Me ya sa Fafaroma yake sanya jan takalmi da sauran tambayoyi

An nuna tufafin da sabon Fafaroman da za a zaba zai sa a cikin taga na ɗakin dinki a Italiya, Gammarelli, a ranar 4 ga Maris, 2013 a birnin Roma.

Asalin hoton, AFP

    • Marubuci, Andrew Webb
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Marubuci, Additional reporting by David Willey
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Rome
  • Lokacin karatu: Minti 7

Bayan zaɓan sabon Fafaroma sai hankali ya karkata zuwa ga hasashen ko zai ci gaba da bin tafarkin Fafaroma Francis wajen nuna sassauci fiye da waɗanda suka gaba ce sy.

Haka kuma akwai batun tsantsane da gudun rayuwar jin daɗi kamar yadda wasu Fafaroma suka saba, kasancewar Fafaroma Francis ya zaɓi rayuwa mai sauƙi maimakon haka.

Me ne ne taƙaimeman aikin Fafaroma?

Maragayi Fafaroma Francis

Asalin hoton, Getty Images

Fafaroma shi ne jagoran fiye da Kiristocin Katolika biliyan 1.4 a faɗin duniya.

Katolika na kallonsa a matsayin magajin Saint Peter, ɗaya daga cikin shugabannin farko na cocin Kirista.

A addinin Kirista, Yesu Almasihu ɗan Allah ne, kuma Saint Peter yana daga cikin sahabbansa 12.

Katolika na da imanin cewa wannan yana haɗa Fafaroma kai tsaye da Yesu wanda hakan ya mai da shi a matsayin wata muhimmiyar madogara ta jagorancin addini.

A duk shekara, Fafaroma ne ke jagorantar manyan bukukuwan addini a cikin cocin Saint Peter da ke birnin Rome, ciki har da manyan ranaku kamar Kirsimeti da Easter

Fafaroma Francis ya ɗaga hannu yana gaisawa da mabiya da suka taru a dandalin Saint Peter yayin addu’ar albarka ta Angelus da ya yi a ranar Lahadi, a lokacin Ranar Matasa ta Duniya, a ranar 24 ga Nuwamba, 2024 a Birnin Vatican.

Asalin hoton, Vatican Media

Bayanan hoto, Bayan an zaɓi sabon Fafaroma, yana yin fitowarsa ta farko a bainar jama'a daga saman baranda na cocin Saint Peter da ke Birnin Vatican domin gaisawa da taron jama'a.

Yana bayyana a saman baranda ɗaya da aka ayyana shi a matsayin Fafaroma bayan zaɓensa, domin isar da saƙonsa na "Urbi Et Orbi" wanda a Latin ke nufin "ga birni da duniya"., wato wata albarka ta musamman da Fafaroma ke bayarwa a lokutan bukukuwa na addini da wasu lokuta na musamman.

Fafaroma kuma na da tawagar mata hadimai masu yi masa hidima.

Haka kuma yana da tawagar mutane da ke taimaka masa wajen rubuta jawabansa.

Ɗaya daga cikin manyan aikinsa shi ne ganawa da fiye da bishof 5,000 daga sassa daban-daban na duniya. Ana tsammanin zai gana da kowanne bishof sau ɗaya a cikin shekaru biyar — wanda ke nufin kusan bishof 1,000 a shekara ko kusan 20 a mako.

A zamanin yauzu, yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje ya zama wani ɓangare na aikinsa.

Shin Fafaroma yana aure?

A baya, an taɓa yin Fafaroma da ya yi aure, kamar St Peter da ake ɗauka a matsayin Fafaroma na farko yana da mata, amma a zamanin yanzu, zai yi wuya a zaɓi wande ke da aure a matsayin Fafaroma.

Tarihin Fafaroma na farko yana da rikitarwa kuma yana janyo muhawara a tsakanin masana tarihi.

Ba a da tabbacin adadin Fafaroma da suka kasance masu aure kafin su zama shugabannin cocin Katolika kamar Saint Peter.

