Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Za a ci gaba da amfani da VAR a Premier League
Gasar Premier League ta Ingila za ta ci gaba da amfani da na'urar VAR mai taimaka wa alƙalin wasa a kaka mai zuwa.
An amince da matakin ne saboda kulob ɗin Wolves ne kaɗai ya jefa ƙuri'ar amincewa da yin watsi da ita yayin ganawar shekara-shekara a ranar Alhamis.
Wolves ɗin ne ya gabatar da ƙudirin kaɗa ƙuri'ar cikin wani kundi da ya miƙa wa hukumar gasar a watan Mayu da ya gabata.
Kafin a daina amfani da VAR ɗin, akwai buƙatar 14 cikin ƙungiyoyi 20 na Premier su kaɗa ƙuri'ar amincewa da hakan.
Sai dai kuma BBC Sport ta fahimci Wolves ba ta samu goyon baya daga sauran ƙungiyoyi ba.
An daɗe ana matsa wa hukumar gasar ta gyara yadda ake amfani da na'urar, wadda aka fara aiki da ita a kakar 2019-2020.
An tabbatar yayin ganawar cewa za a ƙaddamar da wasu sabbin hanyoyin gano satar gida nan gaba kaɗan, yayin da hukumar ta ce za a dinga sanar wa 'yan kallo dalilin da ya sa aka ɗauki mataki a cikin fili.
Ba da sanarwar ɗaukar matakin da aka fara amfani da ita a gasar Kofin Duniya ta Mata ta 2023 na nufin alƙalan wasa za su yi wa magoya baya bayani da zarar an gama amoncewa da matakin da na'urar ta nuna.