Man United na zawarcin Bellingham, West Ham da Sevilla na rububin Zirkzee

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na nazarin ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Borussia Dortmund ɗan ƙasar Ingila, Jobe Bellingham, mai shekara 20 a matsayin aro a watan Janairu. (Express)
West Ham da Sevilla na zawarcin ɗan wasan gaban Manchester United da Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24. (Mirror)
Manchester City da Tottenham sun shiga jerin ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗan wasan tsakiya na Sporting da Denmark Morten Hjulmand, mai shekara 26, inda za su yi hamayya da Manchester United. (Record)
Liverpool na tunanin zawarcin ɗan wasan gaban Newcastle da Ingila Anthony Gordon, mai shekara 24, da ɗan wasan Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25. (Football Insider),
Tottenham da Manchester City na ci gaba da bibiyar ɗan wasan Aston Villa ɗan ƙasar Ingila Ezri Konsa, yayin da Chelsea da Liverpool da kuma Manchester United su ma suka nuna sha'awarsu kan ɗan wasan mai shekara 28 cikin watanni 12 da suka gabata. (TBR Football)
Newcastle da Brighton da Fulham da Brentford duk suna zawarcin ɗan wasan Middlesbrough da Ingila Hayden Hackney mai shekara 23. (TBR Football)
Roma na son sake tattaunawa kan yarjejeniyar aro na ɗan wasan gaban Brighton da Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson, inda ake ganin yiwuwar ɗan wasan mai shekara 21 zai koma ƙungiyar ta Premier a watan Janairu. (Gazzetta dello Sport)
Newcastle da Tottenham na zawarcin ɗan wasan bayan Juventus da Faransa Pierre Kalulu, mai shekara 25. (TuttoJuve)
Barcelona na sanya ido kan ɗan wasan Marseille ɗan ƙasar Ingila Mason Greenwood mai shekara 24. (Sun)
Inter Milan na iya amincewa da tayin da Leeds ke yi wa Piotr Zielinski, inda ake ganin yiwuwar tafiyar ɗan wasan tsakiyar Poland mai shekara 31 a watan Janairu. (Football Insider)
Jami'ai daga Arsenal da Chelsea da Manchester City na sanya ido kan ɗan wasan gaban Bayern Munich da Jamus Lenart Karl mai shekara 17. (Caught Offside)











