Tinubu ya sake roƙon ƴan Najeriya su ƙara haƙuri

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, @officialABAT

Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake yin roƙo ga ƴan ƙasar su ƙara yi wa gwamnatinsa haƙuri inda ya ce sauƙi na nan tafe.

Shugaban ya sake yin jawabi ne ga ƴan Najeriya a wani tsohon bidiyo da aka sake wallafawa a shafinsa na X ranar Laraba bayan jawabin da ya yi a ranar Lahadi a ƙoƙarin lallashin masu zanga-zanga ya sha suka daga ɓangarori da dama.

A cikin bidiyo shugaban, ya nanata cewa yana sane da ƙuncin rayuwa da ƴan Najeriya suka shiga sakamakon janye tallafin fetur.

Wannan bidiyo da shafin shugaban ƙasan ya sake wallafawa ana ganin wani yunƙuri ne na ci gaba da bai wa jama'a haƙuri sanadiyyar halin da al'umma ke ciki.

Ƴan Najeriya da dama ne suka fantsama a titunan biranen ƙasar domin zanga-zangar tsadar rayuwa, inda wasunsu da dama ke kira ga shugaban ya dawo da tallafin da ya cire na man fetur da suka ce ya jefa su cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa.

Amma a cikin bidiyon, shugaban ya ce yana sane da wahalar da ƴan Najeriya ke ciki tare da nanata cewa wahala ce ta ɗan ƙaramin lokaci.

“Wannan lokacin zai iya zama mai wahala a gare mu amma ina son mu yi hangen gaba a cikin wahalar da muke ciki da kuma la’akari da babbar manufar. Mun yi tsare-tsare masu kyau kuma na san za su yi aiki,” in ji Shugaba Tinubu.

Sai dai shugaban ya amince cewa tsare-tsaren da gwamnatinsa ke ɗauka sun ƙara wa ƴan Najeriya raɗaɗin janye tallafin fetur.

Amma ya ce ya yi imanin matakan gwamnatinsa ke ɗauka za su magance matsalolin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki.

“Ina roƙon ku, ku yi haƙuri tare da imanin cewa za mu iya da kuma damuwar da muke nunawa kan buƙatunku. Za mu fita daga cikin wannan ƙangin, kuma saboda matakan da muke ɗauka Najeriya za ta samu ci gaba da kuma more makomarta,” a cewar shugaba Tinubu.

Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a wasu jihohin Najeriya musamman yankin arewaci sakamakon zanga-zangar da wasu ƴan ƙasar suka ƙaddamar ta kwana 10 da suka fara daga ranar 1 ga Agusta.

Tashin hankali a zanga-zangar ya kai ga saka dokar hana fita a wasu jihohin ƙasar.