Yaya ake auna talauci?

Asalin hoton, Getty Images
Fiye da mutum biliyan ɗaya ne a faɗin duniya ke cikin talauci, kamar yadda wani rahoto da ya kalli fuskoki daban-daban na talauci ya nuna a ranar yaƙi da talauci da duniya.
"Mutane da dama na cike da fargabar cewa da wanne za su ji a wannan hunturu da ke tafe, shin da abinci za su ji? Ko yadda za su ɗumama jikinsu?'' in ji Pascal Kutzner mai magana da yawun ƙungiyar Tafel a Jamus, ƙasar da rahoton bai shafe ta ba.
Hatta cibiyoyin ajiye abinci a ɗaya daga cikin ƙasashe masu arziƙi na duniya, kamar Jamus, sun rufe ƙofa ga sabbin kwastomomi, yayin da suke ƙoƙarin tara kuɗin da suke buƙata. ''Farashin makamashi da na abinci na ci gaba da ƙaruwa, Abin da ya sa muke samun ƙarin mutanen da lamarin ya shafa waɗanda ke zuwa wajenmu neman taimako'' in ji mista Kutzner.
Me ake nufi da talauci?

Asalin hoton, Getty Images
A bana, rahoton na MPI ya nuna matsayin talauci ta hanyar duba fuskoki daban-daban a cikin ƙasashe masu tasowa 111. Rahoton ya samu mutum biliyan 1.2 a faɗin duniya wato kashi 19.1 cikin 100 na fama da wasu nau'o'in talauci, kuma rabinsu ƙananan yara ne 'yan ƙasa da shekara 18.
Duk da haka, rahoton ya ba da labari mai daɗi - da ke cewa 'yan Indiya miliyan 415 sun fita daga ƙangin talauci, to amma rahoton ya yi la'akari da binciken da aka yi daga shekarar 2005 zuwa 2021, kuma bai yi duba kan illolin da annobar korona ta haifar ba. Cikin gomman shekaru da suka wuce, duniya ta cika da fatan cewa za a iya kawar da talauci a 2030, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya buri, to amma a 2022, Bankin Duniya ya yi gargaɗin cewa wannan buri ba zai cika ba, saboda annobar Korona da kuma batun yaƙin Ukraine. A shekarar 2020, Bankin Duniya ya ce mutum miliyan 70 a faɗin duniya na rayuwa cikin matsanancin talauci, alƙaluman da suka zarce na 2019. A taƙaice a iya cewa kashi 9.3 cikin 100 na al'ummar duniya na rayuwa a dala 2.15 kimanin naira 1,500 duk rana a shekarar 2020.
Lissafin rayuwa da dala 2.15 a rana, ɗaya ne daga cikin hanyoyin fassara talauci, kuma ana kiransa da matsanancin talauci a faɗin duniya. Don haka, mutanen da ke hawa dogayen layukan karɓar abinci a cibiyoyin raba abinci na Jamus ka iya samun fiye da dala 2.15 kullum, duk haka dai ana iya kiran su da talakawa
Da me ake gane talauci?

Asalin hoton, Getty Images
''Talauci shi ne rashin samun abin biyan buƙatar rayuwar yau da kullum, wannan kuma ya danganta daga al'umma zuwa al'umma, da tattalin arziƙin kowacce al'umma'' kamar yadda Roberto Lacono, wani farfesa a jami'ar kimiyya da fasaha ta ƙasar Norway ya shaida wa BBC.
A mafi yawan ƙasashe masu tasowa ana auna talauci ne da irin kuɗaɗen da suke samu kowacce rana.
Alal misali, duk matar da kuɗin da take samu a rana ya gaza kashi 60 cikin 100 na matsakaicin samu a ƙasar, to tana cikin kasadar faɗawa ƙangin talauci.
Idan kuma abin da take samu ya yi kasa da kashi 50, to ana kallon ta a matsayin wadda ke fama da matsanancin talauci.
"Muna auna talauci ta hanyar kuɗin da ake samu," in ji Oriana Bandiera wani masanin tattalin arziki a makarantar tattalin arzikin ta birnin London.
To amma kuɗin shiga abu ne da ke wahalar auna wa a faɗin duniya. Wannan ne dalilin da ya sa ƙungiyoyin duniya, kamar Majalisar Ɗinkin Duniya, da Bankin Duniya ke zuwa da mabambantan alƙaluma.
Matsayin talauci a ƙasashen duniya

