'Yan wasan Ingila biyar na jerin sunayen gwarazan Fifa ta mata

A

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

'Yan wasan Ingila mata da suka hada da Lucy Bronze da Lauren Hemp da Keira Walsh na cikin waɗanda za su iya lashe kyautar gwarazan Fifa ta 2024.

Lioness Mary Earps wadda ta lashe gwarzuwar mai tsaron raga sau biyu a baya, tana cikin jerin sunayen.

Yar wasan Ingla da Arsenal Beth Mead na cikin waɗanda za su iya lashe kyautar Marta, wadda aka gabatar domin girmama kwallon da ta fi kowacce a ɓangaren mata.

An sanya sunan Mead ne saboda kwallon da ta ci West Ham ta biyu a watan Nuwambar 2023.

'Yar wasan Brazil kwararriyar nan Marta wadda aka sawa kyautar sunanta, tana cikin jerin sunanyen.

Mai horaswa Emma Hayes, wadda ta taimakawa Chelsea ta lashe kofin mata sau biyar a jere kafin ta lashe zinare a gasar wasanni ta Olympic da Amurka.

Kocin Manchester City Gareth Taylor, sabuwar kocin Chelsea Sonia Bompastor da ta Celtic Elena Sadiku na cikin jerin sunayen.

'Yar wasan Spain da Barcelona Aitana Bonmati wadda ta lashe kyautar mata ta 2023, na cikin wannan jeri ha'ilau.

Har yanzu ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a a shafin Fifa za kuma a rufe zaɓen ne 10 ga watan Disamba.

Masu horaswa ƙasashe da kyaftin-kyaftin da 'yan jarida da magoya baya na cikin waɗanda suke zaben.

Jerin sunayen 'yan takarar gwarazan Fifa

Aitana Bonmati (Spain/Barcelona)

Barbra Banda (Zambia/Orlando Pride)

Caroline Graham Hansen (Norway/Barcelona)

Keira Walsh (England/Barcelona)

Khadija Shaw (Jamaica/Manchester City)

Lauren Hemp (England/Manchester City)

Lindsey Horan (USA/Lyon)

Lucy Bronze (England/Chelsea)

Mallory Swanson (USA/Chicago Red Stars)

Mariona Caldentey (Spain/Arsenal)

Naomi Girma (USA/San Diego Wave)

Ona Batlle (Spain/Barcelona)

Salma Paralluelo (Spain/Barcelona)

Sophia Smith (USA/Portland Thorns)

Tabitha Chawinga (Malawi/Lyon)

Trinity Rodman (USA/Washington Spirit)

Masu horaswa

Arthur Elias (Brazil)

Elena Sadiku (Celtic)

Emma Hayes (Chelsea/USA)

Futoshi Ikeda (Japan)

Gareth Taylor (Manchester City)

Jonatan Giraldez (Barcelona/Washington Spirit)

Sandrine Soubeyrand (Paris FC)

Sonia Bompastor (Lyon/Chelsea)

Masu tsaron raga

Alyssa Naeher (USA/Chicago Red Stars)

Ann-Katrin Berger (Germany/Chelsea/NJ/NY Gotham)

Ayaka Yamashita (Japan/Manchester City)

Cata Coll (Spain/Barcelona)

Mary Earps (England/Manchester United/Paris St-Germain)