Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jawabin Tinubu da ya sauya tarihin Najeriya
Tun bayan da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya faɗi cewa "zamanin tallafi ya wuce" a jawabinsa na kama aiki a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Najeriya suka tsinci kansu a wani sabon babin rayuwa da wataƙila ba su taɓa tsammani ba.
"Mun yaba wa shawarar gwamnatin da ta gabace mu na cire tallafin man fetir wanda yake amfanar masu arziƙi fiye da talakawa. Ba za a iya ci gaba da biyan kuɗi tsubububa a matsayin tallafi a daidai lokacin da lalitar gwamnati ke ci gaba da tsiyayewa. Za mu karkatar da kuɗaɗen zuwa wasu hanyoyin mafiya amfani kamar gine-ginen gwamnati da Ilimi da fannin lafiya da kuma samar da ayyukan yi domin inganta rayuwar miliyoyin ƴan ƙasar." In ji Shugaba Bola Tinubu, a jawabin nasa na kama aiki ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Bisa jawabin na Tinubu, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ce ta cire tallafin inda shi kuma ya yi sanarwa.
Jim kaɗan bayan jawabin nasa sai aka fara samun dogayen layukan mai a manyan biranen ƙasar kamar Legas da Abuja da Kano.
Kuma kwana biyu bayan nan wato ranar 31 ga watan Mayu sai kamfanin man na ƙasar, NNPCL ya fitar da sabon farashin mai daga ƙasa da naira 200 zuwa naira 539, kafin daga bisani a ranar 18 ga watan Yuli kamfanin ya sake fitar da sabon farashi na naira 617 wanda shi ne har kawo yanzu.
Tasirin janye tallafin ga rayuwar 'yan Najeriya
Masana tattalin arziki a Najeriya irin su Farfesa Mustapha Mukhtar, malami a sashen koyar da nazarin tattalin arziki a jami'ar Bayero da ke Kano, sun ce babu shakka cire tallafin mai ya yi matuƙar tasiri ga tattalin arziƙin ƙasar mai yawan jama'a fiye da miliyan 200.
"Janye tallafin man fetur da dangoginsa ya haifar da hauhawar farashin fannin zurga-zurga wanda kuma ya shafi farashin kayan masarufi. A ɓangaren gwamnati kuma ya samar mata da kuɗaɗen aiwatar da wasu ayyukan daban wanda shi ne babban burin." In ji Farfesa Mustapha.
Ya ƙara da cewa sakamakon hauhawar farashin sufuri da kayan masarufi " ya jefa 'yan Najeriya cikin matsananciyar damuwa da samun tawayar walwalar da suka sa ba yi ta yau da kullum."
A fagen siyasa ma masanan sun ce cire tallafin man ya shafi ƙimar jam'iyya mai mulki kasancewa ba ya cikin jerin abubuwan da jam'iyyar ta alƙawarta wa 'yan ƙasa a lokacin neman ƙuri'unsu.
"Lallai wannan ya samar da illa a siyasance musamman ma bisa la'akari da cewa wani ɓangare na jawabin da shugaba Tinubun ya yi ba ya cikin rubutaccen jawabin da ya kamata ya karanta a ranar kama aikin." In ji Dakta Kole Shettima, masanin kimiyyar siyasa kuma shugaban gidauniyar McArthur Foundation a Najeriya.
Ko rayuwar 'yan Najeriya za ta sake komawa kamar da?
A yanzu haka tun bayan cire tallafin man da kuma na baya-bayan nan na wutar lantarki, abubuwa suka ƙara tsananta ga 'yan Najeriya - musamman kayan masarufi.
Sakamakon tsadar kayan abinci yanzu 'yan ƙasar da dama ba sa iya samun abinci sau uku a kullum kamar yadda a baya suke samu.
"Ni gwara na mutu da na zauna cikin wannan yanayin na rayuwa. Ba ma iya samun abinci sau uku ni da ƴaƴana guda bakwai. Idan muka ci sau ɗaya ko biyu mun gode Allah. Shinkafa ce muke ci da ake kira Afafata wadda sai mun yi fiye da awa biyu muna tsintar ta...." In ji wata mata da BBC ta tattauna da ita a kwanakin baya.
Wani abu da a baya-bayan nan tsadarsa ke tayar da hankalin 'yan Najeriya shi ne kayan miya inda yanzu haka ƙaramin kwandon tumatir ake sayar da shi naira dubu 13 shi kuma tattasai ake sayar da shi naira dubu takwas.
'Yan kasuwa dai na kokawa da alaƙanta yanayin da tsadar kuɗin sufuri.
To sai dai Farfesa Mustapha ya ce akwai yiwuwar al'amura ka iya komawa kamar a baya kafin cire tallafin da shugaba Tinubu ya yi watanni 12 da suka gabata.
"Idan dai har ƙudirin cire wannan tallafin man fetur aka aiwatar da su kamar yadda ya kamata sannan aka gyara matatu suka koma suna aikin tace ɗanyen mai a kuma sayar da shi ga farashi mai rahusa ga 'yan ƙasa." In ji Farfesa Mustapha.