An zaftare wa Everton maki 10 a Premier League

Asalin hoton, BBC Sport
An zaftare wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton maki 10 nan take bayan da aka same ta da laifin keta dokokin samun riba da kuma ɗorewar kasuwanci na gasar Premier.
Hukuncin shi ne mafi girma na wasanni a tarihin gasar kuma ya bar Everton a matsayi na 19 a kan teburi inda ta rage da maki huɗu kacal.
Kulob ɗin ya ce ya yi bakin ciki da takaicin hukuncin da aka yanke inda ya ce ba a yi masa adalci ba
Everton ta ce tana da niyyar ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Mahukuntan gasar ta Premier sun miƙa Everton ga wata hukuma mai zaman kanta a watan Maris amma ba ta bayyana takamaiman laifin da ake zargin ƙungiyar da shi ba.
Everton ta yi asarar kuɗi a shekara ta biyar a jere a cikin watan Maris bayan ta ba da rahoton giɓin yuro miliyan 44.7m a 2021-22.
Ana iya barin ƙungiyoyin Premier su yi asarar da ba ta wuce fam miliyan 105 cikin shekaru uku kuma Everton ta yarda cewa ta keta ka'idojin riba da ɗorewar kasuwanci (PSR) na zangon lokacin da ya ƙare a 2021-22.







