An sayi dan dambe naira 200,000

Damben gargajiya

Kungiyar damben Kudawa ta kasa ta sayi Bahagon mai Bulala naira 200,000 ranar Lahadi a gidan wasa da ke DeiDei a Abuja ranar Lahadi.

Shi dai Bahagon Mai Bulala mutumin Hadejia ne a jihar Jigawa, Nageriya, amma yake wakiltar Guramada.

Tun da sanyin safiyar Lahadi dan wasan ya je ya gaisa da Alhaji Aminu mai Unguwa, Garkuwan Kudawa ya ce masa zai koma Kudu da dambe.

Kudawa sun tambaye shi koda wanda ya matsa masa sai ya bar Guramada zuwa Kudu, sai ya ce shi da kansa ya amince da wannan hukunci.

Haka kuma dan damben ya fada cewar iyayensa da abokansa sun taka rawar gani, yadda suka ba shi shawara da ya ga ita ce mafita.

Iyayen Kudawa daga Hadejiya sun hada da Wada Hadejia da 'yan Kallamu da Kalla Shushana da Sadam Hussaini da suka buga wa Kudu dambe.

Nan da nan bayan da aka yi masa kida, sai kungiyar Kudawa ta kasa karkashin jagorancin Alhaji Tanko daraktan magani suka ce za su bashi naira 200,000 domin yake kare musu yaki.

Nan da nan Guramada suka ce basu yadda ba, har ma sun yi tayin kara kudin tayin da Kudawa suka yi, amma ba su fito da kudin ba.

Bayan da ake ta ja in ja sai dan wasan da kansa ya karbi bututun magana ya shiga tsakiyar fili ya kuma sanar da cewar ya amince ya zama dan damben Kudawa.

Bayan da fili ya nutsa sai aka bukaci ya yi dambe da dan wasan Guramada, domin a tabbatar ya koma Kudu.

Sai Ali Zuma ya hada wasa tsakanin Bahagon Mai Bulala daga Kudu da Bagobirin Guramada, inda a turmin farko aka buge Bahagon mai Bulala.

Kungiyar dambe kan yi zawarci dan wasa ya koma yi mata yaki, haka shi da kansa idan dan dambe baya samun yadda yake bukata ya kan sauya kungiya.

Ko a baya-bayan nan Shagon Aleka daga Kudu ya koma Jamus, inda aka sauya masa suna Dogon Shamsu.

Tun kan nan Zazu dan wasan Jamus ya koma kungiyar Kudawa, inda ake kiransa da Shagon Alin Bata isarka.