Yadda naɗe-naɗen Trump ke nuna inda gwamnatinsa za ta karkata a wa'adi na biyu

    • Marubuci, Anthony Zurcher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Arewacin Amurka
  • Lokacin karatu: Minti 6

Mako ɗaya bayan Donald Trump ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka karo na biyu, tuni aka fara ganin inda gwamnatinsa za ta mayar da hankali.

Zaɓabɓen shugaban ƙasar ya sanar da naɗa gomman mutane a kan muƙamai daban-daban kawo yanzu, wanda ake ganin shi ne matakin farko na ɗaukar ma'aikatan fadarsa ta WHite House da kuma na muhimman ma'aikatun gwmanati.

Ya kuma yi martani kan kafofin yaɗa labarai da shafukan sada zumunta da suka bayyana inda zai fi mayar da hankali da zarar ya shiga ofis a watan Janairu, inda zai mayar da hankali kan hukumar shige da fice da kuma tsarin ƙasashen waje.

Bayan shiga ruɗani lokacin da ya fara mulki a wa'adinsana farko, yanzu Trump ya fara yin tsare-tsare da ke nuna inda gwamnatinsa za ta karkata - da kuma jami'ai da ke shirye don yin aiki tukuru.

Ga wasu abubuwa da muka sani kan haka kawo yanzu.

Tawagar jami'an shige da fice mai tsauri

Wasu daga cikin sabbin naɗe-naɗen da Trump ya yi na nuna cewa alkawarin da zaɓabɓen shugaban ya yi lokacin yaƙin neman zaɓe na cewa zai kori miliyoyin bakin-haure da ke zaune a Amurka gaskiya ne.

Stephen Miller, wanda ya kasance babban mashawarcin Trump kuma marubuci tun 2015, shi ne mutumin da Trump ya zaɓa don zama mataimakin shugaban ma’aikatan fadar White House kan manufofi.

Zai iya tsara duk wani shiri na ƙorar ɗaruruwan ƴan ci-rani - kuma ya dakatar da shige da ficen mutane ba bisa ka'ida ba. A lokacin wa'adin mulkin Trump na farko, Miller ya shiga sahun gaba wajen bijiro da tsare-tsare masu tsauri da wasu manufofin gwamnati a ɓangaren shige da fice.

Thomas Homan, muƙaddashin daraktan hukumar shige da fice da kwastam a wa'adin Trump na farko, ya goyi bayan manufofin shugaban na raba iyalai marasa takardun shaida da ake tsare da su a kan iyakar Amurka da Mexico.

Yanzu ya koma da wani babban tsari fiye da na baya, a matsayin "tsarin shige da fice" na Trump.

"Zan gudanar da aikin ƙora mafi girma da wannan ƙasar ba ta taɓa gani ba," in ji Homan a wani taron masu ra'ayin mazan jiya a watan Yuli.

Masu sukar lamirin sun yi gargaɗin cewa shirin ƙorar bakin-haure da Trump ke son yi, zai iya lakume sama da dala biliyan 300.

A wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta NBC News a makon da ya gabata, zaɓabɓen shugaban ƙasar ya ce yawan kuɗin da za a kashe kan batun ba wani abu bane.

"Idan mutanen da suka kashe mutane, idan masu shan miyagun ƙwayoyi suka lalata ƙasashe, kuma yanzu za su koma waɗancan ƙasashen saboda ba sa zama a nan,babu buƙatar duba yawan kuɗin da za a kashe" in ji shi.

An naɗa waɗanda za su musguna wa China

Yawancin masu ra'ayin riƙau sun yi imanin cewa China ta kasance babbar barazana ga cigaba da ikon Amurka a duniya, a fannin tattalin arziki da kuma na soja.

Yayin da Trump ke yin taka tsantsan, tare da takaita mafi yawan sukar da yake yi wa China a fannin kasuwanci, yanzu yana cika tawagarsa kan manufofin ketare da masu sukar China.

