Na fara damuwa da yadda ake amfani da na'urar VAR - Sean Dyche

Kocin Everton, Sean Dyche ya ce yin amfani da na'urar VAR a filin wasa na "ƙure haƙurinsa", bayan da aka yi waje da ɗan wasan gaban kulob din, Dominic Calvert-Lewin at lokacin wasansu da Crystal Palace.

An dai cire ɗan wasan mai shekara 26 a karon farko a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa, a lokacin wasan zagaye na uku na gasar Zakarun Turai, a Selhurst Park.

Dominick dai ya taɗe Nathaniel Clyne na Crystal Place, inda ya harɗe ɗan wasan gaban.

Dyche ya ce "hotunan bidiyon na VAR ya nuna wani abun daban."

"Idan kana son nuna bidiyo a hankali, to ka yi wa komai hakan. Babu 'yar haɗuwar jiki kuma a lokacin wasan a fili, rafalin bai ce komai ba amma bayan da aka nuna a VAR sai kuma komai ya ƙazance."

Rafali Kavanagh da farko dai bai dauki kowane irin mataki ba amma bayan sake dubawa a VAR sai ya ɗaga wa ɗan wasan jan kati a minti na 79.

Yanzu dai za a sake nuna yadda taɗiyar ta wakana a Goodison Park nan gaba a watan Janairu. To sai dai wannan ne karo na uku da ake korar Calvert-Lewin a wasa.