Yadda wasan Dambe ke samun goyon baya a duniya

- Marubuci, Marco Oriunto
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
Yayin da rana ke faɗuwa a birnin Kano, ƴan wasan dambe ne ke ƙoƙarin shiga filin daga a jihar da ta kasance birnin na biyu mafi girma a Najeriya.
Amon kiɗan kalangu ne ke tashi a cikin filin damben gabanin fafatawa a wasan karshe na gasar dambe ta cin kofin Sarkin Kano Mai Martaba Ado Bayero.
Ɗaruruwan magoya baya ne, waɗanda yawancinsu suka je dandalin tun sanyin safiya, suka zagaye wurin.
Sun yi ta kiran sunayen zakarun guda biyu don karfafa musu gwiwa, waɗanda suka shiga filin shirye domin dambatawa.
"Akwai wani kiɗa da aka buga don ni kaɗai kafin fara damben. Wannan kiɗan ya karfafa min gwiwa da kuma ƙara min karfi don yin dambe yadda ya kamata," in ji Abdullahi Ali Ahmed, wanda aka fi sani da Coronavirus, a tattaunawarsa da BBC Africa.
"Kiɗan yana firgitawa, sai dai na ajiye tsoro na a gefe guda. Ban ji wata fargaba ba."
Ɗan wasan damben mai shekara 21 na shirin fafatawa da abokin dambensa, wadda ake kyautata zaton ta samo asali cikin Hausawa sama da dubban shekaru da suka wuce.
"Dambe wasa ne na jajirtattu waɗanda ba sa tsoro," in ji Maxwell Kalu, wanda ya kirkiro da Ƙungiyar masu Dambe ta Afrika da kuma ya shirya gasar.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Wasa ne na yadda mazaje ke shirya wa fafatawa."
Masu dambe kan ɗaure igiya a hannunsu a daidai wajen yatsunsu, inda suke amfani da ita wajen kai naushi ga abokin faɗa da kuma kare kai.
Ana yin haka ne da niyyar 'yin kisa' - wanda yake nufin kayar da mutum zuwa ƙasa a cikin wasan dambe.
Kwana guda kafin fafatawa a wasansa na karshe, Coronavirus ya fara yin atisaye da wuri, inda yake koyon salo daban-daban na dambe kama daga kai naushi, tsugunawa da kuma ɗaga kayan nauyi a cikin filin damben da aka tana da da ke wajen birnin Kano.
Wani tsohon hoton mai gina jiki na Amurkqa Ronnie Coleman da ke nuna karfin jikinsa ne ke manne a jikin katangar filin.
Ya samu sunan da ake kiransa da shi na Corona daga wajen wani mai kallon dambe wanda ya bayyana irin yadda yake dambe lokacin da ya kai wata ziyara zuwa Abuja.
"Mun girma muna jin kalmar dambe saboda yana ɗaya daga cikin wasannin gargajiya da muke da su," in ji ɗan damben.
"Na fara shiga dambe tun ina yaro kuma haka na ci gaba da jajircewa a wasan. Daga nan na lura cewa na fara samun nasara a dukkan damben da nake yi."
Yadda wasan Dambe ke sauyawa

A can baya, wasu masu yin dambe na amfani da gilasai a hannunsu domin rage barazanar samun matsala, sai dai an daina amfani da hakan a yanzu da cewa ba ya bisa ka'ida.
"Ba zan yi karya ba, akwai wasu yanka a hannuna, ciwuka da kuma zubar jini a hanci a dambe," in ji Kalu.
A wani yunkuri na saka gasar dambe zama wanda ba shi da haɗari, Ƙungiyar Masu Dambe ta Afrika ta ɓullo da sabbin dokoki, ciki har da yin turmi na minti uku-uku (a baya babu haka) da kuma tsarin maki da za a bai wa masu dambe.
"Mun kuma duba batun yadda mutun zai kai abokin faɗansa ƙasa," in ji Kalu. "Da kuma tabbatar da cewa mutum ya kalla cikin sauki, da kuma saka masu dambe cikin kariya."
Ƙari a kan haka, Ƙungiyar Masu Shirya Damben ta Afrika ta ce jami'an lafiya na nan a kowane lokaci a filin dambe domin ba da agaji.
Coronavirus yana sane da muhimmancin kasancewa cikin lafiya yayin wasan.
Gare sa da kuma iyalansa, dambe ba abu ne da yake sha'awa kaɗai ba. Abu ne kuma da mutum yake samun kuɗi.
"Yawancin rauni da nake ji shi ne samun kwarzane... a fuska, ko a goshi. Wani lokaci kuma a jikina," in ji Corona.
Mahaifiyarsa mai suna Khadija Ahmed ta kasance mai yi masa addu'a a kowane lokaci idan zai tafi yin faɗa. Tana kuma sane da irin barazana da wasan damben da ɗanta ke yi.
"Yana da jajircewa da kuma kwazo tun yana yaro," in ji ta.
"Ya kasance yaro mai ilimi sosai da kuma yake da karfi. Ina addu'ar a fara wasan lafiya a kuma gama lafiya, ba tare da ya ji wani rauni ba, gurɗewa, karaya, ko kuma kowane irin rauni."
Goyon bayan masarauta