Mutum-mutumin St Peter yana kallon taron jama'a a Vatican

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, St Peter ya kasance yana da aure kafin ya zama Fafaroma
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A baya, An taɓa yin Fafaroma da suke da aure — misali, Fafaroma Hormisdas (514–523), an kyautata zaton shi ne ya haifi magajinsa Fafaroma Silverius da kuma Fafaroma Adrian II (867–872) kuma ya zauna tare da matarsa da 'yarsa a fadar Lateran.

Masana tarihi na ganin cewa Fafaroma John XVII da Clement IV suma sun yi aure kafin su zama Fafaroma.

Duk da haka, ba a da wata shaida mai ƙarfi da ke nuna cewa wani daga cikin Fafaroma 266 da Vatican ta lissafa ya yi aure bayan zama Fafaroma, kodayake ana kyautata zaton wasunsu suna yi alaka da mata a asirce.

A zamanin yanzu, yana da matuƙar wuya a ga wani mai aure ya zama Fafaroma. Duk da cewa kowanne namijin Katolika da aka yi wa baftisma na iya zama Fafaroma a ƙa'ida.

Tun daga shekarar 1378, duka Fafaroma da aka zaɓa sun fito ne daga cikin manyan limaman kirsta— kuma babu wanda ke da aure a cikinsu da ke da ikon zaɓe a yanzu. Ana kuma buƙatar malaman Katolika su kasance ba su da aure (celibate).

Ko da yake akwai wasu keɓantattu da ke ba wasu mazajen aure damar zama firistoci — kamar a cikin Katolika na ritin Gabas ko tsofaffin malamai na Anglican da suka koma Katolika — ba za su iya zama manyan limamai ba, wanda hakan ke hana su samun damar zama Fafaroma.

Ko Fafaroma na da albashi?

An ruwaito cewa Fafaroma Francis ya ba da albashinsa ga ayyukan jinƙai.

A shekarar 2021, wani mai magana da yawun Vatican ya bayyana cewa: "Fafaroma baya karɓar albashi kuma bai taɓa karɓa ba."

Fafaroma Francis ma ya ƙi karɓar wasu daga cikin jin daɗin da ke tattare da muƙaminsa, inda ya zaɓi zama a gidan baƙi na Vatican, wato Casa Santa Marta, maimakon ɗakunan alfarma.

Fafaroma Benedict XVI daga Jamus, ya ɗaga hannu daga saman baranda na cocin Saint Peter a Vatican bayan an zaɓe shi a matsayin sabon Fafaroma a ranar 19 ga Afrilu, 2005.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Fafaroma Benedict XVI ya shugabanci Cocin Katolika daga shekarar 2005 har zuwa lokacin murabus ɗinsa a shekarar 2013.

Fafaroma Benedict XVI, ya ɗauki matakin da ba kasafai ba na yin murabus a shekarar 2013, yana mai cewa dalilin ya kasance na matsalolin lafiya. Kafar watsa labarai, ciki har da jaridar Italiya la Stampa, ta ruwaito cewa yana karɓar fansho.

Har tsawon yaushe Fafaroma ke mulki?

Yawancin Fafaroma suna shugabanci ne har zuwa lokacin mutuwarsu kamar yadda Fafaroma Francis ya yi, inda ya yi aiki daga 2013 har zuwa 2025.

Babu wani Fafaroma da ya yi murabus tun daga Gregory XII a shekarar 1415, kuma Benedict XVI ne na farko da ya yi hakan da kansa tun daga Celestine V a 1294.

Masana tarihin sun sha muhawara game da yawan Fafaroma da suka yi murabus.

  • Pontian a shekarar 235
  • Silverius a shekarar 537
  • John XVIII a shekarar 1009
  • Benedict IX a shekarar 1045
  • Celestine V a shekarar 1294
  • Gregory XII a shekarar 1415

Ta ya ya ake zama Fafaroma?

A cewar dokar Canon, wato tsarin dokokin addini da ke tafiyar da cocin Kirista, ana iya zaɓar waɗannan mutane a matsayin Fafaroma, in ji Catholic Online.