Zaɓabɓen shugaban ƙasar ya zaɓi ɗan majalisar dokokin Florida Mike Waltz, wani kanal ɗin soja mai ritaya, a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro - wani muhimmin matsayi a cikin fadar White House.

Waltz ya ce Amurka na cikin "yaƙin cacar baka" da ƙasar China kuma yana ɗaya daga cikin mambobin majalisar dokoki na farko da suka yi kira ga Amurka ta ƙaurace wa wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing na shekarar 2022.

A watan Oktoba, 'yar majalisa Elise Stefanik, wadda Trump ya zaɓa jakadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya, ta zargi China da "kutsa kai cikin zaɓuka da mugun nufi" a daidai lokacin da rahotanni ke cewa masu satar bayanan da China ke mara wa baya sun yi yunkurin tattara bayanai daga wayoyin tsohon shugaban.

Yayin da har yanzu Trump bai bayyana sunan wanda zai bai wa sakataren harkokin wajen Amurka a hukumance ba, Sanatan Florida Marco Rubio - wani mai adawa da China - da alama shi ne kan gaba wajen neman muƙamin babban jami'in diflomasiyyar.

A shekarar 2020, gwamnatin ƙasar China ta sanya wa Rubio takunkumi bayan da ya ɗauki matakin hukunta ƙasar saboda murkushe masu zanga-zangar neman demokraɗiyya a Hong Kong.

Yaawanci dangantaka tsakanin Amurka da China tana tsami a lokacin wa'adin Trump na farko, musamman takaddamar kasuwanci da kuma ɓarkewar cutar Covid-19.

Gwamnatin Biden, wadda ta ci gaba da tsarin harajin da Trump ya ɗora wa China tare da sanya sababbi, ta ɗan yi ƙoƙarin daidaita dangantakarsu.

Yanzu ana ganin cewa gwamnatin Trump mai zuwa a ta ɗora daga inda ta farko ta tsaya.

Sabon matsayin Elon Musk

Yayin da jerin sunayen waɗanda Trump ya naɗa ke karuwa, akwai wata ƙungiya da ta rage - kuma tana da matukar tasiri.

Elon Musk, wanda ya fi kowa arziki a duniya, ya kasance a gidan Trump na shakatawa ta Mar-a-Lago.

Rahotanni daga kafafen yaɗa labarai na cewa yana ba wa zaɓabɓen shugaban shawara kan naɗin ministocin har ma ya shiga tattaunawa tsakanin Trump da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky a makon jiya.

A daren ranar Talata, Trump ya ba da sanarwar naɗa Musk don yin aiki tare da ɗan kasuwar kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Republican Vivek Ramaswamy a ma'aikatar inganta ayyukan gwamnati.

Musk ya kasance yana bayyana ra'ayoyinsa na siyasa akai-akai akan dandalinsa na sada zumunta na X, ciki har da amincewa da yunkurin Sanata Rick Scott na Florida na zama shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa.

Kwamitin harkokin siyasa na Musk ya kashe kusan dala miliyan 200 don taimakawa yaƙin neman zaɓen Trump, kuma ya yi alkawarin ci gaba da bayar da kuɗaɗe a ƙoƙarinvciyar da ajandar zaɓabɓen shugaban ƙasar da kuma taimakawa 'yan takarar jam'iyyar Republican a zaɓen 'yan majalisar dokoki mai zuwa.

A halin yanzu, ya rage a ga inda Robert F Kennedy Jr zai karkata, wani jigo mai mahimmanci.

Trump ya ce yana shirin bai wa tsohon ɗan Democrat kuma mai shakkun allurar riga-kafi, dama don ganin rawar da zai taka wajen sake mayar da Amurka mai cikakkiyar "lafiya".

"Yana son yin wasu abubuwa, kuma za mu ba shi goyon baya," in ji Trump a jawabinsa na murnar lashe zaɓe.

