Dan kasuwar ya zargi kayan abincin dabbobi na cikin gida a matsayin wadanda ingancin su bai kai yadda ya dace ba.

“Ingancin ba shi da kyau. Kamfanoni na amfani da nama ko kifi mai rahusa, ko ma kayan masarufin da lokacin amfanin su ya wuce.“

Matsalolin Mage

Sai dai wannan sabuwar doka da ake tanadi ba karnuka kawai ta shafa ba. Har da maguna da kada a cikin jerin sunayen dabbobin.

Iran ta yi suna a matsayin tushen nau’in maguna da aka fi sani da Persian cats, kuma suna daga cikin nau‘in maguna mafi shahara a duk fadin duniya.

A Persian cat in a Tehran cafe
Bayanan hoto, Har da mage dokar ta shafa

“Shin za a yarda cewa yanzu haka magen Persia bata tsira a kasar haihuwar ta ba?", wani likitan dabbobi a birnin Tehra ya ce a lokacin da yake hira da BBC.

“Babu alamar hankali a wannan dokar. Masu karfin ra’ayi ne suke son nuna wa jama’a irin ikonsu” a cewar sa.

Dr. Mohebi, wanda shi ne shugaban likitocin dabbobi na Iran ya kira wannan tanadin doka a matsayin ”abun kunya”.

”Idan majalisar dokoki ta amince da wannan doka, to ƴaƴanmu da jikokin za su tuna mu a matsayin mutanen da muka haramta karnuka da maguna saboda kawai karnuka da maguna ne.”

Mutanen da suka mallaki dabbobi ‘yan lele kamar wata mata mai suna Masha na cikin matukar damuwa akan yanayin dabobinsu nan gaba.

”Ba zan kuskura in nemi izinin wa ‘ɗana’ ba,” ta ce.

”Idan ba su ba ni izini ba fa? Ba zan iya barin shi a waje ba.”