Wane hali tauraron fim ɗin Indiya Dharmendra ke ciki a asibiti?

धर्मेंद्र

Asalin hoton, The India Today Group via Getty Images

    • Marubuci, Ravi Jain
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hindi
  • Lokacin karatu: Minti 2

Ana ci gaba da jinyar sanannen ɗan wasan fim ɗin Indiya Dharmendra a asibitin Breach Candy da ke birnin Mumbai na ƙasar Indiya.

Tawagar wasu likitoci ce ke lura da lafiyar jarumin a kowane daƙiƙa.

BBC ta yi yunƙurin jin ta-bakin ɗaya daga cikin likitocin da ke kula da lafiyar tauraron na Bollywood, sai dai ya ƙi ya ce komai, inda ya kafa hujja da kare bayanan sirri na maras lafiya da iyalinsa.

Sai dai bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an kwantar da Dharmendra a asibiti ne mako uku da suka gabata, inda yake fama da matsalar numfashi da kuma cutar lumoniya.

An kwantar da jarumin ne a ɗakin marasa lafiya da ke neman kulawa ta musamman, bayan la'akari da shekarunsa.

A ranar Talata ne ƴarsa, Dharmendra Esha Deol da matarsa, Hema Malini suka bayyana rashin jin daɗi kan yadda aka riƙa yaɗa labaran ƙarya, da kuma yaɗa labarin 'rasuwarsa' a kafofin sadarwa.

Esha Deol ta rubuta a shafinta na Instagram cewa "Kafafen yaɗa labarai suna gaggawar yaɗa labaran ƙarya. Mahaifina na cikin yanayi mai kyau kuma yana ci gaba da farfaɗowa. Mun gode da addu'o'inku na samun lafiyarsa."

Matar Dharmendra, wadda ita ma sananniyar tauraruwar fim ce Hema Malini ta rubuta a shafinta na Instagram cewa "Abin da ke faruwa ba abu ne da za a iya yafewa ba! Ta yaya wata kafa za ta riƙa yaɗa labarin ƙarya game da mutumin da ke jinya kuma yana farfaɗowa daga rashin lafiyar da take fama da ita?"

Ta ƙara da cewa "wannan rashin girmamawa ne! Ya kamata a martaba sirrin iyali."

Taurarin fim sun je dubiya asibitin

धर्मेंद्र, हेमा मालिनी

Asalin hoton, STR/AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Matar Dharmendra, Hema Malini ta nuna rashin jin dadi kan labaran ''ƙanzon kurege'' da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta kan lafiyar mijinta
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Salman Khan, wanda ke kallon Dharmendra a matsayin abin koyi, an gan shi ya kai ziyara a asibitin a yammacin ranar Litinin.

Jarumi Govinda, wanda shi ma ya yi aiki tare da Dharmendra a finafinai da dama shi ma ya je asibitin da daddare domin ziyartar maras lafiyar.

Ɗaya daga cikin hadiman Dharmendra ya tura wa sashen BBC Hindi saƙon kar-ta-kwana a ranar Litinin yana cewa "Jikin Dharmendra na warwarewa kuma a halin yanzu ya ji sauƙi… Muna roƙon al'umma su yi masa addu'a sannan kuma su yi ƙoƙarin martaba sirrin iyalansa."

Tun bayan da aka kwantar da Dharmendra a asibiti, babu wani bayani game da rashin lafiyarsa, ko dai daga asibitin ko kuma daga likitocin da suke kula da shi.

A ranar Litinin, mutane sun riƙa tuɗaɗa zuwa asibitin na Breach Candy.

Babban ɗan maras lafiyar Sunny Deol ya kasance a asibitin da safe, sai dai ya bar asibitin da rana, inda aka ga ya koma asibitin da yamma.

Ita ma matar Dharmendra Hema Malini ta je asibitin, sai dai bayan wani lokaci an ga ta tana fita daga asibitin a cikin mota.