Ɗaukaka ikon shugaban ƙasa a kan na majalisa

Yayin da Trump ya hau kan karagar mulki, ‘yan Republican na da iko a Majalisar Dattawa kuma har yanzu suna iya karɓar majalisar, ko da karamar tazara.

Sai dai kuma matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka tun farko ya nuna cewa ya fi damuwa da yin amfani da karfin ikonsa na shugaban ƙasa fiye da yin aiki da ɓangaren majalisa.

A makon da ya gabata, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta cewa ya kamata shugabancin Majalisar Dattawa ta Republican ya sassauta hanyar naɗin muƙamai - wanda zai ba shi damar cike manyan ayyukan gwamnati ba tare da amincewar Majalisar ba lokacin da ba ta cikin zama.

Matakin zai karfafa ikon shugaban ƙasa ta hanyar yin watsi da rawar da kundin tsarin mulkin majalisar ya tanada na "ba da shawara da yarda" kan waɗanda aka naɗa a siyasance.

A halin da ake ciki, zaɓabɓen shugaban ƙasar ya ci gaba da yin watsi da waɗancan ’yan majalisar wakilai.

Sanatocin da suka koma matsayin gwamnati za a iya maye gurbinsu da gaggawa ta hanyar naɗa gwamnan jiharsu.

Amma duk wani guraben Majalisa - kamar na Stefanik da Waltz - na buƙatar zaɓe na musamman wanda zai ɗauki watanni kafin a tsara shi.

Wasu daga cikin mashawartan Trump, ciki har da Musk, sun yi gargaɗin cewa zaɓabɓen shugaban na iya yin barazana ga shirinsa na majalisar dokoki idan ya fidda 'yan Republican da yawa daga zauren majalisar.

Ko da a cikin mafi kyawun yanayi, dokokin majalisa na ɗaukar lokaci, ƙoƙari da kuma sadaukarwa.

Za a iya aiwatar da aikin zartarwa, kamar ɗaukar sabbin matakai kan bakin haure, ta hanyar amincewar shugaban ƙasa.

Aƙalla a yanzu, take-taken Trump sun nuna cewa ya fi mayar da hankali kan ƙorar bakin haure daga ƙasar.

Saka wa magoya baya

Trump dai ya fara naɗa mutane cikin dubban gurabe da ake da su a sabuwar gwamnatin shugaban ƙasa, sai dai ban da manyan jami’an ma’aikata da ya ce zai maye gurbinsa.

A cikin 2016, a matsayinsa na sabon shiga siyasa, dole ta sa ya dogara da kafa ƙarin 'yan Republican a manyan ayyuka.

A wannan karon, yana da ɗimbin muƙarrabai waɗanda suka kasance gani-kashe ninsa bayan shekaru takwas.

A ranar Talata, Trump ya naɗa gwamnar South Dakota Kristi Noem a matsayin sakatariyar tsaron cikin gida, da kuma mai gabatar da labarai a kafar yaɗa labarai ta Fox News kuma marubuci mai ra'ayin mazan jiya, Pete Hegseth a matsayin sakataren tsaro.

Dukansu sun kasance masu goyon bayan Trump masu tsauri tun daga farko.

Wasu kamar Rubio da Stefanik, sun kasance masu sukar Trump a farkon takararsa ta shugaban ƙasa, amma a yanzu sun kwashe shekaru suna nuna cewa munanan kalaman nasu ya zama tarihi.

Rubio, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa da Trump a 2016, mai yiwuwa har yanzu yana da burin zuwa fadar White House.

An ce sau da yawa Trump ya yi ta naɗa waɗanda ake ganin sun jawo hankalinsu a lokacin wa'adinsa na farko.

Trump na iya ba da fifikon naɗe-naɗensa kan sakawa magoya bayansa a naɗe-naɗen ma'aikatansa na farko, amma matsin lamba na mulki zai nuna cewa ko wa'adin mulkinsa na biyu zai bambanta da na farko.