An wanke Sepp Blatter da Platini daga zargin rashawa

Former Fifa President Sepp Blatter arrives at the tribunal for the verdict. He wears a navy suit, stares directly at the camera and holds both hands up.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sepp Blatter ya sauka daga muƙaminsa na shugaban Fifa yayin da ake masa zargin rashawa
    • Marubuci, Ruth Comerford
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

An wanke tsohon shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa Sepp Blatter da tsohon shugaban Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai (Uefa) Michel Platini daga zargin rashawa a hukumar ƙwallon ƙafar ta duniya.

A ranar Talata wata kotun ɗaukaka ƙara da ke garin Muttenz, kusa da birnin Basel na ƙasar Switzerland ta wanke mutanen biyu waɗanda ake zargi da saɓa ƙa'ida kan kuɗi fam miliyan 1.6 da Blatter ya biya Platini a shekarar 2011.

Dukkanin mutanen biyu sun musanta zarge-zargen.

A shekarar 2022 ne wata kotu ta fara wanke mutanen, sai dai masu shigar da ƙara na ƙasar Switzerland sun ɗaukaka ƙara.

Turka-turkar ta faro ne daga shekarar 2015, lokacin da aka zargi hukumar ta Fifa da ayyukan rashawa, lamarin da ya kai ga jami'an tsaro sun kai samame a ofishin hukumar da ke Zurich, sanadiyyar wani bincike da ake yi a Amurka.

Wannan shi ne babban abin kunya da ya faru a fagen wasan ƙwallon ƙafa na duniya, ya gwara kan jami'an hukumomin ƙwallon ƙafa da kuma jagororin ɓangaren kasuwanci.

Lamarin ya tursasa wa Blatter ajiye aiki kuma ya kawo ƙarshen fatan da Platini ke yi na gadon sa a kan muƙamin.

Hukumomin ƙasar Switzerland sun zargi Blatter da Platini da ha'intar hukumar Fifa ta hanyar zamba. Inda suka ce tura kuɗin ba ya kan ƙa'ida.

Mutnanen biyu sun ce kudin na wani tsohon aiki ne da Platini ya yi wa Fifa a baya.

Former UEFA President, Michel Platini (C) arrives to the hear the trial verdict at the special appeals court in Muttenz.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tsohon shugaban Uefa Michel Platini ya ce "ƙimarsa ta dawo" bayan yanke hukuncin