Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barca da Man U sun ja daga kan Rashford, Man City, da Chelsea da Munich na son Thiago
Har yanzu Manchester City, da Chelsea da Bayern Munich na nuna sha'awarsu ta daukar dan wasan gaban Brazil Igor Thiago, mai shekaru 24, duk da cewa ya sanya hannu kan sabon kwantaragi da Brentford. (Teamtalk)
Dan wasan baya na Faransa Dayot Upamecano, mai shekaru 27, ya ki amincewa da bukatar Liverpool da Real Madrid ta sayensa a wannan bazarar bayan ya sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya da Bayern Munich. (Sports Illustrated)
An shaida wa Arsenal, Chelsea da Tottenham cewa dan wasan gaban Brazil Endrick ba zai tashi a wannan bazarar ba. Real Madrid ta ce dan wasan na ta mai shekaru 19, wanda ke zaman aro na tsawon kakar wasan nan a Lyon ya kammala zamansa a can, zai koma Bernabeu a kakar wasa mai zuwa don ita ma tana da bukatarsa.(Teamtalk)
Manchester United za ta nemi sayar da golanta Andre Onana a wannan bazarar. Dan wasan mai shekaru 29 na Kamaru yana zaman aro a Trabzonspor bayan ya rasa gurbinsa a Old Trafford. (Sun)
Tottenham ta bar kofa a bude ga kocin Amurka Mauricio Pochettino, mai shekaru 53, don komawa kungiyar a lokacin bazara, saboda yadda a baya kocin dan Argentina ya jagoranci kungiyar zuwa wasan karshe na gasar zakarun Turai. (Telegraph)
Manchester City ta shirya bayar da kusan Yuro miliyan 50 (£43.4m) don siyan dan wasan baya na dama na Brazil Wesley Franca, mai shekaru 22, daga Roma a lokacin bazara. (Fichajes)
Newcastle, da Tottenham, da Aston Villa na gogaya da Arsenal, da Chelsea, da Liverpool, Manchester City da Manchester United wajen neman ɗan wasan gaba na Bournemouth, Eli Junior Kroupi, mai shekaru 19. (Teamtalk)
Barcelona na son rage farashin da take son siyan dan wasan Man United Marcus Rashford, wato £26m da aka amince da shi a baya, kan dan wasan mai shekara 28, wanda ke zaman aro a kungiyar, sai dai Manchester United ta kafe a kan farashin. (Express)
Barcelona na kallon ɗan wasan baya na Sporting, Gonçalo Inacio, mai shekaru 24, a matsayin babban burin da ta sanya a gaba don ƙarfafa bayanta, sai dai akwai bukatar ta biya Yuro miliyan 70 (£60m) kan dan wasan. (Fichajes)