Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Babu yankin da za mu ware wa takarar 2027 - ADC
Jam'iyyar ADC ta gamayyar wasu ƴan hamayya a Najeriya ta ce za ta bai wa duka mambobinta da ke da sha'awar tsayawa takarar zaɓen shugaban ƙasa su gwada sa'arsu.
ADC ta ce duk wanda ake son tsayawa takara daga cikin mambobinta ya fito, za ta ba shi dama a yi zaɓen fitar da gwani, don samun wanda zai yi mata takarar a zaɓen na 2027.
Jam'iyyar ta ce za ta fifita cancanta wajen zaɓen wanda zai yi mata takara a zaɓen maimakon yankin da ɗan takara ya fito.
Matakin jam'iyyar a zuwa ne a daidai lokacin da manyan jam'iyyun ƙasar biyu APC mai mulki da PDP, babbar mai hamayya suka keɓe wa kudancin ƙasar takarar shugabancin ƙasar a 2027.
'Za mu fifita cancanta fiye da yanki'
Jam'iyyar ta ADC ta ce tana da shugabancin da ke girmama dimokaraɗiyya, da zai bai wa kowa dama, wanda kuma hakan shi ya bambantata da sauran manyan jam'iyyun ƙasar.
Yayin wata hira da gidan talbijin na TVC News, mai magana da yawun jam'iyyar Bolaji Abdullahi ya ce jam'iyyar za ta bai wa kowa damar fitowa takara a zaɓen mai zuwa.
Bolaji ya ce ADC ba ta damu da kowa ya taya takara cikin ƴaƴanta ba, saboda jam'iyyarmu tana da ingantaccen tsarin fitar da ɗan takara.
"Duka mutanen da za su iya tsayawa takara sun yi imani da tsarin jam'iyyarmu ta tadanar wajen fitar da ɗan takara'', in ji shi.
Ya ce a yanzu abin da ADC ta saka a gaba shi ne ginata da kuma ƙarfafata, tare da tallatata ga ƴan Najeriya.
Me matakin na ADC ke nufi a siyasance?
Masana harkokin siyasa na ganin cewa sai jam'iyyar ta ADC ta yi taka tsan-tsan wajen tabbatar da wanan iƙirari nata.
Farfesa Kamilu Sani Fagge masanin kimiyyas siyasa kuma malami a jami'ar Bayero da ke Kano ya ce jam'iyyun APC da PDP da suka riga suka ɗauki matakin keɓe wa kudanci takarar shugaban ƙasa sun yi hakan ne, saboda suna ganin hakan ne sai kai su ga gaci.
''Ita APC dama ɗantakarta wanda shi ne shugaban ƙasa daga kudu yake, kuma koda ana zo zaɓen fitar da gwani ba wanda zai kayar da shi, tun da shi take so'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa ''ita kuwa PDP ta ɗauki matakin ne saboda tana ganin hakan ne zai kai ta ga nasara''.
Sai dai malamin Jami'ar ya ce wannan mataki da jam'iyyun biyu suka ɗauka ya saɓa wa tsarin dimokraɗiyya da kundin tsarin mulkin Najeriya.
"Wannan abu da suka yi ba ya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma ya saɓa wa doka''.
Farfesa Kamilu ya ce idan har jam'iyyar ADC ba ta yi taka-tsantsan ba wajen fitar da ɗan takara, to za ta iya watsewa saboda dama ba ta gama haɗuwa ba.
''idan har ta kuskura ta yi ɗauki ɗora to lallai hakan zai jefa jam'iyyar ciin matsala, lamarin da zai kai ta ga rugujewa'', in ji shi.
'ADC na da dama mai kyau'
Dakta Yakubu Haruna Ja'e shugaban sashen kimiyyar siyasa na Jami'ar jihar Kaduna ya ce ADC na da dama mai kyau ta shirya wa zaɓen 2027.
Ya ce idan har jam'iyyar ta samu damar fitar da muhimmin ɗan takara mai farin jini a arewa to lallai zai iya yin nasara.
''Kasancewar duka manyan jam'iyyun sun tsayar da ɗan takara daga kudu, hakan na nufin ƙuri'un kudu za su rabu gida biyu, kuma dama APC ba ta da wani farin jini har a yankin Yarabawa da Tinubu ya fito''.
''To idan ƴan arewa suka haɗe kai, kuma ADC ta fitar da ɗan takara mai ƙarfi da farin jini zai iya yin nasara, saboda dama yankin arewa ƙuri'un suka fi yawa'', in ji shi.
''Wannan dama ce ga ƴan adawar, idan har suka iya fitar da wani gogaggen ɗan takara, to tabbas zai samu goyon bayan arewa, kuma wataƙila zai iya samun wasu ƙuri'un daga yankin kudu'', in ji shi.
'Ɓangaranci zai taka rawa a 2027'
Farfesa Kamilu Sani fagge ya ce idan har jam'iyyun siyasar Najeriya ba su hankali ba, zaɓen 2027 zai kasance mai cike da ɓangaranci a cikinsa.
''Zaɓen zai iya ɗaukar nau'in ɓangaranci da ƙabilanci da ma addini, idan ba a yi a hankali ba'', in ji shi.
Ya ce kuma an kama hanyar hakan tunda manyan jam'iyyu biyu APC da PDP tuni sun ɗauki ɓangaranci, tunda sun keɓe wa kudanci takara.
''Yanzu PDP ana ganin kirista za su fitar da shi, saboda wurin da suka karkata, da wuya a iya samun ɗan takara musulmi''.
Yana mai cewa hakan zai iya maido da siyasar addini da ƙabilanci ko ɓangaranci a Najeriya.