  • Ana iya zaɓar kowanne namijin Katolika da aka yi masa baftisma kuma yana da hankalin tunani a matsayin Fafaroma
  • Duk da cewa tun fiye da shekaru 500 da suka wuce ba a zaɓi wani da ba babban limami ba, tarihi ya nuna cewa ana iya zaɓar wani malamin addini ko ma talaka.
  • Idan wanda aka zaɓa bai riga ya zama Bishop ba, dole ne a naɗa shi Bishop nan take kafin ya hau kujerar Fafaroma.

Masana da dama sun bayyana cewa halin kirki na daya daga cikin abubuwan da ake la'aka ba a bayyana hakan a matsayin doka ba.

Manyan limaman Katolika ƙasa da shekara 80 za su taru a sirriance domin su zaɓi sabon Fafaroma.

Asalin hoton, Mimmo Chianura-Pool

Bayanan hoto, Manyan limaman kristan ƙasa da shekara 80 za su taru a sirriance domin su zaɓi sabon Fafaroma.

Sai manyan shugabannin Katolika da ake kira Cardinal – waɗanda dole ne su kasance ƙasa da shekara 80 – ke da damar kada ƙuri'a don zaɓen Fafaroma.

An dade ana gudanar zaɓen Fafaroma a sirrance tsawon ƙarni da dama, bisa ƙa'idodi masu tsauri da aka shimfiɗa don hana shisshigi daga waje.

Me ya sa Fafaroma ke saka jan takalmi?

A cikin addinin Katolika, kalar ja yana nuni da shahada da kuma wahalhalun da Almasihu ya sha da suka haɗa da azaba da kame da shari'a da gicciyen Yesu kamar yadda aka bayyana a Sabon alƙawari.

Fafaroma Benedict XVI da yawancin sauran Fafaroma da suka gabace shi sun bi wannan al'ada ta sanya jan takalmi.

Fafaroma Benedict XVI sanya da jan takalmin shi
Bayanan hoto, Jan takalmin Benedict XVI sun kasance wani muhimmin ɓangare na mulkinsa a matsayin Fafaroma, wanda yake sanyawa a matsayin alamar iko da matsayi.

Sai dai, a matsayin Fafaroma, Francis ya zaɓi sanya takalmi baƙi – wata alama da masu lura suka fassara a matsayin ƙoƙarinsa na kaucewa jin daɗin alfarma da shahara.

An sanya masa takalmi baƙi a ƙafarsa lokacin da aka kwantar da gawarsa domin mutane su zo su yi masa ban kwana.

 Fafaroma Francis sanye da baƙin takalmi a ƙafarsa lokacin da aka kwantar da gawarsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An sanya wa Fafaroma Francis baƙin takalmi a ƙafarsa lokacin da aka kwantar da gawarsa domin mutane su zo su yi masa ban kwana.

An dai samu bambance-bambance a kan wannan al'ada na kalar takalmin da Fafaroma zai saka.

An ruwaito cewa Fafaroma John Paul II ya taɓa sanya takalma ja mai duhu a wasu lokuta.

Mujallar rayuwar zamani ta Amurka Esquire ta ce ya kuma taɓa sanya "takalman fata ruwan kasa"

Me ya sa cocin Katolika ke da Fafaroma?

Kamar yadda aka bayyana a baya, Katolika suna ganin Fafaroma a matsayin magajinin Saint Peter, ɗaya daga cikin waliyen Yesu.

Saboda haka, ana iya ganin Fafaroma a matsayin shugaba, kuma wani muhimmin ɓangare na tubalin rayuwa na Cocin Katolika.

Fafaroma yana ba da jagora ga Katolika da kuma ba da shawarwari kan yadda za su fuskanci ƙalubale da matsalolin rayuwa – manya da ƙanana.

Hakanan yana taimakawa shugabannin cocin da ke ƙasa da shi wajen nemo hanyar da za su jagoranci al'ummominsu.