Dambe wasa ne na gargajiya da aka fi saninsa tsakaninsa mahauta da ƴan kasuwa a can baya, sai dai an samu masu nuna tsangwama kan mutanen da ke yin wasan a tsakanin wasu ƴan Najeriya.
Sai dai samun goyon bayan Basarake daga ɗaya daga cikin jiha mafi girma a Najeriya da wasan dambe ya yi, alama ce da ke nuna cewa tsangwamar da ake yi wa wasan na sauyawa.
"Abu ne mai muhimmanci a al'adar Kano," in ji Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda ya ce ya goyi bayan wasan dambe tun tale-tale."
"A matsayina na jagoran al'umma da kuma al'ada, ina kallon dambe a matsayin abu mai muhimmanci kuma zan ci gaba da bai wa wasan goyon baya don samu ci gaban musamman ma ga tarihi," in ji Sarkin.
Wasan dambe ya samu gagarumar magoya baya a faɗin duniya, musamman da zuwan kafofin sada zumunta.
Ɗaya daga cikin bidiyon dambe da aka fi kallo a dandalin YouTube ya samu makallata sama da miliyan 25.
A gefe guda, ɗaya daga cikin masu shirya Wasannin Dambe ya saka hannu kan kwantiragi da Ƙungiyar Masu Dambe a farkon wannan shekara, abin da ke nuna cewa wasan na ƙara samun karɓuwa.
"Fatana shi ne bai wa masu dambe ƙarin damarmaki da kuma babban fage na dambatawa," in ji Kalu.
"Ba ya ga Najeriya, magoya baya a Amurka da Brazil na cikin mutane da suke son abin da muke yi."
Nuna hazaka da samun nasara

A can filin damben, Sarkin Kano ya isa ne cikin wata mota kirar Rolls Royce mai ruwan bula - an ruwaito cewa Basaraken na da sha'awar motocin kuma yana da irinsu da yawa.
Sarkin zagaye da tawagarsa waɗanda suka yi shiga irin ta alfarma, na kallon Coronavirus da abokin faɗansa Audun Tunga yayin da suke fafatawa.
Masu damben guda biyu suna wakiltar Gidan Kuduawa da Gidan Guramaɗa, waɗanda suka kasance biyu daga cikin tawagogi uku da ke fafatawa a Gasar.
"Wanda ya yi rashin nasara zai koma gida cikin mota mai ɗauke da itace, yayin da wanda ya yi nasara zai shiga cikin jirgi" in ji mai sharhin wasan. "Duka wannan saboda albarkar Sarki!"
Bayan turmi uku, an ayyana wanda ya yi nasara.
Ganguna sun sake ɗaukar ɗumi yayin da magoya baya kuma ke ta sowa da nuna annashuwa.
Alkalin wasan ya ɗaga hannun dama na Coronavirus, abin da ke alamta nasara.
Ya samu nasara, sai dai tsarin dambe na nufin cewa ɗaukacin kofin zai tafi zuwa Gidan Arewa, wanda ya samu maki mai yawa a gasar ta kwana biyu.
"Mun samu kyautuka kaɗan bayan yin faɗan," in ji Coronavirus.
An ba shi kyautar 150,000 saboda fafatawa da ya yi - wanda ya kasance ninki biyar a kan albashi mafi karanci a Najeriya.
"Wasu lokutan ana manna mana kuɗi a gaban masu kallo," in ji shi.
Irin kyautar kuɗaɗen sun saka dambe na ƙara samun magoya baya a ƙasashen waje, kuma da yawa sun yi tafiya zuwa Mali, Burkina Faso, Kamaru da kuma Nijar domin kallon wasan, wasu lokuta har da take dokar rufe iyakoki da aka kakaba bayan yin juyin mulki.
A gefe guda, Coronavirus, zai koma gida cike da farin ciki kan nasarar da ya yi, ga kuma kyautar kuɗi wanda ya ce zai yi amfani da shi wajen gina rayuwarsa.
"Duk da yadda nake ɗaukar dambe a matsayin sana'a ta, amma ina fatan samun aikin da ya fi shi, inda daga nan zan yi ritaya daga dambe. Ina yin wasan ne kawai na ɗan wani lokaci."














