Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kurakurai 13 da na'urar VAR ta tafka a gasar Premier cikin wata shida
- Marubuci, Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief football news reporter
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugabannin da ke lura da gasar ƙwallon ƙafa ta Premier a Ingila sun bayyana cewa na'urar da ke taimaka wa alƙalin wasa wajen yanke hukunci (VAR) ta tafka kuskure sau 13 tun bayan fara wannan kakar.
Hakan na nufin an samu raguwar kurakuran da na'urar ke yi idan aka kwatanta da kakar da ta gabata, inda ya zuwa irin wannan lokaci ta tafka kuskure sau 20.
Na'urar ta yi kuskuren sauya hukuncin alƙalin wasa sau huɗu sannan ta yi kuskuren rashin sauya hukunci sau tara a cikin wasanni 23 da aka buga, in ji kwamitin alƙalan da ke lura da taƙaddamar da ake samu a lokacin wasa.
An samu lokuta 70 da aka yi amfani da na'urar ta VAR a wasanni 279 na gasar Premier a wannan kakar ya zuwa yanzu, kwatankwacin amfani da na'urar sau ɗaya a cikin wasa uku.
Masu lura da gasar sun ce ƙwarewar na'urar wajen yanke hukunci ya ƙaru zuwa kashi 96.4% idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata.
"Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure ɗaya wajen yanke hukunci zai yi," in ji wani babban jami'in ƙwallon ƙafa, Tony Scholes.
"Mun san cewa kuskure ɗaya tal zai iya cutar da ƙungiya. Sakamako da kuma makin da ƙungiya ke samu na iya sanyawa a kori mai horaswa ko kuma ɗan wasa ya rasa damarsa a cikin ƙungiya."
Hakan ya faru ga Erin ten Hag - domin ɗaya daga cikin kurakurai huɗu da na'urar VAR ta tafka shi ne bai wa West Ham bugun fanareti a wasa na ƙarshe da kocin ya jagoranci ƙungiyar Manchester United.
Haka nan wasu alƙalan wasan sun fuskanci cin zarafi, inda a kwanakin nan ƴansanda suka ƙaddamar da bincike kan "barazanar cin zarafi" kan alƙalin wasa Michael Oliver bayan wasan da Arsenal ta yi nasara kan Wolves da ci 1-0 a watan Janairu.
Wannan ya biyo bayan matakin da alƙalin wasan ya ɗauka na bai wa ɗan wasan Arsenal, Myles Lewsi-Skelly katin kora - matakin da daga baya aka soke bayan ƙorafin da ƙungiyar ta shigar.
Shi ma tsohon lafari David Conte, an kore shi ne a watan Disamba bayan binciken da aka gudanar kansa.
Hukumomin gasar Premier dai ba su bayyana lokuta 9 da na'urar VAR ta ƙi soke wani mataki ba - kuma babu tabbas ko batun jan katin da aka bai wa Lewis-Skelly na ciki.
Amma hukumar ta yi bayani kan kurakurai huɗu da na'urar ta tafka ga manema labarai.
Kuskure huɗu da VAR ta tafka
Outtara ya 'taɓa ƙwallo da hannu' - Bournemouth 1-1 Newcastle, 25 ga Agusta
- Abin da ya faru: Dango Outtara ya zaci cewa ya ci wa ƙungiyarsa Bournemouth ƙwallon da za ta ba ta nasara lokacin da ya zura ƙwallon da kai. Lafari David Coote ya bayar da ƙwallon.
- Matakin VAR: Mai kula da na'urar VAR a wasan, Tim Robinson ya bai wa Coote shawarar soke ƙwallon, inda ya ce an taɓa ƙwallon da hannu. Kasancewar yana da yaƙini kan hukuncinsa, bai buƙaci lafari ya kalli bidiyon lamarin ba.
- Sakamako: Kasancewar babu cikakkiyar hujjar da za ta tabbatar da cewa ƙwallon tabbas ta taɓa hannun Ouattara, shugaban hukumar lura da alƙalan wasan gasar Premier, Howard Webb a lokacin da ya tattauna da kafar yaɗa labarai ta Sky Sports, ya ce - VAR ta yi kuskure wajen soke cin ƙwallon.
De Ligt ya kwashe Ings - West Ham 2-1 Man Utd, 27 ga Oktoba
- Abin da ya faru: Ɗan wasan gaba na West Ham, Danny Ings ya faɗi a cikin 18 lokacin da yake fafutikar buga ƙwallo tsakaninsa da mai tsaron baya na Manchester United, Mathijs de Ligt. Lafari David Coote ya bayar da damar a ci gaba da wasa amma sai mai kula da na'urar VAR, Michael Oliver ya buƙaci a sake dubawa a talabijin na gefen fagen wasa.
- Matakin VAR: Daga nan ne Coote ya bayar da bugun fanareti, wanda ɗan wasa Jarrod Bowen ya zura a raga, kuma hakan ya bai wa West Ham nasara a wasan.
- Sakamako: Washegari United ta sallami Ten Hag daga aiki. Daga baya Web ya ce bai kamata a bayar da fanareti ɗin ba.
Jan katin da aka bai wa Norgaard - Brentford 0-0 Everton, 23 ga Nuwamba
- Abin da ya faru: Ɗan wasan Brentford, Christian Norgaard ya tokari golan Everton, Jordan Pickford a gwiwa lokacin da suke fafutikar kaiwa ga ƙwallo a cikin 18.
- Mataki VAR: Lafari Chris Kavanagh bai hura fawul ba amma sai mai kula da na'urar VAR ya buƙace shi ya sake duba wurin a talabijin ɗin gefen fage. Bayan sake dubawa, nan take ya ɗaga wa Norgaard jan kati.
- Sakamako: Kwamiti mai zaman kansa ya soke dakatarwar da aka yi wa Norgard na wasa uku bayan ƙorafi da aka shigar.
Soke ƙwallon da Milenkovic ya zura - Nottingham Forest 3-2 Southampton, 19 ga Janairu
- Abin da ya faru: Nikola Milenkovic ya jefa ƙwallo a raga da kai inda hakan ya sanya Nottingham Forest ta yi gaba da ci 4-1.
- Matakin VAR: Na'urar VAR ta umarci lafari Anthony Taylor ya soke cin saboda ɗan wasan Forest, Chris Wood ya yi satar fage inda hakan ya hana masu tsaron baya na Southampton damar ƙalubalantar ƙwallon. Wood bai taɓa ƙwallon ba.
- Sakamako: Kwamiti mai zaman kansa da ya duba lamarin ya ce ya kamata a bayar da cin.