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A wasu ƙasashe matalauta kuɗin shiga, ba a auna kuɗin da ake samu saboda mutane ko dai ba su da aiki na dindindin, suna gudanar da sana'o'i, ko kuma sukan yi noma domin samun abin da za su ci, don haka ba za a iya auna kuɗin da suke samu ba'' kamar yadda Bandiera ta shaida wa BBC.
A ƙasashe masu tasowa, saboda mutane ba sa ajiye kuɗi da yawa, abinci shi ne babban abin da ke laƙume kuɗaɗen da suke ɓatarwa. "Bankin Duniya na la'akari da abinci da suturar da mutum ya saya a ciki mako ɗaya tare da haɗa su waje ɗaya a matsayin abin da mutum ke kashewa'' in ji Bandiera.
To amma a ƙasashe masu arziƙi ba su da wannan matsala, don haka Bankin Duniya ya zo da wani 'mizani' da zai taimaka wajen auna talauci a duk ƙasashen duniya. "Sun samu wasu ƙasashen sahun farko waɗanda ke fama da matsanancin talauci, da waɗanda ke fama da talauci, da kuma waɗanda ba su da alamar talauci. Sun yi duba ne da mafi ƙarancin kuɗin da mutum ke bukata a rana'', in ji Bandiera .
Wannan mizani da Majalisar Ɗinkin Duniya da Bankin Duniya suka samar a 1990 za a iya amfani da shi domin auna matsayin talaucin a kowacce ƙasa.
Mallakar gida, da biyan kuɗin makaranta, da kula da lafiya na cikin ma'aunin?

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Lacoco ya ce ba kawai iya kuɗin shiga ba ne ake amfani da shi wajen auna matsayin talauci. "Kuɗin da kake samu a rana ba zai iya bayyana haƙiƙanin talaucinka ba," in ji shi. Samun ƙarin kuɗin shiga wani lokaci ba shi ne ke nufin ka samu ci gaba a kasuwa, ko sana'a ba. ''A yanzu akwai ɓangarori da dama da ake auna talauci da su a duniya, waɗanda cikin sauƙi ke taimakawa wajen gano mutanen da ke cikin tsananin buƙata'', in ji Lacono.
Rahoton MPI na auna ɓangarorin talauci da dama cikin faɗin ƙasashe masu tasowa fiye da 100, tun shekarar 2010. "Muna auna talauci kai-tsaye," kamar yadda Alkire ta faɗa wa BBC. Kowanne gida da mutumin da ke cikinsa na da irin nau'in talaucin da ke damun sa, ta ɓangarori daban-daban kamar kula da lafiya, da ilimi, da kuma matsayin rayuwa.
Akwai makin da ake bai wa kowa, wanda ke duba fannonin rayuwa kamar samun abinci mai gina jiki, samun wutar lantarki, da man girki, shin yaranka na zuwa makaranta, da sauran batutuwa. "Muna kallon mizaninmu a matsayin takwara ga mizanin da aka saba auna ƙangin talauci wanda ke duba kuɗin shiga, da kuɗin da ake kashewa'', in ji Alkire. Ta ƙara da cewa binciken MPI ya haɗa da hanyoyin da aka saba auna talaucin da su.
Me ya sa auna ƙarfin talauci ke da muhimmanci?

Asalin hoton, Getty Images
Alkire ta ce an yi amfani da rahoton MPI a wannan shekarar domin auna talauci, kuma zai taimaka matuƙa wajen yaƙi da talauci a duniya. Alkire ta ce ''misali mutum miliyan 437 na fama da talauci a ɓangaren ruwan sha da tsaftar muhalli, sannan mutum miliyan 593 na fuskantar rashin wutar lantarki da gas''.
Alkire ta ce ''misali mutum miliyan 437 na fama da talauci a ɓangaren ruwan sha da tsaftar muhalli, sannan mutum miliyan 593 na fuskantar rashin wutar lantarki da gas''. "A wannan lokaci na matsi, wanda ke matuƙar tasiri kan rayuwar talakawa yana da matuƙar muhimmanci a samar da waɗannan abubuwa don ceto al'ummomi''. in ji ta.
A yayin da mutane da dama ke ƙoƙarin samun abin da za su rayu da shi, hatta a ƙasashe masu ƙarfi, Farfesa Bandiera ya ce yana da matuƙar muhimmanci a kalli talauci a matsayin yanayin da mutum ke rayuwa''. "Domin kuwa talaka a Jamus mai kuɗi ne idan aka kwatanta shi da talakan Sudan, don haka dole mu yi imanin cewa talauci wani yanayi ne da kowanne ɗan adam a faɗin duniya ke shiga, abin da ya sa dole a bi hanya ɗaya wajen auna shi''.











